CHAPTER THREE

504 41 1
                                    


    Washegari da safe kamar k'arfe goma duk suna cin abinci a dinning, wayar Farooq neh ya fara ringing wanda yake kusa da Mummy, mik'a masa wayar tayi, kamar bazai karb'a ba tace "Yesmin ce fa", da sauri ya karb'a wayan ganin SWT SIS b'aro-b'aro akan screen na wayarsa yasa yayi rejecting call d'in nan take ya kirata ya danna a loudspeaker ya ajiye akan dinning  yacigaba da cin abincin sa, ringing d'aya biyu tayi picking call d'in tace
"Hello Yaya nah"
Gyaran murya yayi yace "Assalamu Alaykum", shuru tayi na d'an wasu seconds dan tasan tayi laifi a koh yaushe yana ce mata ta daina amsa waya da Hello sai da sallama, sai can tace
"Wa'alaykum Salaam Yaya nah"
"Kin tashi lafiya?"
D'an guntun tsaki taja tace
"Yaya nah zan fita school kuma gashi Lawal driver baya gidan kuma kasan ni ban iya driving ba gashi inada test eleven o'clock"
  A tsawace Khaleal dake facing nasa yace
"Toh uban meye kike so ya miki eh?"
Take ta katse wayan, wani kallo Farooq ya masa Khaleal kuma ya d'an ja guntun tsaki yace
"Yarinya duk kun bi kun shagwab'a ta sam bata da manners idan driver baya nan meye sa baza ta hau napep ba?"
Haydar dake gefen sa ya yamutse fuska yace
"Easy Man, ka cika min kunne da ihun ka yanzu sai ya saka ni ciwon kai ai mtsw" Ya cigaba da cin abincin sa kamar bashi yayi maganar ba..
Farooq tasowa yayi ya d'au car key'n shi wanda yake saman dinning d'in ya juya yana kallon Mummy yace
"Mummy lemme drop Yesmin a School"
"Ohk toh ba matsala sai ka dawo"
  Fita yayi baice wa tagwayen mazan ci kan ku ba, Mummy kuma murmushi tayi dan idan tana tare dasu tana ganin hali iri-iri....

    Cikin minti goma sha biyar sai gashi a gidan su Ammi, zaune ya tarar da ita a parlour tana dama fura. Har k'asa ya durk'usa ya gaishe ta, bayan sun gaisa yace
"Ammi fura da nono da sassafen nan"
Murmushi tayi tace "Kai ma dai tambaya kake kasan ni da son fura da nono kamar me, koh k'arfe biyun dare idan na tashi zan ita shan fura da nona"
"Hmm lalle kina k'okarin Ammi"
Bayan sun gama gaisawa ta tambaye sa su Mummy da jiki yace mata duk suna nan kalau, shuru kusan minti biyar baiga Yesmin ba yace
"Ammi ni Yesmin ta tafi School d'in neh?"
Kan ta bashi amsa sai ga Yesmin d'in ta fito, Yarinya ce budurwa wanda ak'alla bazata haura shekaru goma sha takwas ba, wankan tarwad'a ce irin mai kyau d'in nan kamar na black Americans, kyakkyawa ba laifi amma duk da tana mace yayun ta tagwayen maza sun fita kyau, sanye take cikin atampa d'inkin doguwar riga wanda ya amsa jikin ta,   Murmushi tayi tace
"Lahhh Yaya ai wallahi ban san ka isoba"
"Ba komai idan kin shirya muje koh kar kiyi late"
"A shirye nake muje"
Ammi bud'e baki tayi tace
"Yanzu Yesmin dan baki da kunya shine kika kirasa ya kaiki school bayan na baki kud'i ki hau taxi"
  Turo bakin ta tayi tace "Toh Ammi meye laifi dan Yaya nah zai kaini makaranta"
Ammi ta d'aga kanta tace "Umm lalle ba laifi, kai neh ma Farooq da baka da aiki"
Dariya Farooq yayi yace "Haba Ammi ai anything for our only sis"
"Toh Allah kiyaye hanya"
"Ameen Ammi" duk suka had'a baki...

