CHAPTER ONE

1.5K 101 6
                                    

Bismillahir Rahmanir Raheem


Hope you all will enjoy it

Stay blessed

♡♡♡♡♡♡♡♡♡

    *Cross River State (Calabar)Nigeria.*

   Bakassi LGA

   Wata yarinya ce budurwa kyakkyawan gaske take k'okarin cire kayan ta a parlour, bud'e baki nayi ni Nana dan ba k'aramin mamaki nayi ba sabida a parlour'n ba ita kad'ai bace, akwai wata mata wanda ak'alla bazata haura shekaru arba'in ba zaune tana gyara ganye , sai wani saurayi wanda shi bazai haura shekaru ashirin da biyar ba, da wani dattijun mutum wanda ak'alla zai kai saba'in duk suna zaune a parlour'n. Ita kuwa yarinya budurwar nan haka tacire  rigan jikin ta tsaf a gaban su ba kunya zindir haihuwar uwar ta, ta d'aura wani shara sharan gyale wanda dashi da babu duk d'aya, sai wani yamutse fuska take, she looked up with a puzzled frown on her face, Saurayin dake zaune a cushion yayi dariya yace
"Ahh LOLA why are you frowning your face anh?"
  Matar dake gyara ugu leave take ta d'aga kanta tana kallon wanda aka kira da Lola itan ma ita take kallo matar tace
  "What are you frowning at me for? Enh Lola?"
  Tura bakin ta tayi tace
"Mummy I really wanna attend this birthday party ohh!"
"And what if I don't permit you to go?"
K'ara turo bakin ta tayi tace
"Mummy I am now a grown up gurl, for goodness sake I am eighteen years, e-i-g-h-t-e-e-n good years Mummy" tayi emphasising shekarun.
Wani harara Mummy'n ta mata tace
"And so bloody what? Lola and so what? I said you ain't going anywhere and that's final"
  Hawaye neh shar shar ya fara sauk'a akan kuncin ta, dan tayi maita taje birthday party'n k'awar ta Abigail dan ta had'u da saurayin ta. Fita tayi a parlour'n tana mai bubbuga k'afanta ta.

    *Kano State, Nigeria*

    Wani mansion parlour neh had'add'e wanda yasha kayan alatu, tsaya misalta had'uwan parlour'n inaga waste of time neh. Wata farar mata ce kyakkyawan gaske  zaune akan wani foreign cushion designer, can gefen ta kuma wasu masu tsananin kama na hango wanda kallo d'aya na musu na tabbatar TAGWAYE ne, kamar su har ya wuce misali. Tsaya k'are musu kallo nayi naga kusan komai nasu iri d'aya tun daga idanuwan su, hanci da bakin su da kuma sajen dake kwance luf a kyakkyawan fuskan su. Suman kansu neh ya bambanta, d'ayan yabar suman ya d'anyi tsayi d'ayan kuma ya bari dai-dai baida tsawo. Da na tsaye k'are musu kallo sai naga wanda suman kansa ya d'an fi tsowo yafi haske kad'an duk da dukkan su farare neh.
  A can wani gefe kuma wani saurayi neh wanda sa'an su zaune, wankan tarwad'a neh yana da manyan idanuwa, bakin sa d'an k'arami dashi, hancin sa dogo kamar biro da sajen sa wanda ya kwanta luguf akan fuskan sa, suman kansa bak'i k'irin yasha gyara, na kasa tantance tsakanin tagwayen maza da shi d'in wa yafi kyau..

