Episode 9

396 27 0
                                    

https://chat.whatsapp.com/DgTUlodRcp2AHM4rmfKTqK

AURE UKU

    (a hospital romance)

            By

    Chuchujay.

EPISODE 9⃣

  Washe gari bata shiga Asibitin ba saboda weekend ne kuma musamman saturday ,sunday ne takan shiga , Tana tsaka da bacci taji ana ja mata ƙafa,

"Yi tayi kamar bata san anayi ba ,"Cigaba da jan ƙafar yasata farkawa ,

Dariya nadiya tasa tace "hamma nameer i won dole ka bani Tab din ka na sati nayi game,"Ɗan bata rai yayi yace"mami why do You wake up We bet ne 'fa.

"Tashi tace tace "akan me kuka yi betting ɗin tell mami"

"Haurowa gadan da take Nadiya tayi tana Mai washe hakora tace "mami betting mukayi nace masa yau saturday mami na bacci amma nasan idan naja miki kafa zaki tashi ,shine hamma nameer yace Ai bazaki tashi ba Cos kina da gajiyan weekday ,amma idan kin tashi yasa mun tab ɗin sa na sati ɗaya".

"Ƴar karamar dariya umaimah tayi Kafun ta kalli nameer dake faman haɗe rai zai bawa nadiya Tab ɗin sa tace"okay ku saurare ni,"Anything betting is haram,ko menene shi koda da wasa ne,a musulunci babu kyau 'dan Haka Banda Wasan betting,

"Idan nameer zai baki tab ɗin sa aro ne to Ya baki amma ba wai ɗan Kin cinyesa a bet ba ,okay".

"Kaɗa kai sukayi a tare inda Nameer  yace dama mami banyi niya ba"cos duk ranar da na arama nadiya Tab ɗina sai ta cinye chaji tas take dawo mun dashi .

"Mami nima Tab ina san na kalli johnny johnny hamma Nameer kuma baya bani,

"Dariya Umaimah tasa ga maganar da Abdallah wanda yake shigowa da gudu shatu na binsa a baya yayi".

"Ɗannowa yayi kan gadon yana Mai hawa jikinta yayin da ta rungumesa ,"

Zama shatu tayi bakin gadon tace"Adda ina kwana ?"Kin tashi kenan.

"Murmushi tayi tace "wallahi shatu sun tashe ni zan ce ma ,ina fatan baku jira ni ba kun karya ."

"Kaɗa kai tayi tace "ai Adda kema kin san rigimar Abdallah da rashin haƙurin sa ga yunwa ba zai bar mu shan ruwa ba musamman ace mun kai sha ɗaya ."

"'Ɗan buɗe ido tayi tace "har sha daya ,kace na sha bacci,".

"Mami mene plan ɗin yau ko za mu Roly park ne it have been a While,nameer Ya faɗa yana Mai Marairaice murya..

A tare suka haɗa baki wajen faɗin"roly park,suna chanting tare,".

Zata yi magana taga wayanta na ringing da baƙuwar Number,

Ɗauka tayi ta kara a kunnenta tana Mai faɗin hello a yayin da yaran nata suka cigaba da faɗin Roly park ,Roly park,.

Daga ɗaya bangaren taji an kashe wayan 'dan Haka tace naji roly park kuje Auntyn ku ta shirya ku bari na yi wanka na ci abinci,

"Ihu suka fara cike da murna ,kana suka fita nadiya na faɗin Yau zan ridding real horse".

"Kallan shatu umaimah tayi bayan fitar nameer da nadiya tace"Auntyn  yara shiryawa zakiyi muje fa".

"Murmushi tayi tace "Adda kuje dai ku dawo kinsan ni ba ma'abociyar san fita bace,ina nan gida ina jiran ku,ga wankin su Abdallah chan ma nasa cikin washing machine ga gugan su kinsan ni da aiki muna haɗe amma wani zuwan zan biku.

AURE UKU(completed)Where stories live. Discover now