   Bayan sun shiga motar sa ya kama hanyan BUK, Yesmin tace
"Yaya shikenan dan na kiraka sai ka saka a loudspeaker kowa yaji, da yanzu wani sirri nake so na fad'a maka ai sai kasa naji kunya"
Murmushi yayi yace "Ohhh daman akwai wani sirrin da zaki iya fad'a min baza ki iya fad'a wa Khaleal koh Haydar ba?"
  "Sosai ma kuwa"
"A'a ni dasu duk d'aya neh duk abunda zaki iya fad'a min toh suma zaki iya fad'a musu, ki bar ganin they are too harsh on you but suna miki irin son da nake miki"
  K'arya wuya tayi tace " Eyyah nasani fa Yaya"
"Yawwa toh 'yar k'anwata"
  Murmushi tayi tace "Yaya Farooq nafi son Mummy ta haifa na miji"
Murmushi yayi yace "Why Sis?"
"Sabida idan ta haifa mace zanji kishi"
Take ya juya ya kalle ta yace
"Kishi kuma? Keda k'anwar ki?"
"Toh Yaya Farooq ai idan mace ce zaka daina ji dani, ka samu sabuwa zaka manta ni". Ta fad'a haka idon ta cike da hawaye, sosai yayi dariya dan shi har ya manta last time da yayi dariya haka yace
  "Don't worry Sweet Sis koh da mace ce kece 'yar gaban goshi na kinji?"
"But still nafi son namiji"
"Kedai Allah kawo mai albarka mace koh namiji"
"Ameen" ta amsa a sanyaye..
"Zan rok'a Abba ranar auren ki na zama alwalin ki, kuma fa idan kika samo miji kan ki nuna wa kowa ki nuna min sai naga ya min zan bada go ahead"
Wani irin bak'in ciki taji ya ziyarce zuciyar ta, shuru tayi bata k'ara cewa uffan ba har yayi dropping nata a school, da zata sauk'a ya mik'a mata dubu biyar yace
"Kici abinci anjima zan sa Lawali yazo ya kaiki gida"
Karb'a tayi tace "Nagode" ta fita ta rufe k'ofan shi kuma take yaja motar ya fice. Wasu zafafan hawaye neh suke sauk'a akan kuncin ta, take ta goge su ta manna bak'in glass a fuskan ta........