  Matar ce ta gyara zama tace
"Nikam gaskia hankali na bai kwanta ba, wai ba kai da Farooq aka bada sunan ku da number'n ku a tura ku Jigawa ba, ya akayi shi ya samu kai baka samu ba, su rasa garin da zasu tura shi sai ma Calabar fisabillah"

  D'ayan 'yan biyun neh wanda suman kansa yafi tsawo ya fashe da dariya wanda yasa naga dimples nasa sun lutsa wanda ya k'ara fidda masa kyau yace
"Kai Ammi, toh ai da Maiduguri suka tura shi"
Dunkule ta masa tace
"Kaga bana son shashanci KHALEAL,Tab ai da kuwa sai dai a hak'ura da service d'in gaba d'aya, Yanzu nikam HAYDAR ya za'ayi neh?"
  D'ayan 'yan biyun  wanda ta kira da Haydar murmushi yayi wanda yasa fararen hak'oran sa suka baiyana da tsiririn wushiryar sa, gyara zama yayi yace
"Ammi ki daina damun kanki mana abu three months kawai zanyi zan  neman rediployment na dawo gida"
"Hmm Allah sa toh dan ni gaskia hankali na bai kwanta da calabar'n nan ba"

D'ayan saurayin dake zaune wankan tarwad'a yace
"Ammi ki daina damuwa please ba abunda zai samei shi In Shaa Allah"
  "Baza ka ganeh baneh FAROOQ, kasan halin abokin ka, kar ina zaune lami lafiya naga ya kawo mun mata 'yar can ba musulma ba yace zai aure ta"
  Da Khaleal da Farooq duk suka fashe da dariya, wani kallo Haydar yake musu irin sun raina shi d'in nan yace
"Haba Ammi nida naje England ma banzo da mata ba, naje Madina banzo da mata ba sai Calabar? Allah sawwaka"
Khaleal yayi dariya yace "Um um banda cika baki Allah dai ya rufa asiri"

"Ameen wallahi, dan nikam gaskia ban tsaman zan amince ba" cewer Ammi
  Khaleal yace "Why Ammi? Naga babban jihadi neh ai"
"Sosai kuwa babban jihadi neh amma we can't take the risk, tun abun da ya faru da marigayi Adamu, a lokacin da Hajiya Fauziya take ban labari nasha kuka, gaskia Farooq mamar ka tana da hak'uri" Farooq murmushi kawai yayi dan shima a duk lokacin da ya tuna abun duk da yana k'arami sai yaji jikin sa ya mutu likis.

  Tasowa duk sukayi Haydar yace
"Ammi yau kam a can gidan zamu kwana"
"Toh shikenan ba matsala but dan Allah kuzo gobe da safiya"
Farooq yace "Allah kaimu"
Ta amsa da "Ameen"

     Sanda suka fita a gidan Farooq da Khaleal suka k'ara fashewa da dariya, Farooq  yace wa Haydar
"Aboki nah Ammi tace tasan halin ka, ba wanda bai sanka da 'yan mata ba mutumina"
Had'a rai yayi yace "Kufa garori neh, ni duk 'yan matan da kake gani na dasu wallahi su suke bibiyata"
Khaleal yayi dariya yace "Ai kai d'in white blood neh da kai"
"Sosai kuwa asalin white blood ma" duk sukayi dariya.. Anan neh na k'are musu kallo sosai, wanda shi Khaleal yafi Haydar da d'an tsawo kad'an duk da dukkan su dogaye neh, sai dai shi kuma Haydar yafi shi da faffad'an k'irji kad'an duk da duk kansu suna da jiki irin mazan da ake so kamar John Abraham na bollywood , Farooq tsawon sa zaizo daidai da Khaleal kuma shima yana da broad chest da figure mai kyau'n gaske kamar Hrithik Roshan. Ni na kasa tantance tsakanin tagwayen maza da Farooq wa yafi kyau/had'uwa/tsaruwa..

Duk suka shiga mota k'irar Honda accord 2017, Haydar shi zaiyi driving, Farooq kuma yana gefen sa, sai kuma Khaleal da ya zauna a back seat.

  
   Tell me what you think ov the story

Your votes and comments shi zai bani more effort to post

Vote

Comment

Share

#AnaMugunTare

NIDA TAGWAYEN MAZA Where stories live. Discover now