episode 5

444 33 0
                                    


AURE UKU

(a hospital romance)

    BY

   CHUCHUJAY

EPISODE 5⃣

    Riƙe Paki dake koƙarin yin gurin KB yayi gam yace"no Paki ,no wannan maganar ba wadda zaka shiga bace ,damƙe hannu Paki yayi kamar zai kaiwa wani naushi yana Mai Cije haƙoran sa, yasan da fushin da tabbas idan Ya je gurin zai zubarwa da Dr Jabir haƙora ".

Juyowa umaimah tayi a lokacin da maganar Dr Jabeer ta dakar mata zuciya dai dai saitin da yake mata ciwo,

Ta daɗe tana jin rumours  ana cewa tana rabawa matan masu kuɗi irin su jikin ta shi yake hana ta Aure, amma bata taba samun wanda Ya faɗa mata kan fuskarta ba,

Bawai abun baya damun ta bane, yana damun ta musamman yarda jita jita ke cigaba da yaɗuwa akan ta,

Shin wai ita ta ɗorawa kanta ƙaddarar da Allah Ya jarabceta da?.

Ɗan karamun murmushi tayi tace "za kaga ƙarfin connection,ba kace kuɗin babana bai zaunar dani gidan Aure ba?"Zaka Ga yarda yarda kuɗin babana zai daure ka for defamation of character tunda baka taba ganin lokacin da na bawa Ko wacce mace jikina ba kamar yarda ka faɗa,

I'm gonna show you what money can do here Jabir,

If you'll excuse me.

Juyawa tayi tana mai Jin wata kwalla na zubo mata wadda tayi saurin gogewa a lokacin guda kuma idanun ta suka sauka kan Paki wanda ke tsaye yana Kallan abunda ke faruwa ransa a mutuƙar bace kar ma ace Da Ya lura da kwallar cikin idanunta.

Ɗauke idanunta tayi daga nashin ta nufi cabin ɗinta 'dan shirin Aikin da za tayi,

Gama shirinta ke da wuya ta juya zata fito taga an buɗe kofar,ɗagowa tayi,

Idanunta ne suka shiga cikin nasa,

Cire idanunta tayi cikin nasa tana Mai kashe wayanta ,

Muryarsa ta tsinta a yayin da yake faɗin,"zaki iya yin Aiki a haka".?

Wata irin karamar dariya tayi ta ɗago da idanunta ta kallesa tace"first this is My personal cabin 'dan na tabbata a sama Kafun ka shigo kaga an saka Doctor Bulama's Cabin Nasan atleast  ka iya karatu zuwa nan,

Secondly we Are not that close beside ban san ka ba,ina so ka riƙe wannan Alaƙar ta supervisor da dalibi itace tsakanina da kai dan naga alama kana san wuce gona da iri,kasan limit ɗinka,

Thirdly ina san ka sani,i dont mix duk wani abu da Ya shafi Aikina da wani abun duk girmansa so don't mistake what happened as My weakness

Now get out."

Gyara tsayuwar sa yayi yana Mai folding hannunsa a kirjinsa cikin blue kayan likitoci, a bangare ɗaya kuma yana mata wani irin kallo Mai kashe jiki,

Coffee ɗin da ya kawo mata Ya aje kan table Ɗinta har lokacin idanun sa na kan idanunta Kafun yace"cold coffee ne 'dan nasan ba lallai kin karya ba,a lokutan da kika ware na Aikin da za'ayi kinci minti goma a waje ,komai yayi ready ke ake jira ,so take the coffee and ina san ki sani Ko Auren ki goma a duniya da yara kimanin faɗin duniya akwai wanda hakan bai dame sa ba da duk wani Abu da za'a faɗa akan ki.

Juyawa yayi Ya fita a cabin Ɗin.

    Bin kofar tayi da kallo a yayin da taji cikin ta yayi wani ƙugin yunwa,

Daga cup Ɗin coffee ɗin tayi ta shanye Cos bata san shiga O'R ba tare da tasa komai a cikinta ba,

Amma tabbas za suyi magana dole tasa gayen nan a inda ya dace dashi.

AURE UKU(completed)Where stories live. Discover now