CHAPTER SEVEN

407 33 3
                                    


     Farooq tsayawa yayi yana kallon Khaleal, baiyi mamaki ba dan yasan wannan halin sa neh, d'an juyawa yayi ya kalla Yesmin yace
"Sis kiyi hak'uri please kije Madu ya kaiki"
Yesmin ba yadda ta iya duk da taji bak'in ciki sosai, so take tace toh suje da yamma amma tana tsoro tace
"Toh shikenan ba komai" zata bud'e k'ofa ta fita a cikin motar yace
"No tsaya karki fita, bari na fita Madu ya kaiki da motan ni zan bi Khaleal"
"Ohk toh"
Fita yayi a motan ya kwala wa Madu kira, sai ga Madu'n ya fito, Farooq yace
"Amm something came up wallahi please ka kaita wajen telan ta"
"Ohk Oga ba matsala"

Bud'e motan Khaleal Farooq yayi ya shiga, yana shiga Khaleal ya tada motan sai hanyan airport, suna hira har suka iso airport d'in.

Jira sukayi har kusan minti talatin kan jirgin Daddy ya sauk'a. Tun a nesa suke murmushi da suka hango sa, namiji wanda bazai haura hamsin ba wankan tarwad'a, kallo d'aya zaka masa ka tabbatar da bafulatanin usul neh. Ware hannayen sa yayi sai gasu duk sun shige ciki, dariyan manya yake yana bubbuga bayan su yace
"Yara nah it been long, hope na same ku cikin k'oshin lafiya?"
Murmushi duk sukayi suka amsa da
"Alhamdulillah".
   Jiran kayan sa sukayi bayan an kawo suka cusa a bayan mota, daga nan sai asibiti. Mummy ba k'aramin farin ciki tayi ba da ta kalla mijin ta, sosai suka gaisa da Ammi ta mik'a masa baby, har hawaye yayi dan farin ciki. Daga nan ya shiga wajen likita yayi requesting a sallame ta, ba tareda b'ata lokaci ba aka rubuta mata takardan sallama.
  Daga nan duk aka tattara kayan su sai gida, suna zuwa kowa yayi wanka. Daddy, Khaleal da Farooq sun had'u suna cin lunch, Daddy yayi gyaran murya yace
"Abban'n ku yana lagos munyi waya dashi, yanzu idan mun gama cin lunch sai naje na kalla buildings naku"
Duk suka amsa da "Toh"
Bayan sun gama suka shiga wani motan Daddy Ferari fara sol mai d'an karen kyau, Khaleal neh yake driving sai Daddy dake gefen sa sai kuma Farooq dake baya. Sosai sukayi tafiya kan suka iso wajen.
  Ma'aikata neh dayawa a wajen sai kai da kawo wa da suke, babban waje guda biyu neh duk suna facing juna wanda har yanzu basu gama ba uncompleted building neh balle na gano muku me suke ginawa. Bayan Daddy sun sauk'a sunyi magana da engineers na wajen da sauran ma'aikata suka zagaya duk waje biyu d'in, sosai suka gaji dan wajen ba k'aramin babba baneh. Daga nan suka hau motar su suka kama hanyan gida.

