CHAPTER SEVENTEEN

573 50 12
                                    

Hiii Readers: Please don't forget to vote, share to your love one's (Watsapp, Facebook, Twitter, IG, etc). I'll be so grateful if you do so, and I want you to know that I love you all. And thanks for being patient with me, thanks for enduring my typing errors and grammers. Thanks most to all those that votes! Don't be a silent reader, tell me your opinions!!! Your opinions might change the story!!! Atleast if you can't vote or comment, SHARE!!!!!!

THIS PAGE IS DEVOTED TO MY GHANIAN FRIEND @Reine

♤♤♤♤♤♤♤♤♤♤♤♤♤♤♤♤

Suna landing a Abuja bayan sun d'au bag nasu Haydar ya d'an yamutse fuska yace
"I really don't like the idea na mu kwana a gidan Uncle Tukur". Farooq shima yamutse fuska yayi tareda jan d'an guntun tsaki yace
"Neither do i, but babu yadda muka iya haka Ammi da Mummy suka ce"
Haydar d'an sosa suman kansa yayi yace
"The house is boring"
D'an dariya Farooq yayi yace "Not the house but the people living in the house are damn boring"
Haydar ya d'anyi dariya ta gefe yace
"Broh ina wancan yarinyan da muryan ta kaman engine markad'e sai uban yanga idan tana tafiya kamar wanda stool ya mak'ale mata a pant.. Ehn what's that even her name?"
Farooq bai san lokacin da ya fashe da dariya ba yace
"Ohhh boi you wicked, yarinyan she is ok fa ba laifi.. Nima gaskia can't recall her name"

Suna hira har suka tare taxi ya kaisu gidan wan Baban Farooq Alhaji Tukur Iliyasu Lamid'o wanda ke cikin wuse 2.
Sosai matar sa Hajiya Nana Fiddausi ta tarb'e su da fara'ar ta, Matace bak'a ba laifi tana da kyau daidai na rufin asiri, murmushi tayi tace
"Ai da kun kira sai mu aika driver yazo ya d'auke ku"
Take duk suka sosa suman kansu kamar wani had'in baki, Farooq ya d'anyi murmushi wanda bai kai piece of an atom ba yace
"Ba komai fa Hajju"
Kiran wani ma'aikacin gidan tayi tace ya kaisu masaukin su, tace
"Idan kunje kunyi freshen up sai kuzo kuci abinci"
Godiya suka mata suka bi bayan mai aikin, d'aki neh babba da toilet mai kyau a ciki, mai aikin yana fita a d'akin Haydar ya d'au bag nasa ya cire wani bedsheet wanda ya d'auko tun daga kano, Farooq kallon sa yake baki bud'e yace
"What are you trying to do?"
D'an b'ata rai Haydar yayi yace "Wanna change the bedsheet, can't you see? Are you fucking blind?"
Ni Nana kallon bedsheet na kan gadon nayi, kallo d'aya zaka yiwa bedsheet d'in ka tabbatar sabuwa ce fil amma a hakan Haydar keson ya canza. Farooq girgiza kansa yayi ya fad'a toilet, Haydar kuma da yatsa d'aya yake zame bedsheet d'in daga kan gadon yana wani yamutse fuska kamar wanda yaga kashi akai.
Wani yaro neh k'arami wanda bazai haura shekaru shida ba ya bangaje k'ofan yashigo da gudu yana ihu, can kuma sai ga wata yarinya wanda baza ta haura goma sha takwas, bak'a ce tanada idanuwa daidai wanda they ain't too big nor small, sai hancin ta dogo da bakin ta d'an ma daidai ci wanda ya dace da fuskan ta, wani irin b'oyayyen kyau take dashi wanda sai ka k'are mata kallo zaka san tanada tsantsan kyau, ta biyo shi da gudu cikin d'akin wanda ita bata san akwai mutaneh a ciki ba...
Tana ganin Haydar take ta tsaya cak, ji tayi duniyan ya tsaya mata cak, ita a rayuwar ta bata ganeh Haydar da Khaleal, sai dai tasan d'ayan su yana da d'an sassauci duk da dukkannin su akwai ra'ayi da miskilanci. D'an ja da baya tayi tace
"Yaya 'yan biyu sannu da zuwa! Ina yini" cikin muryan ta wanda yake da d'an fad'i kamar wanda take d'an fama da cough (tari).
Shi kuwa yana ganin an bangaje k'ofan d'akin ya tsaya kallon ikon Allah, sosai suka bashi haushi amma ba yadda ya iya tunda gidan uban su neh, kawar da kansa yayi yace
"Lafiya". Ya cigaba da zame bedsheet na kan gadon da yatsa d'aya yana mai yamutse fuskan shi da nuna tsantsan kyama akan bedsheet d'in, Yarinyan kallon sa ta tsaya yi ganin yadda yake cire bedsheet d'in zuciyan ta ba k'aramin sosa yake mata ba ganin bedsheet sabuwa haka fil amma ake masa wannan wulakancin, a zuciyan ta tace "Wannan tabbas Haydar neh, da Khaleal neh da d'an sassauci dan Haydar yafi Khaleal rashin mutunci, wani zuciyan yana ce mata wannan Khaleal neh dan da Haydar neh sai ya sauke mata rashin mutunci irin yadda ta bangaje d'akin babu sallama". K'anin ta da suka shigo tare take ya rungume Haydar yace
"Yaya twins yaushe kazo? Kai kad'ai neh kazo koh kaida d'ayan twins da Yaya Farooq? "
A nan neh yarinyan tace yanzu zata tabbatar wa kanta wanene wannan, dan Haydar yana son yara duk rashin mutuncin sa Khaleal kuma shi baya kula yara asalima baya son disturbance na yara. Haydar rungume yaron yayi yace
"Faisal nida Yaya Farooq neh"
Anan ta tabbatar wa kanta wannan Haydar neh, dan da Khaleal neh bata tsaman zai basa amsa dan baison surutun yara.. Tace
"Faisal zo ka bani waya ta"
A lokacin neh Farooq ya fito a toilet, take Faisal yaje ya rungume sa yace
"Yaya Farooq ina tsaraba na?"
D'an murmushi Farooq yayi wanda bai kai har cikin zuci ba yace
"Yana airport gobe zan kawo maka"
Dariya Faisal yayi yace
"Banda Anty Maryam koh?"
A lokacin Farooq ya d'aga kansa ya kalle yarinyan wanda k'anin ta Faisal ya kirata da Maryam
"Ummm" kawai Farooq yace dashi...
Maryam d'an sunkuyar da kanta k'asa tayi dan dukkan su ba wanda ya mata kallon kirki harda Farooq wanda yake zaman d'an uwan ta tace
"Yaya Farooq sannu da zuwa"
Wanda shi lokacin yana cire laptop nasa a jakan sa yace
"Uhum Yawwa"
Juyawa tayi tana tafiyan ta a hankali ranta babu dad'i....

Haydar bayan ya gama cire bedsheet d'in ya mik'awa Faisal yace
"My boy kaje kasa a washing machine dan yayi datti sai ka dawo kaji?"
Take Faisal ya amsa bedsheet d'in ya fita da gudu, Haydar kuma yana shimfid'a bedsheet nasa ya kwanta akan gado tareda lumshe idanuwan sa yana mai tunanin yarinyan Bakassi LG wanda ke cikin Cross River....

Vote! !!!!!!!

Comment!!!!!

Share!!!!!

NIDA TAGWAYEN MAZA Where stories live. Discover now