episode 19&20

432 27 2
                                    

AURE UKU

(a Hospital romance)

    By

Chuchujay ✍🏽

Episode 1⃣9⃣➡2⃣0⃣

    Kamar guguwa haka Nana ta faɗo cikin ɗakin ,

Tsaye Paki yake gefen Umaimah dan tana turo kofar Ya matsa ,

Wani irin kallo yake bata ran sa a mutukar bace

Daga bayan ta ummu dake biye da ita tace "Nana yanzu Kin yarda imam baya da lafiya shine abunda Ya kawo umaimah nan ,amma ba abunda kike tunani ba".

    Kallan ummu dake maganar Nana tayi kafun ta matsa gurin Umaimah wadda ta fara ja da baya dan bata manta cizan da Ummu tayi mata ba saboda yarda Ya bar mata tabo,

Shinshina ta Nana ta fara kamar wata kare Kafun tace "kwarankwatsa Habiba yarinyar nan kanshin turaren imamu take ,hakan kuma abu ɗaya yake nufi wanda Shine daga jikin sa take."

Cikin bacin rai imam yace "subhanallah ,Nana menene haka wai?"

Wacce irin magana ce daga jikina take?

    Duka ta kai masa wanda yayi saurin kaucewa tace "dan ubanka babu abunda ban sani ba musamman wanda Ya dan danganci mata irinta ,idan ba kinibibi ba uban menene Ya kawota duba imamu cikin gidan nan?

Ko ance mata bamu da likitan da yake zuwa duba mune ,

Wanda ma yasha gwagwarmaya a filin daga ,Ya samu horo na sojoji mazan fama masu jini a jika .

    Kallan umaimah tayi wadda take ji a ranta da ace nana ba kakar paki bace ta daɗe da maganinta,

Cikin yin fiki fiki da ido tace sameera zo ki gane mun bakinta kamar sumba suka sha dan naga Ya kumbura ko ido nane?.

Da sauri sameera da ta biyo bayan su tace"zancen ki dutse Nana wallahi gashi nan da tazo bakin ta ba a haka yake ba ,ni dama tunda naga Ummu ta fito ,KB ma Ya fita nasan Akwai magana,amma nasan ummu bazata saurareni ba,ke kuma gashi baki gida,shi yasa kina shigowa naga Ya kamata na faɗa maki wannan zance kiyiwa tufkar hanci.

    Wani irin kallo Ummu ta bawa sameera kafin tace"anya sameera za'a tafi haka kuwa ?,

Mene yake damunki,duka duka yaushe na bar su a dakin sannan menene laifi idan har likita da mara lafiya suka keb'e a ɗaki tare ?

Haba dan Allah muna yiwa mutane zato Mai kyau mana.

    "Ba shakka habiba,ba shakka ƴar masu jan kunne har tasan wai ayiwa mutum zato Mai kyau,

Gaskiya Muntari nikam Ya cuce ni da Ya Auro ki,

Duk yan matan Fulani dake garin nan kyawawa Ya rasa wadda zai Aura sai wadda addinin ta ma yake da rauni,

Ke da baki da tarbiyya ina zaki samu damar bawa wani,?

Kan umaimah ta kuma yi wadda ta kai maƙura ,ta ɗaga hannu zata mareta tayi saurin rikewa.

    Wani karamin murmushi tayi a yayin da Nana ta saki baki tana Mai rafka salati,

Sauke hannun nata Umaimah tayi da nutsuwa tace"Nana ke babba ce ,sannan ke kaka ce,kuma a matsayin ki na Nana'n imam na ɗauke ki kamar tawa,dan Allah ki bari sannan duk abunda kike tunani bashi ne Ya shiga tsakanina da Imam ba,ni ina da abunyi a asibiti ,

Kallanta ta mayar kan ummu tace "ummu imam is okay yanzu sannan Zan bawa KB magunguna Ya kawo masa ,stress ne kawai yake damun sa."

    Murmushi ummu tayi tana Mai jin umaimah a ranta kafin tace"na gode My daughter,Allah yayi miki albarka.

AURE UKU(completed)Where stories live. Discover now