CHAPTER FIFTEEN

436 32 2
                                    


    Yana sauk'a a Abuja ya nema hotel kusa da airport yayi booking, akwai gidan su Abba'n Siyama amma baya son tsayawa a gidan dan Baba Hawwa zata addabesa da maganar auren shi da Siyama bayan shi ba sonta yake ba, Nordic Villa Hotel yayi booking wanda yake kusa da airport a lokacin k'arfe goman safe, kwanciya yayi akan gado yana ta tunanin ina ma zai k'ara ganin yarinyan can wanda baisan sunan ta ba, ganin tunanin bazai taimaka mishi ba ya jawo wayar sa ya danna ma Siyama kira, tana picking yace
"Kina Abuja neh?"
"A'a, kana...." bata k'arasa maganan ba ya katse wayan, neman number'n Jamila yayi yana ringing d'aya ta d'auka tace
  "Hello Dear"
"Jamila kina Abuja?"
"Eh! Ba kana Cross River baneh?"
D'an guntun tsaki yaja yace
  "Kizo ki same ni a Nordic Villa room 148 D yanzu"
"Ohk"
Tana gama fad'an Ohk'n ya katse wayan, shiga cikin toilet yayi yayi wanka ya d'aura towel, jin k'aran bell ana dannawa yasa yaje ya bud'e k'ofan. Wata yarinya ce kyakkyawan gaske wankan tarwad'a doguwa, sosai take da kyau mashallah, tana ganin sa take ta shige jikin sa tace
"Dear I miss you alot"
K'ara manna ta yayi da jikin sa yace
"And I missed you more"
Tana nan shige da jikin sa ya rufe k'ofan, wani irin kiss ta soma masa kamar wata mayunwaciya, d'an raba jikin sa yayi da nata yace
"Kinsan bana haka ki shiga kiyi wanka"
D'an zare idanuwan ta tayi tace
  "Yanzu fa na fito a wanka nazo nan"
Barin ta yayi ya tako gaban dressing mirror ya fesa jikin sa da body sprays yace
  "Nidai ki shiga kiyi wanka"
Ba yadda ta iya a haka ta tub'e a gaban sa ba tsoron Allah  (wa'iyazubillah) ta fad'a toilet koh neman towel bata yi ba, nidai nace kyawun ta na banza.. Tana fitowa ya d'auke ta cak ya dira ta akan gado, gaba d'aya jikin ta yake mata wani rikitaccen kiss yana shafa duk ilahirin jikin ta yana murzata ta koh ina, ita kuma sai nishi take tana mai k'ara shigewa jikin sa................

   Da misalin k'arfe bakwai Haydar ya raba jikin sa da Jamila, shiga toilet yayi yayi wanka, bayan ya fito yayi shirin sa tsaf yayi sallah'n Isha. Dauk'an jakan sa yayi ya bubbuga Jamila wanda da shigan sa toilet har bacci ya kwashe ta yace
  "Ni zan wuce"
A hankali ta bud'e idanuwan ta cikin muryan bacci tace
  "Ohk toh sai mun sake had'uwa, don't forget to give me a call Durlin"
  "Koh zaki komo Cross River inda nake aiki?"
Murmushi tayi tace "Haydar kenan, ka barni a nan kai kanka kasan idan ba dan talauci ba ba abunda zai sa in saida jiki nah, iskancin da nake haka ya isa ba sai naje na zauna da kai a wani garin arna ba"
D'aga kafad'an sa yayi irin bai damu ba ya cire waya a jikin sa, transfer ya mata na dubu d'ari biyu a take yace
  "I transferred you kud'in mota ki koma gida"
"Aiit" Tana mai duba wayan ta
"Banga alert ba inaga network neh, but idan ya shigo I'll give you a call"
  "Ohk" Yana mai d'aga jakan sa tace
"Bye"
Fita yayi ba tareda da ya k'ara cewa uffan ba, yana fita ya tsaida da taxi, cikin minti biyar ya kaisa airport.....


     *Kano*

   Da misalin k'arfe taran dare a gidan su Farooq, Khaleal da Farooq neh zaune a parlour'n su suna kallon Empire, sallama sukaji take duk suka juya da mamaki jin muryan Haydar, sosai sukayi mamaki duk suka bud'e baki suna kallon sa, shiga yayi ya zauna akan kujera yaga basu da alaman amsa masa sallama sai wani kallon da suke bin sa dashi, wayar sa neh ya fara ringing ganin Jamila yayi picking wayar, can wajen ta tace "Haydar naga alert thanks", "Uhum" kawai yace da ita ya katse wayan. Tasowa yayi daga zaunen da yake ya bud'e d'akin sa ya shiga ya rufe ba tareda sunyi magana da Khaleal koh Farooq ba. Yana shiga duk sukayi ajiyan zuciya suka cigaba da kallon su ba tareda sun ce wani abu ba.....
   Haydar kwanciya yayi akan gado ya rufe idanuwan sa, duk da Jamila tana gamsar da shi amma yau baiji ya gamsu irin yadda ya gamsu da yarinyan k'auyen nan ba. Da alk'awarin sai ya neme ta duk inda take a k'auyen ya fad'a mata kudirin sa akan ta.. Da tsantsan tunanin ta ya kwanta bacciiii. ....

