Page 21

492 41 15
                                    

D'an ajiyan zuciya ya sauk'e yace
"Allah sa Mummy"
"Now stop worrying yourself kaji Habibi? In Shaa Allah everything will be alright I promise"
Haka Mummy sanda taga hankalin sa ya d'an kwanta kan ta kashe wayan, bayan ta katse wayan take ya hau net yayi booking flight da zai kaisa kano, yayi sa'a da safe akwai wanda zai tashi zuwa Kano.

Washegari

Kano

Tun k'arfe goma sha d'aya jirgin su yayi landing a kano, Mummy da kanta tayi driving tazo ta d'auke sa a airport. Bayan ya shiga motan ya zauna Mummy murmushi tayi taga cikin 'yan kwanakin nan har ya fad'a yayi duhu tace
"Farooq how are you?"
D'an guntun murmushi yayi yace
"Mum I am fine"
"I know you're not, but bara muje gida first I cooked your delicious meal"
Tada motan tayi haka har suka isa gida babu wanda yace uff, bayan sun isa gida Mummy tace
"Habibi kaje kayi wanka first sai kazo kaci abincin ka"
"No lemme see Samha first, I missed her alot"
D'an dariya tayi tace "Samha tana d'akin ta, muje ka ganta". D'aki neh babba yasha kayan alatu da kayan wasa iri iri sai kace shago guda na siyar da kayan babies suka shiga anyi painting purple da pitch. Wata yarinya ce k'arama wanda bazata haura shekaru goma sha biyar ba rik'e da Samha, tana ganin su ta mik'awa Mummy samha'n ta durk'usa har k'asa ta gaishe da Farooq, d'an sama-sama ya amsa gaisuwan yana mai kawar da fuskan sa dan take yaji wani irin wari da k'auri na buzaye. Mummy mik'a masa Samha tayi akan ya karb'e ta, girgiza kansa yayi yace
"No Mummy ki bari sai kun mata wanka first"
With a surprising look take kallon sa tace
"What do you mean?"
Juyawa yayi yana fita a d'akin yace "Nothing Mummy, I am just saying sai kin mata wanka tukun, kuma karki bawa kowa ya mata wanka ke nake so ki mata wankan"
Yana gama fad'an haka ya fice a d'akin, Mummy girgiza kanta tayi tace
"Hindu bara nayi mata wanka, kema sai kiyi wanka ki shirya kije islamiya"
Yarinyan da aka kira da Hindu ta k'ara durk'usawa tace
"Toh Hajiya", Murmushi Mummy tayi tace
"I told you times without number ki daina kirana da Hajiya, just call me Mummy kinji?". Ita Hindu wanda ba turanci take ji ba amma ta ganeh abunda take nufi tace
"Toh Mummy"
"Yawwa good girl, koh kefa?"

Bayan Mummy ta shiga d'akin ta tayi wa Samha wanka ta fito dinner amma shuru babu Farooq, wuce side nasa tayi tana sallama, can sai a Farooq yafito a d'akin sa sanye da farar jallabiya yana k'amshin perfumes fuskan sa fayau kamar wani mara lafiya, d'an murmushi Mummy tayi tace
"Naji ka shuru baka fito ba?" D'an sosa suman kansa yayi yace
"Wallahi Mummy yanzu nake shirin fitowa"
"Okay toh muje koh?"
"Toh". Karb'an Samha yayi daga hannun ta yana mata wasa haka har suka iso kan dinning d'in, bayan ya zauna Mummy tayi serving masa abinci ta tura masa gaban sa, kallon ta yayi dan irin yawan abincin da ta zuba masa, b'ata rai tayi tace
"Eat it all"
Shuru yayi yana kallon abincin da ta d'ura masa a gaban shi
"Mik'o mini ita?"
Mik'a mata Samha yayi tace "Oya start eating, kaga yadda ka rame kuwa?"
"Okay" sai ya fara ci
D'an murmushi tayi tace
"Koh kai fa?"