  Bayan ya koma gida yaga gidan shuru, babu Mummy, tagwayen maza da mai aikin su Marka. Fita yayi bakin gate ya samu Tukur mai gadin su yace
"Nikam Tukur ya gidan shuru ba kowa sun fita neh gaba d'aya"
"A'a wallahi Hajiya ce nak'uda yazo mata shineh duk suka fita"
Nan take yaji hankalin sa ya tashi yace
"Wani hospital suka kaita?"
  "Kashh wallahi ban sani ba"
Cire wayar sa yayi a aljihu yayi dialing number'n Haydar, ringing d'aya yayi receiving yace
"Farooq muna Amina Kano Teaching Hospital mun kai Mummy but karka damu she is fine"
"Ohk" Ya katse wayan zuciyan sa na mai bugawa.
Nan take yaja motar sai asibiti, yana zuwa ya tarar da Ammi da tagwayen maza, duk suna nan a tsatsaye, hankalin sa tashe yace
  "Ammi ya Mummy nah?"
Murmushi tayi ta rik'e hannun sa gam tace "The doctors assured us that she will gonna be alright In Shaa Allah just calm down and pray for her"
Wani ajiyan zuciya ya sauk'e, Haydar neh yazo ya kama kafad'ar sa yana shafa bayan sa yana cewa "Chill Man"
Da k'yar ya samu ya nutsu yana mai addu'a Allah sauke Mummy'n shi lafiya. Sai can kusan bayan minti talatin wani doctor ya fito yace
  "Kunce Alhaji baya gari koh? Toh ina yaron sa yayi signing wannan form d'in dan already k'arfin ta ya k'are sai dai a mata C.S"
  Hankalin su ba k'aramin tashiwa yayi ba, ganin haka doctor'n yayi murmushi yace
"Calm down In Shaa Allah ba abunda zai same ta"
  Da k'yar Ammi ta lallashe Farooq yayi signing form d'in doctor'n ya bayar dashi...
  Kowa dai sai addu'a suke karanto wa duk wanda yazo bakin su, sai kusan bayan awa biyu doctor'n ya fito ya mik'a wa Farooq hannu murmushi kwance akan fuskan sa yace
"Congratulations ta samu bouncing baby gurl". Duk take suka rungume doctor'n suna mai jin wani irin farin ciki yana ratsa jikin su, Ammi tace
  "Toh ya Mummy'n?
"Kar ku damu yanzu an gama mata aiki tana bacci ma"
"Zamu iya shiga duba su?"
"Sure yanzu zaku iya shiga but please kar kuyi surutu ku tada ita a bacci"
"In Shaa Allah" cewar Khaleal
Kowa dai so yake ya riga d'aya fara shiga d'akin sai ture ture suke a k'ofa, Ammi tace
"Haba kuyi hak'uri mana ku shiga d'aya bayan d'aya koh ce muku akayi yarinyan zata b'ace". Haka dai duk suka samu suka shiga, yarinya ce kyakkyawa fara sol da ita kwance akan gadon yara har an mata wanka an saka mata kaya, Farooq zai kai hannun sa ya d'auka take Khaleal ya riga sa d'aukan ta. Khaleal bud'e baki yayi yace
"Wow Mashaa Allah tubarakallah"
Hakan nan duk suka zagaya Khaleal suna kallon baby'n, Haydar yace
"Bani ita please". Farooq ma yace
"A'a ni dai mik'o min ita", Khaleal wani kallo ya wurga musu yace
"Toh yaushe na d'auke ta da zan mik'a muku ita yarinyan da koh seconds biyar bata yi a hannu na ba"
Ammi dake gefen su tace "Kunga mik'a min yarinyan nan kuda koh iya rik'e jariri baku iya ba", Khaleal tsayawa yayi yana kallon ta bashida niyan mik'a mata ita, wani kallo ta watsa mishi tace
"Nace ka mik'o min ita ba", bawai dan yaso ba ya mik'a mata baby'n ya yamutse fuska shi a dole yayi fushi.
Ammi ta juya wajen Farooq tace kaje da Haydar da Marka ku kwaso da duk kayan da za'ayi amfani dashi, Khaleal kai kuma ka kira 'yan uwa da abokan arziki ka sanar dasu".
  Duk kallon ta suke basu da alaman amsa mata balle suyi abunda ta saka su, hakan nan duk saka nema waje suka zauna suna kumbure-kumburen fuska, Ammi tace
"Ikon Allah yanzu kenan baza kuyi abunda na saka ku ba har sai kun rik'e baby'n koh? Toh kuzoku ku amshe ta kowa second talatin"
Da sauri dukkan su suka taso, Haydar yace
"Wallahi Ammi banda Khaleal"
Ammi tace "Kowa dai 30  seconds"
  Farooq neh ya fara amsar ta, wani irin farin ciki yaji mara misaltuwa, kusan minti d'aya a hannun sa, Ammi tace
"Mik'awa Haydar", kamar kar ya mik'a haka dan dole ya mik'a masa, Haydar har cikin jinin sa yake jin baby'n a ransa, sosai yake jin sonta, haka nan ya mik'a wa Khaleal daga nan Ammi ta karb'a jaririyan tace
"Yanzu maza kowa yaje yayi aikin dana saka sa"
Ba dan sun so ba suka fita a d'akin..........

    Nana Fa'ad

Vote pls

NIDA TAGWAYEN MAZA Where stories live. Discover now