episode 7

431 27 0
                                    

AURE UKU

(a hospital romance)

      By.

  Chuchujay

EPISODE 7⃣

Umaimah!

Na'am Daddy .

Gyaran murya yayi yana mai gyara zaman sa yace "umaimah naji komai da yake faruwa ,sannan ina Mai baki Haƙuri ga dukkan abunda ya faru wanda a yanzu Ya zama past ɗin da baza'a kuma maimaitawa ba nan gaba na miki Alƙawari,

Yanzu ki ɗauko su Abdallah kizo mu koma gida zamu zauna a yi magana wadda na tabbatar miki babu makamancin Abunda Ya faru da zai kuma faruwa indai nine Mai gidan Bulama sannan marin da Ali Ya miki har haƙuri zai baki .

Shiru tayi kafun tace"ni Daddy bana so Ya bani haƙuri kawai ina san Ya kiyaye Ko da Wasa kar Ya kuma marina, 'dan Allah Daddy idan ya kuma shari'ace zata rabani dashi, tunda dai su basu ɗauke ni yar uwar su ba,tun kuruciya ina sane  da dukkan abunda suke min daga su har hajiya,yaya Abubakar ne kawai yake nuna ni tashi ce".

Sannan ni Daddy ba zan koma gida ba, ba tare da na samu Mai kulamun dasu nadiya ba tunda Family na duk Albarkars u babu Mai sansu.

Dafa ta yayi yace "umaiman daddy idan kina faɗan Haka har da Daddy fa".

Ɗan karamun murmushi tayi tace"ni banda Kai Daddy dan nasan da ace kai mace ne zaka kula mun da yarana kamar Kai ka haifesu,"

Yanzu ma Dada tace zamu tafi da shatu ƴar baffa dikko ƙanin baffa da mijinta Ya rasu babu abunda take gida ni ko biyan ta ne zan nayi duk da tace bata so,

Hankalina zai fi kwanciya idan tana tare dasu,sannan ba wai nace Aunty sadiya bata mun ba, Daddy itama Ga ɗawainiyar yaranta ga na su nadiya abun yana mata yawa,

Dama kuma Nameer jiya yace mun yana san zai rubuta exam ɗin NTIS (Nigerian Turkish international school)na Abuja yayi jss to sss a chan wanda dama nima na dade Ina so.

Murmushi daddy Ya faɗaɗa yace kinga shikenan sai suje tare da Ibrahim(ibi) ya samu ɗan uwa,

kicin kicin tayi da ranta tace"Daddy nifa ba wai bana san Alaƙar su nameer ne da jikokin ka na gun su yaya usman ba kawai ni dai gwanda nameer yaje Abuja ɗin in yaso su suje na nan Adamawa ɗin. "

Tabbas abunda zaisa umaimah ta nemi su ibi suyi nisa da nameer ba ƙaramun abu bane duba da yarda take nunawa yaran kauna ,

Shafa kanta yayi yace shikenan yarda kike so Haka za'ayi, yanzu dai kije gurin baffa ki kira su nameer ɗin mu koma gida tunda ai nasan Ko yanzu kikace shatun tazo zata zo Ai baza a tsaya ma dasu Nadiya karatu ba ,ga Abdallah ma za'ayi enrolling ɗinsa ya kamata kuma ace da kaina naje na saka shi.

Bata san cigaba da musu da Daddyn nata 'dan Haka tace "to daddy".

Sallama sukayi da Dada da baffa yayin da suka ɗauki shatu wadda a kalla umaimah zata bata shekaru huɗu da haihuwa ,

Taron gaggawa daddy ya kira a daren ranar wanda dukkan sun tabbatar da sun hallarta har da matan su kafin Ya buga musu zazzafan warning ɗin da Ya tabbatar suma zasu wa ƴaransu dan bazai lamunta ba su b'ata masa gida da negativity ba.

Sanin Halinsa yasaka ko wannensu shiga taitayi.

Washe gari da sassafe ta wuce asibiti inda daddy kamar yarda Ya faɗa Ya dauki Abdallah da kansa ya kaishi makarantar su Nadiyan domin saka shi.

Tana zaune a office kamar kullum bayan Farouk Ya gama shigar mata da duk abunda take bukata ciki har da coffee ,bata nemi wani cookies ba 'dan yau da irish and egg sauce ɗin da shatu tawa su nadiya ta taho ,

AURE UKU(completed)Where stories live. Discover now