Page 20

625 53 19
                                    


Hi Readers☺ Please don't forget to press the star bottom... Vote! And Share To Your Love Ones😀😊 Thank You!
     
           Motan ta direct ta d'auka da gudu suka bar haraban asibitin. Wani irin rikitaccen gudu take wanda Lola hankalin ta yayi mugun tashi, ita bata tsaida motan ba har sanda ta gansu a cikin garin kaduna.

   Farooq yana shiga cikin asibitin ya had'u da Doctor d'in, Dr'n yayi murmushi yace "Farooq I'm so glad I meet you daman yanzu gida nake so na tafi, sister'n ka ta tashi Alhamdulillah" Wani irin sanyi Farooq yaji a zuciyan sa da wani masifan farin ciki mara misaltuwa, take ya washe fararen hak'oran sa yace
"Thank you Dr"
Nan take da gudu-gudu yayi hanya zuwa d'akin,  to his very own surprise yana bud'e k'ofa yaga d'akin wayam ba kowa, zuciyan sa neh yayi wani irin bugawa, wani zuciyan sa yace Farooq calm down maybe wannan ba d'akin baneh you entered the wrong room, fita yayi a d'akin ya dubu k'ofan d'akin yaga same room number neh ROOM 2B VIP. Da gudu ya k'ara komawa ya shiga cikin d'akin yana fad'an "Khadeejah! Khadeejah! Khadeejah!" Har toilet yashiga yaga wayam ba kowa, da gudu ya fita a d'akin ya shiga d'akin dake kusa dasu hankalin sa tashe yace "Dan Allah bakuga Khadeey ta ba?"
Dattijuwan da d'azu ta bawa Aunty Mary hijab tace "D'azu dai Aunty'n ku ta shigo ta amsa hijab wai zatayi sallah"
Take ya fita a d'akin da gudu yaje wajen securities, a tsawace cikin tashin hankali yace
"Where is my sister? Ina yarinyan da na kawo ta nan?"
Kallo-kallo suka farayi d'ayan ya amsa "Sir ka duba cikin d'akin mai kyau or maybe tana cikin toilet". Tas! Farooq ya wanke sa da mari mai rai da lafiya ya kama collar na rigan shi yace
"Did you just called me blind? Na duba mai kyau koh? banda ido neh? Koh an fad'a maka ni makaho neh? Wallahi Allah idan ban ganta ba sai na kulle ku! Wallahi sai na kulle ku! Meye aikin ku? Taya zaku barta har ta fita a cikin hospital d'in nan in this her condition? Wallahi bazan barku ba, kuma yanzu yanzun nan ku nema mun ita a cikin asibitin nan". Yana gama fad'an haka ya sake collar'n yana yawo a cikin asibitin yana kiran "Khadeey!!!!!!!!!"

  Fita yayi a asibitin ya tada motan shi haka ya ringa zagaye cikin Abuja koh Allah zai sa a ganta amma shuru, komawa yayi asibitin koh sun ganta wani mutum neh yace ai yaga sun shiga mota tun da rana sun bar asibitin. Da k'yar ya iya barin asibitin ya koma hotel da yake zama da misalin k'arfe d'aya na dare ba wai dan ya hak'ura da neman ta ba. Yana zuwa yayi alwala yayi sallah yana hawaye yana mai rok'an Allah ya nuna masa 'yar uwarsa Khadeejah, baccin da bai samu yayi ba kenan sai bayan sallah'n Subh yana idar wa bacci ya kwashe shi.....

     *Calabar*


   Haydar tun zuwan sa Bakassi yake neman yarinyan da koh sunan ta bai sani ba, a haka yaji sam garin baya masa dad'i, shi har abun ya fara bashi tsoro anya kuwa mutum ce ba aljana ba, haka dai shi kad'ai yata tunani gashi a matse yake he need someone beside him.
    Zaune yake a cikin office nashi wanda aka ware masa a makarantan shi kad'ai yana tunanin anya bazai tattara kayan sa ya bar garin ba, knocking na k'ofan akayi, da husky voice nasa yace "Yes come in"
Abigail ce ta shigo tana wani irin shu'umin murmushi, kallon sa take tana wani cije lips nata, Haydar sama da k'asa yake kallon ta, a zuciyan shi yace 'Not bad'. D'an b'ata rai yayi yace
"Any problem?". D'an kame-kame ta farayi tace "Ummm Sir I missed your C.A test yesterday"
"And so what?" Ya tambaye ta yana mai kallon cikin kwayan idanuwan ta. Cusa hannu tayi cikin suman kanta tace
"Makeup test sir" ta fad'a tana mai tsoron amsan da zai bata. D'an kawar da fuskan sa yayi gefe yace
"Meet me later in my house"
Da sauri ta d'aga idanuwan ta ta kalle sa cox she never expected this, wani irin murmushi tayi tace
"Thank you Sir"
Koh kulata baiyi ba haka ta fita a office d'in tana mai jin dad'i, tana fita Haydar ya fashe da dariya yace "Ke ba 'yar iska ba zan koya miki hankali"

