CHAPTER SIX

422 38 1
                                    



    Washegari da safe  wanda ya kama ranar Monday, Lola ce akan gado ta rufu da blanket, Mami ce ta shigo d'akin tana
"Lola! Lola you better   wake up or you will be late for school". Tana mai bubbuga k'afanta, jan bargon Lola tayi ta bud'e idon ta wanda yayi k'anana yayi jazur unlike asalin idon ta wanda the dark is so dark and the white is excessively white, Mum take hankalin ta ya tashi tace
  "Daughter what happen? What is wrong with you? Are you sick?" Tana mai tattab'a jikin ta dasu wuyan ta, da k'yar ta iya bud'e baki tace
"Mami headache, a serious headache Mami, I can't go to school today" Tana mai rik'e kanta.
Kalan tausayi Mami tayi tace
"Ayyah so sorry dear, and your temperature is very high maybe it's fever and malaria, try and brush your teeth Dear and i'll bring your breakfast" Tana mai shafa fuskan ta.
Da sanyayyen murya tace
"Ohk Mami"
Mami ta fita a d'akin Lola kuma da k'yar ta iya tasowa akan gado ta fita waje tayi brush dan wani irin jiri ke d'aukan ta dan tun jiya abunda ya faru bata sake cin abincin ba kuma bata runtsa ba tana komawa d'akin ta taga Mami da plate na abinci, Plantain da doya neh soyayye, Mami tace
  "Come and eat Dear after that I will take you to the chemist"
"Ohk Mami". Zama tayi daram ta cinye abincin tas, bayan ta gama ci Mami tace
"Oya stand up let's go to the chemist"
Kwanciya tayi akan gado tace "Mami don't worry I will be fine no need for us to go to the chemist"
"Lola are you sure?"
D'aga kanta tayi tace "I will be fine Mami, let me have some rest please"
"Ohk as you said, let me call Abigail and tell her that you're sick you can't make it to school today so that she can tell your class master"
"Aiit Mami, can you excuse me now"
"Sure". Mami ta fita a d'akin, Mami tana fita taja bargo sai bacci daman jiya bata samu tayi bacci ba tana ta tunanin John....

   Haydar neh a gaban principal aka bashi zai na d'aukan SS3 da SS2 economics both science and Art....
Ransa duk b'ace ya shiga aji uku Art, a rayuwar sa ya tsana teaching, bayan ya shiga yayi introducing kanshi da suna Aliyu Badamasi, sosai 'yan ajin suka sha wutan sa, kowa sai yaba kyawun sa suke, duk da basu son northerners amma ya musu, matan kowa sai tofa albarkacin bakin sa yake, Abigail ce ta kura masa ido tana kallon sa, shi kuma ya lura da irin kallon da take masa, sosai abun yake k'ona masa rai dan ya tsana a saka shi gaba a ta kallon sa, ba ma ita kad'ai ba har sauran matan aji sai dai nata yafi worst, dan tagumi tayi ta zuba masa ido ba koh k'yiftawa har ya cinye time nasa ya fita...

  Lola ce kwance akan gado tana sharkan baccin ta Abigail ta shigo d'akin, bubbuga ta da k'arfi take tana fad'an
"Lola abeg please wakeup"
A hankai Lola ta bud'e idon ta wanda suka rine tace
"What Abigail? Abigail what? Mtsww"
"Anhh Lola!"
"You know I hate it when someone wakes me up when I am sleeping"
"Abeg jare stand up, your Mum told me you're sick that you have fever but I know you're lying, it just what happened yesterday between you and John that is still bothering you"
"Mts God forbid, I've even forgotten about him"
Dariya sosai Abigail tayi tace
"You can't be serious Lola, Abeg wake up lemme gist you"
Da k'yar ta iya tashiwa ta zauna tace
"I am all ears what happen?"
"Emmm Qyeen...I've never see a handsome guy like Aliyu"
D'an guntun tsaki taja tace
"And who the hell is this Aliyu? A hausa boy? Where do you met him?"
Gyara zaman ta Abigail tayi tace
"Yes a hausa boy! He was send here in our school for his primary assignment"
Rolling eyes nata Lola tayi tace "A corper?"
Da excitement tace "Yeah a corper!"
Dogon tsaki Lola taja tace
"What is wrong with you Abigail? What the hell is wrong with you? Every freaking year you fall for every corper that is being assigned here, and after they all used you they dumped you at every end. The southerners dumped you, even the westerners and the guys from east dumped you at end. So this northerner, this hausa boy will also dump you after he use you. Infact I know this hausa boys, he won't even love you, he won't fall for your stupid trab"
B'ata rai tayi Abigail tace
"What do you mean by that?"
Tasowa tayi tace "You heard me well Abigail, that hausa boy won't fall for you"
"Hausa boy!hausa boy! Lola did you forget that your father is also a hausa man and he fell in love with...."
Ran Lola neh yayi bugun b'aci ta dakatar da Abigail tace
"Don't you dare talk about my dad again"
D'aukan jakan ta Abigail tayi tace
"Aiit bye, till we meet tomorrow in school. I am sorry if i wronged you in any way"
Lola koh kulata batayi ba, Abigail har ta kai bakin k'ofan d'akin ta juya tace
"Ehen Lola! There will a party at 12:00 am, I think you should come to get over John"
Lola tunani ta d'an tsaya yi tace
"Where?"
"At Paul's house"
"I will see what I can do"
"Aiit goodbye"
"Bye"

  
   Bayan Abigail ta fita a gidan Lola tunani ta fara yi ta yaya zata fita a gidan k'arfe sha biyun dare, sai can kanin maman ta ya fad'o mata a rai wanda suke zauna duk gida d'aya, d'an murmushi tayi tace "Yessss!"