    _Washegari_

Yau ya kama ranar suna jama'a 'yan uwa da abokan arziki sun cika makil sai kaiwa da kawowa ake a gidan Alhaji Muhammadu Iliyasu Lamid'o, yarinya taci suna Khadeejah takwaran kakar su wato mahaifiyar Mummy. Farooq neh ya d'auka yarinyan ya zuba mata idanuwa yana kallon ta, sai can yayi murmushi yace "Mummy amma kin san me?"
Mummy wanda tasha swiss less mai tsadan gaske tun daga earring,necklace da bracelet duk na gold neh tayi murmushi tace
  "A'a Farooq"
D'aga yarinyan ya koma yi kusa da fuskan ci yana mai shafan fuskan ta yana kare mata kallo yace
"Mummy little angel tana bala'in kama da Khadeey nah, gashi takwaran su d'aya"
Murmushi Mummy tayi tace
"Anya kuwa Farooq?"
"Sosai fa Mummy, sai dai Khadeey nah tafi wannan kyau"
Dariya Ammi tayi wanda take zaune a gefe tana jin su tace
  "Kai dai Farooq da k'anwar ka Khadeejah, Allah kawo ranar da zamu ganta"
Sallaman Haydar neh yasa duk suka d'ago kai suna kallon sa da mamaki, Mummy bud'e baki tayi tace
  "Haydar? Koh dai Khaleal neh?"
Ammi shuru tayi tana kallon ikon Allah, har k'asa ya durk'usa ya gaishe su, Ammi salati tayi tace
  "Haydar yaushe ka dawo ban sani ba koh nace banda labari?"
Mummy tace "Haydar lafiya kake koh dai?"
  Murmushi yayi yace "Lafiya kalau wallahi kawai inaso ayi sunan nan neh dani"
Duk bud'e baki sukayi suna kallon sa, Mummy tace
  "Yaushe ka shigo gari?"
Yana mai sosa suman kansa yace
  "Jiya da daddare Mummy... Around nine haka"
  Ammi tace "Haydar kaji tsoron Allah ka fad'a gaskian abunda ya kawo ka" ta kafe sa da ido dan tasan halin d'an ta tasha ganin sa da Siyama a d'aki ta kirasa ta masa nasiha amma inaa, kansa a k'asa yace
  "Ammi ki yarda dani"
Mummy tayi dariya tace
  "Ki bar sa mana inaga har ya gaji da garin can, why not kana bawa principal na makarantan kud'i idan yaso sai after every month kaje kana signing, tunda ma wata uku kawai zakayi ka nema rediployment"
"Na gwada hakan baiyu ba amma In Shaa Allah zan k'ara masa magana"
  Mummy tace "Da zaifi kam"
Karb'an Khadeejah yayi a hannun Farooq, kallon ta yake yana yaba irin kyawun halittan ta, yace
"Mummy Khadeejah sunan ta koh?"
Murmushi tayi tace "Khadeejah!"
"Mashaa Allah Mummy, a gida kuma mai za mu kirata?"
Ammi tace "Kul! Kar ku kuskura ku canza mata suna"
D'an dariya Haydar yayi yace "Zamu na kiran ta da suna SAMHA, sabida kyakkyawa ce"
  Murmushi Mummy tayi tace "Duk yadda ka yanke dai-dai neh Haydar"
Murmushi shima yayi yace "Mummy ku kula min da ita sosai, sabida matata ce"
Ammi hararan sa tayi tace "Allah sauwak'a na baka 'yata"
Dariya Mummy tayi tace "Idan banda kai Haydar ai kan ta girma kana da 'ya'ya manya-manya"
D'an zare manyan idanuwan sa yayi yace
  "Haba dai Mummy! I am just twenty three, kuma sai na kai fourty zanyi aure" (Bud'e baki nayi da yace shekarun sa ashirin da uku dan ban tab'a tsammanin yaro baneh sosai haka).
Khaleal neh yashigo d'akin yace
"Get out! Waye zai baka little angel namu?"
Dariya Mummy tayi tace "Kudai sai Allah"
"Oya yanzu yanzun nan ku fita ku bar d'akin nan duk kun hana wasu shigowa kun cika mana d'aki gaku kartawa"
Farooq neh ya taso daga kan gadon da yake zaune yace
  "Toh tunda kin kore mu Ammi"
  Nan take Haydar shima ya taso yace
  "Sai anjima ku" Ya kwantar da baby'n akan gadon ta.
Mummy tace "Haydar ka huta da gajiya, ka samu waje shuru ka kwanta kata bacci"
"In Shaa Allah Mummy" yabi bayan Farooq.. Khaleal kuma zama yayi akan gado ya d'au Samha Ammi sai masifa take ya fita a d'akin amma yayi banza kamar ba dashi ake ba, Mummy kuma sai dariya......
  Suna fita Farooq ya mik'awa Haydar hannu yace
  "Ya akayi broh ka dawo gida da wuri haka"
Shima Haydar mik'a masa hannu yayi yace
  "Broh ka bari fa, kai ma kasan bana iya kwana uku ba tareda nayi abun ba"
  Wani kallo Farooq ya watsa masa ya girgiza kansa yace "Allah shirye ka"
  "Ameen Ameen wallahi"
Farooq bud'e motan sa yayi ya shiga, shima Haydar ya bud'e ya shiga motan, kallon sa Farooq yayi yace
  "Wani abun neh?"
Girgiza kansa Haydar yayi yace "Why did you asked?"
"Naga ka shiga min mota ka zauna, kasan inda zanje?"
D'an guntun tsaki Haydar yaja yace "Koh lahira neh muje"
Kallon sa Farooq yayi yace "You will never gonna change" Ya fisga motan suka bar haraban gidan..........

 

    Toh masu karatu har yanzu bamu zo asalin labarin ba, Kamar yadda sunan novel d'in yake *"Nida tagwayen maza"*..... Shin meye kuke ganin zai faru a gaba??????

  Be patient karku gaji da bibiyata!!!!!!

Vote!!!!!

NIDA TAGWAYEN MAZA जहाँ कहानियाँ रहती हैं। अभी खोजें