*Calabar*

     Lola ce zaune a parlour tayi tagumi tana tunani ta yadda zatayi ta fita a gidan k'arfe sha biyun dare, kanin Mami da take tunanin zai taimaka mata ta fita bata ganshi ba har kusan goma da rabin dare, tayi trying number'n shi baya shiga dan daman k'auyen mostly network nasu ba kyau. Mami ce ta fito a d'akin ta ganin Lola tayi tagumi yasa ta tako har zuwa inda take, hannun ta ta aza a wuyan Lola tace
  "Lola how are you feeling now?"
D'an yamutse fuska Lola tayi tace
  "Mami I am feeling better"
"Yeah I can feel that your body temperature is somehow normal now, don't forget to take your medicine before going to bed"
"OK Mami". Mami zata shiga d'akin ta Lola tayi saurin cewa
"Ammm Mami!". Mami take ta tsaya cak tace
"Yes Dear"
D'an sosa suman kanta tayi tace
"Uncle Peter is still not yet back and is getting late"
"Ohhh mtsw! He traveled to the city in the morning but he'll be back in next few days. He wanted to woke you up before he goes but I told him not to cox you ain't feeling well"
D'an sosa suman kanta tayi tace
"Ohh ayyah"
Mami kallon ta ta tsaya yi tace
"Any problem?"
Take ta girgiza kanta tace
  "Not at all Mami"
"Ohk, lemme close the door". Take tazo gaban Mami tace
"Mami just give me the key I will lock it you don't have to worry yourself"
Mami kallon ta ta tsaya yi tasan dai Lola akwai wani abun da take shiryawa dan tasan ta bata k'aunar rufe k'ofa, tace
  "No I will do it myself, just go and sleep it's getting late and you ain't feeling well"
Lola ta rasa meye kuma zata ce tace
  "OK Mami". Ta shige d'akin ta, Mami d'aukan key tayi ta rufe k'ofan.
   Lola sai duba time take da wayar ta, take ta dannawa Abigail call tayi sa'a yashiga, tana picking tace
"Hello Abigail"
"Lola hope you will attend this party, you just can't miss ohh"
"Mtsw Abigail I seriously don't know what to do, Mami locked the door and the key is with her. And even I if I steal the key and try to open the door later at night you know the door makes sound and she might caught me". Cusa hannu tayi cikin suman kanta tacigaba
"I really don't know what to do Abigail, think of a way out to get me out of this hell house"
Abigail itama shuru tayi tana d'an tunani, ganin shurun yayi yawa Lola tace
"Abigail are you there?"
"Umm Yes, I'm thinking of a way out. That old door of yours won't get you out safely even if you try to steal the key"
"Yessss ohhh Abigail"
Ji tayi wayan ya katse kud'i ya k'are, wani dogon tsaki taja tace
  "God help me I seriously wanna attend this party I just can't miss it"
Ji tayi message ya shigo wayan ta take ta bud'e taga Abigail
  _"Hea I tried to call you but the network is soo bad. Why not you should make tea add cocodamol and give it to her. I am freaking sure if she take it she will have a very sound sleep. She might even not wake up uptill next life (lol)"_
  D'an guntun murmushi tayi tace "Ohh Emmm Geee Abigail you wicked". Take ta tashi akan gado taje parlour ta d'au flask wanda yake cike da ruwan zafi ta zuba a cup guda biyu ta saka lipton da sugar, shiga d'akin ta tayi ta d'au wani magani wanda nake da tabbacin shineh cocodamol da Abigail ta fad'a mata, guda biyu ta jefa a d'ayan cup na tea d'in ta gauraya ta d'auka ta fita da shi sai d'akin Mami. A lokacin Mami ta durk'usa tana addu'a, bayan ta gama Lola ta amsa "In Jesus Name Amen!"
Mami murmushi tayi tace
"Lola you're still awake?"
"Yes Mami I couldn't sleep"
"Hope all is well?"
"Yupp Mami". Mik'a mata cup na tea d'in tayi wanda ta zuba kwaya guda biyu a ciki tace
"Mami have this". Murmushi Mami tayi tace
"Awww Thank You Dear" Ta karb'a tea d'in, Lola tace
"You are welcome"
Mami kurb'an tea d'in take a hankali tace
"So what's up?"
D'an murmushi Lola tayi tace
"Nothing"
"I don't believe you, just tell me"
Gyara zama tayi tace "Mami I wanna apply for Bayaro University Kano in my JAMB"
Take Mami ta ajiye cup na hannun ta tace
"Why? There are many good universities in south,west and east. Why in the north?"
Murmushi Lola tayi ta d'au cup na tea na Mami'n ta mik'a mata tace
"Finish your tea Mami, if you don't like it is ok"
"Not that i don't like it, is just that....". Bata k'arasa maganan ba Lola tace
"Shhhh just finish your tea Mami and is fine if you don't like it". Ita dai Allah Allah take ta shanye bacci ya d'auke ta Suna cikin hira har bacci ya d'auke Mami, ganin tayi bacci take ta d'au key na k'ofan, zuwa d'akin ta tayi ta canza kayan jikin ta, wani gown ta saka wanda babu hannu ta d'au wayar ta. A hankali ta saka key ta bud'e k'ofa, duk yadda taso k'ofan kar yayi k'ara amma inaa sanda yayi k'ara, a sand'a ta fita a gidan.
   Garin shuru baka jin k'aran komai sai na tsuntsaye, Allah ya sota garin akwai wutan Nepa koh ina da haske, sanda tayi d'an tafiya sannan taje k'ofan gidan su Abigail, wayar ta tacire ta danna mata kira, da k'yar ta samu ya shiga sabida network, ringing d'aya ta katse wayan sabida ba kud'i a ciki. Cikin minti biyu sai ga Abigail itama ta fito a gidan su, Jan Lola tayi suka bar k'ofan gidan, sanda suka d'an yi tafita kan Abigail ta sake hannun ta.

   I didn't get time to edit, but In Shaa Allah zanyi editing idan na samu time. You might find the spelling or the grammer wrong so please bear with me!!!

Vote

Comment

Share

NIDA TAGWAYEN MAZA Where stories live. Discover now