    Da daddare misalin k'arfe takwas na dare Haydar na zaune yana kallon film a wayan sa yaji ana knocking masa k'ofa, tasowa yayi ya bud'e dan already har ya rufe k'ofan dan yasan babu mai zuwa masa. Abigail ce tasha kwalliya, wani riga off shoulder ta saka wanda rabin fulanin ta a bud'e yake, da wani mini skirt. Yana ganin ta ya bata hanya yace "Come in" Bayan ta shiga ya rufe k'ofan, neman waje tayi ta zauna tana mai k'arewa d'akin kallo. Shima bayan Haydar ya zauna tayi k'arfin hali tace
"Good evening Sir"
Haydar amsa mata ciki-ciki yayi yace "Evening"
"Umm Sir I am here for the test"
D'an kallon ta yayi yace
"Ohk"
Mik'a mata question paper'n yayi yace "10mins"
Da sauri ta amsa ta fara answering dan fill in the blank neh shi kuma ya koma yacigaba da kallon film nashi yana kallon time, minti goma na cika yace "Time up". D'an murmushi tayi tace
"I am done already". Thank you Sir Aliyu" ta mik'a masa paper'n. Karb'a yayi ya ajiye shi ya cigaba da kallon film nashi, sai can kusan minti goma taga bai k'ara kulata ba tace
"Sir I'm going"
"Ohk" Ya bata amsa a takaice, abun taji zafin sa sosai, shi kanshi Haydar ta tada masa da sha'awa amma ya dake a zuciyan sa yace "Ai zata raina ni, ba yau ba amma sai gaba ta raina kanta" Yana wani irin shu'umin murmushi.
Haka nan ta fita a gidan jikin ta babu kwari dan ba haka ta so ba.

*Abuja*

    Farooq bai tashi a bacci ba sai kusan k'arfe goma na safe, a firgice ya tashi ya shiga wanka ya saka kayan sa, bayan ya shirya ya fita neman Khadeejah, haka ya ringa yawo a garin Abuja koh Allah zai sa ya ganta amma shuru........

   Sati d'aya shur yana neman Khadeejah babu ita ba labarin ta, yayi mugun rama yayi bak'i. Zaune yake a cikin d'akin sa yayi tagumi yana tunanin ina zai fara neman Khadeejah, wayan sa ya fara ringing, 'Mummy' ya gani baro-baro akan screen na wayarsa, picking call d'in yayi ya saka a loudspeaker ya ajiye wayan a gefen sa ya kwanta yace
"Hello Mummy" Ajiyan zuciya ta sauk'e tace
"Ya akayi Habibi?"
Muryan sa yana shaking yace
"Lafiya kalau Mummy"
"Noi sarei? "
"Alhamdulillah Mummy"
Mummy d'an shuru tayi na some secs kan tace
"Habibi baka Lagos, an fad'a mini bakaje ba, kuma Uncle Tukur ya fad'a min baka gidan sa. Habibi where are you? Where are you my son? I am so worried wallahi koh abinci bana iya ci, it been a week now ina jira ka fad'a min amma shuru kace min kana lagos kuma ba haka baneh. Yaushe ka fara b'oye min abu Umar? I am your mother for goodness sake, ka fad'a min abunda ke damun ka, ka fad'a min kana ina zanzo na same ka"
Hawaye neh shar shar shar suka fara sauk'a akan kuncin sa, muryan sa na rawa yace
"Mummy ba komai fa, Mummy ki yarda da ni"
Mummy muryan ta na rawa tasan tabbas akwai abunda ke damun Farooq, ji tayi kamar yana kuka, hankalin ta yayi mugun tashi tace
"Habibi zan fita neman ka tunda kai bazaka fad'a min inda kake ba, so kake hawan jini ya kashe ni?"
Farooq bai san lokacin da ya fashe da kuka ba yace
"Mummy I saw her! Mummy I saw her!"
Hankalin ta neh ya k'ara tashi tace "You saw who Habibi?"
Cikin kuka yace "Mummy I saw Khadeejah! Khadeejah 'yar uwata, jini nah"
Mummy tuni itama ta fara hawaye tace
"Habibi where are you now?"
"I am in Abuja"
"Ohk just send me your address I'll come and meet you there"
"Mummy don't worry yourself zanzo ni Kano gobe In Shaa Allah"
"Promise?"
"I promise"
"Ohk Habibi Allah kaimu, don't worry yourself kaji? Watarana In Shaa Allah Khadeejah zata dawo garemu, da k'afan ta"

       Nana Fa'ad

NIDA TAGWAYEN MAZA Where stories live. Discover now