"Hindu! Hindu! Hindu!" Mummy ta fara kwala wa Hindu kira, take ya ajiye spoon dake hannun sa yace
"Who re calling Mummy?"
"Mai rainon Samha, tazo ta kwantar da ita bakaga tayi bacci ba?"
Ajiye spoon na hannun sa yayi yace
"Mummy idan kina so naci abincin nan dan Allah karki kira mun yarinyan nan, I don't wanna perceive that filthy smell"
Kallon mamaki take masa tace
"What smell?"
"Mummy bakiji tana warin baroroji ba?"
"Haba Son! Ka daina fad'an haka, wallahi ni dai bana jin komai"
"Idan bakya ji please ni don't call her here, kuma idan baza ki iya rik'e Samha ba ni da kaina zan ringa rik'eta, tayaya zaki na bawa wata tana rik'e mun k'anwa neh for goodness sake Mummy?"
"Habi....." bata ida abunda take so ta fad'a ba sai ga Hindu ta fito, take Farooq ya tashi ya bar kan dinning d'in ya shige b'angaren sa..
Mummy murmushi tayi da taga Hindu a cikin kayan Islamiyan ta tayi kyau abun ta, tace
"Au har kin shirya zuwa makaranta koh?"
Kanta na kallon kasa tace "Eh Mummy"
"Okay! Daman inaso ki kwantar da Samha neh amma ki bari kawai zan kwantar da ita"
"A'a ki kawo na kwantar da ita man hajiya"
"No ki bari ba komai ki tafi kawai"
"Toh shikenan Hajiya sai na dawo"
"Yawwa"
Ta juya har tayi taku uku Mummy tace "Hindu"
Take Hindu ta juya tace
"Na'am Hajiya" Tana mai matso wa kusa da Mummy, Mummy tayi murmushi tace
"Sau nawa zan fad'a miki ki daina kira na Hajiya, call me Mummy okay? Koh baki d'auke ni uwa ba?"
Take Hindu ta girgiza kanta tace
"A'a Mummy kiyi hak'uri"
D'an guntun dariya Mummy tayi tace
"Tam shikenan, sai kin dawo. Allah kiyaye hanya"
"Ameen Mummy". Ta juya tana tafiyan ta a sanyaye, Mummy tana son Hindu ba dan komai ba sabida marainiya ce, ga uwa uba hankali da nutsuwa. Hindu yarinya ce kyakkyawan gaske, fara ce amma hasken ta ba can ba, tana da manya-manyan idanuwa da hancin ta tsit kamar pencil, sai bakin ta wanda daidai ya dace da fuskan ta.

Mummy bayan ta kwantar da Samha a d'akin ta ta wuce b'angaren Farooq, zaune ta tarar dashi yana danne-danne da wayar sa. Zama tayi a gefen sa tace
"Son how are you?"
Muryan can k'asa-k'asa yace
"Alhamdulillah Mum"
Karb'an wayan hannun sa tayi ta ajiye a gefe ta kama hannayen sa
"You saw Khadeejah?"
Take yaji tunanin ta ya dawo masa fil a cikin brain nasa yace
"Mummy I saw Khadeey, you can't believe how beautiful she is"
"Kana nufin tafi da kyau?"
D'an murmushi yayi yace
"You can't compare Mummy, her dimple, her fair skin and everything"
"Wow! I wish nima na ganta, yanzu tana ina?"

Writer's Note

Hello My Dear Ones

Pls bare with me cox i have to complete DUNIYA INA ZAKI DAMU BEFORE I PROCEED THIS STORY
I PROMISE YOU YOU WON'T REGRET READING IT, IT'S HALF TRUE LIFE STORY.
THANK YOU
I LOVE YOU ALL❤️🥰🥰🥰

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Jun 29, 2019 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

NIDA TAGWAYEN MAZA Where stories live. Discover now