episode 8

429 30 0
                                    

AURE UKU

(a hospital romance)

     By

CHUCHUJAY

EPISODE 8⃣

    Wani irin tafarfasa paki yake Kafun yace "wallahi idan baka tashi ka fita ba zan karyaka na karya banza 'dan wallahi babu abunda zai faru".

"Idan kana ganin kuma kuri nake kar ka tashi ka fita,"

Ganin irin tafarfasar da Paki yake yasa Habib tashi Yana faɗin"wallahi sai kasan ka nausheni dan wallahi Asirinku Ya gama tonuwa Kai da ita ,"

"Sannan Ai ba karya bane nine nan nafara daga daga da ita ,kai ni koda zan karbi budurcinta ka tambayeta ta fada maka a banza na karbeshi da wulaƙanci,a buge kuma yarda zaka gane a banza na ɗauki abunda kake bibiya,sannan maza biyu bayan ni suka bi gurin sai kuma waɗanda baka sani ba Kai kanka,ni nasan a yanzu Ya zama tafki"

"Ba karamu ɗaci da takaici maganganun Habib suka bawa Umaimah ba musamman da Ya kasance a gaban Paki wanda ita ta jawowa kanta da tace Ya tsaya,she shouldn't have involved him,

"Bata damu da mutane su san Aurenta ba amma abinda Habib ke faɗa sirrinta ne,rabon da amata wulaƙanci irin wannan har ta manta,

"Naushi Paki yake Kai masa ta ko ina ta yarda Habib ɗin bashi da halin ramawa,"

"Security Landline ta kira wanda babu bata lokaci mutum uku suka shigo ,sakin sa paki yayi yace da Security ɗin su tafi dashi"

"Har lokacin bakin Habib bai mutu ba ,babu abinda yake faɗi sai "wallahi sai kun san dani kukayi ,sannan kisa a ranki kamar na ɗauki Nameer ne,kuma sai na tona muku asirin iskancin da kuke"

Har suka fitar dashi yana surutai,

"Cije baki paki yayi yana kallan kofar da aka fita da Habib ,debating yake da zuciyarsa na ya juya ko kar ya juya."

"Juyawa yayi inda idanunsu suka haɗu cikin na juna yayin da nata ke cike da kwallar dake san fitowa".

"Cije bakinsa yayi yace"well im Sorry akan abunda Ya faru,He's a psychopath bai  kamata ace kin saka maganar sa ba a zuciya ta dame ki   "

"Hannayen sa Ya dora akan kunnuwa sa da sigar toshewa yace "maganganun da Ya faɗa ,na toshe kunnuwa na ,kisa aranki banji ko ɗaya ba,sannan ki sani babu Abunda wani zai fada akanki naji soyayyarki tayi rauni a zuciyata,"Hasalima karamun sanki naji kamar anyi"

"Dariya tasa cikin hawayen da yanzu suke reto a kuncinta kafun tace"Stop pretending kamar kasan ni wacece saboda wasu abubuwan da kaji a kaina,ka ɗaina tunani kai wani knight 'in a shining amour ne you are all scums duk hallayyar ku ɗaya ".

"Zama yayi kan kujera yana Mai faɗin wallahi.."

"Bai Kai ga ƙarasawa ba tayi watsi da kaya dake kan table ɗinta tace "GET OUT FROM HERE BEFORE I lOOSE IT".

"Tashi yayi in surrending manner yana Mai ɗaga hannunsa sama yace "yi hakuri zan fita,".

Babu musu ya juya Ya bar office ɗin.

"Riƙe bakin ta tayi ta saka wani kuka Mai cin rai tace "oh GOD this is embarrassing ".

Koda Ya fita Kai tsaye changing room Ya wuce yana Mai jin zuciyarsa na masa zafi,ga wata zazzafar soyayyar umaimah da tausayinsa da Ya kuma Shigarsa,kamar yarda ta faɗa baisan wace ita ba ,sannan shi a yanzu soyayyarta yake nema in yaso duk lokacin da taji Ya kamata zata bashi labarinta,

AURE UKU(completed)Where stories live. Discover now