     *Kano*

     Farooq zaune yake a d'akin sa rik'e da hoton yarinya k'arama wacce baza ta haura shekaru biyar ba, Yesmin ce tana ta sallama ba'a amsa mata ba ta cusa kai ta shiga cikin d'akin, ganin Farooq tayi rik'e da hoto ya kurawa hoton ido, tab'a sa tayi take ya dawo cikin haiyacin sa, murmushi tayi tace
"Baka rabuwa da hoton Khadeejah"
Sosa suman kansa yayi yace
"I think of her every day, every hour, every minute, every second, and every moment of my life"
Zama Yesmin tayi a kusa dashi tace
"Don't worry Yaya Farooq, In Shaa Allah one day she will definitely look for her father's relatives"
  "I earnestly pray for that day"
  Murmushi Yesmin tayi tace
"Yanzu Yaya ka kaini wajen tela nah na karb'a kaya nah"
"Mtsw ni kam wai yaushe zaki koya driving neh? Ina driver ya kaiki mana"
Turo bakin ta tayi tace "Ammi fa ta aike sa market"
D'an guntun tsaki yaja yace "Kije ki ni yanzu bacci nake ji idan na tashi i will let you know sai muje"
B'ata rai tayi tace "Toh shikenan"
Zata fita taji yace "Ki jirani a waje yanzu zan shirya muje"
A take ta juya tana murmushi tace "Thank you My Yaya"
D'an b'ata rai shima yayi yace
"Koh sai na canza mind na neh, nace kije zan same ki"
Take ta fita a d'akin tana dariya, jallabiyan dake jikin sa ya cire ya saka T-shirt red da wando jeans black, ya d'au p-cap bak'a ya saka a kanshi da wando snickers mai tsadan gaske black & red, ya d'au agogon shi k'irar Armani ya saka, ya fesa jikin sa da turare, sosai yayi kyau, kyau'n ma ba a magana, d'aukan car key'n shi yayi ya fita haraban gidan, yana fita sai ga Khaleal shima ya fito wanda shima k'ananan kaya neh a jikin sa, rigan sa bak'i wanda ya d'an kamashi ya baiyanar da broad chest nasa, da hannun sa wanda kallo d'aya zaka masa kasan yana cin gym, sai wandon sa fari, da p-cap da snickers dake kafan sa bak'i, sosai ya amshe sa ya masa kyau abu da farin mutum..
Ganin Farooq da yayi ya d'an tako kusa dashi yace
"Ya ina zuwa?"
Farooq wanda koh d'aga kai baiyi ba balle ya kalle sa yana danne-danne da wayarsa yace
"Any problem?"
Yesmin wanda yanzu ta fito ta canza kaya ta saka bak'ar Abaya tace
"Yaya Khaleal wajen tela na zai kaini na karb'a kaya nah"
D'an b'ata rai yayi yace "Ina drivers na gidan nan?"
"Duk basu nan"
Wani kallo Khaleal ya watsa mata yace
  "You know I hate lies, yanzu naga Madu driver kice duk basa nan"
Take Farooq ya d'aga ido ya kalle ta, ita kuma take hawaye ya cika a idon ta tace
"Nifa ban san yana nan ba d'azu na duba shi baya nan"
Wani irin bak'in ciki taji dan ita tafi son Farooq ya kaita, a duk lokacin da suke tare ji take farin ciki ya lullub'e ta, takan ji wani irin farin ciki mara misaltuwa. Khaleal neh ya kwala wa Madu kira, sai gashi Madu ya amsa take yazo inda suke tsaye, Khaleal yace
"Ka kaita wajen telan ta yanzu yanzun nan"

"Toh Oga an gama"

  Hawaye taji shar shar yana sauk'a akan kuncin ta, Madu d'aukan mota yayi ya kawo har wajen inda suke tsaye yace
"Hajiya Yesmin zo muje koh"
Sai anan Farooq ya d'aga kansa ya kalle Madu yace
"Ka maida motan zan kaita"
Yesmin wani irin farin ciki taji a ranta, Khaleal kuma take ya d'aga kai ya kalle Farooq yace
"Nifa I don't freaking mind koh China zaka kaita"
D'an gyara tsayuwar shi yayi yace
"Then why are you interfering, it's non of your business? "
D'aga kafad'an sa Khaleal yayi yace
"Yeah you're right! It's non of my fucking business". Khaleal shiga cikin motan sa yayi ya barsu, Farooq shima ya shiga cikin motan sa Yesmin ta zauna a kujeran gefen sa, ya tada motar kenan Khaleal ya bud'e glass na motar sa yace
"Dad ya taso kuma in next 20mins jirgin su zai sauk'a, he called you baya shiga ya kirani na fad'a maka, kuma yana zuwa gida idan ya shirya yace zamu kaishi yaga buildings namu, so kaga baka da time, yanxu the choice is left for you, is either ka kaita wajen telan ta or muje airport"


Vote

Comment

Kar ku gaji da rashin post pls

Abubuwa too much for me

NIDA TAGWAYEN MAZA Where stories live. Discover now