CHAPTER SIXTEEN

379 41 0
                                    

Calabar

    A b'angaren Lola kuma washegarin da Haydar yayi tafiya ta fara zuwa makaranta koh Allah zai sa ta ganshi, sati d'aya shur tayi kullum sai taje makaranta amma ina bata kallon sa, har bin ta k'ofan gidan sa take amma shuru ba alaman sa, sosai ta shiga cikin damuwa, dan zuciyan ta yana matuk'ar so ya k'ara ganin sa, ita har ta manta da abunda ya mata yanzu sam bai damun ta kamar da, a zuciyan ta cewa take " I ain't gonna die a virgin afterall, wani irin bak'on lamari takeji a tattare dashi wanda bata san menene ba, ita dai rok'an Allah take su k'ara had'uwa.

      Zaune take ita da Abigail a d'aki suna karatun Jamb dan ya gabato, knocking na k'ofar d'akin su akayi, Lola wanda ta zuba ido tana kallon textbook na gaban ta amma hankalin ta sam baya kan text book d'in tayi nesa a tunanin Aliyu, d'aga manyan idanuwan ta tayi ta kalla k'ofan ta d'an ja guntun tsaki tace
"Yes come in!"
Mami ce ta shigo d'akin tana murmushi, Abigail ta d'an durk'usa tace
"Good evening Mami"
Shafa suman kanta tayi tace
"Evening my daughter! How are you?"
"Fine Mami"
"So you gurls are preparing for Jamb? I wish you all the very best of luck"
"Thank you Mami"
Kallon Lola tayi tace "Emm Lola, Aunty Mary wanted you to go and meet her in Abuja from there you both will go to Lagos. She said is urgent you must have to leave tomorrow"
Zare idanuwan ta tayi tace
"Mami!!!! Hope all is well? I really don't wanna go anywhere". Bayan kwanaki da suka wuce ita take damun Mami akan sam tana son zuwa Abuja, Mami tsantsan mamaki tayi da Lola tace bata so taje. Mami tace
  "But why?"
"I ain't ready". Lola ita duk tunanin ta karta tafi Aliyu shi kuma yazo, bayan addu'a take akan Allah k'ara had'a ta dashi ta fad'a masa abunda ke yawo a cikin zuciyan ta, brain nata da kuma jinin jikin ta.
Mami tace "Ready? Azin how?"
D'aga textbook na gaban ta tayi tace
"Mami I need to read cox exam is approaching and you know time is running faster than we could think"
"You have almost three months before to write the exam"
  "Mami I know! But I ain't going period!"
Mami b'ata rai tayi tace "Lola you must leave tomorrow"
  "Must?" Tana mai kallon Mami da mamaki dan Mami bata tab'a tilasta mata akan lalle sai tayi tafiya ba. Mami d'an kallon Abigail tayi wanda take karatu amma tasan hankalin ta yana kan zancen su tace
"Maganan kud'in gadon Dad naki"
( Ni Nana zare idanuwa nah nayi dan ban tab'a kawo a kaina suna jin wani abu a cikin yaren hausa ba balle har suyi making sentence mai kyau da yaren hausa)
Cusa hannun ta tayi cikin suman kanta tace
"Mtsw ohh, ohk"
"You better get ready" Mami ta fad'a ta fita a d'akin. Lola wani irin bak'in ciki taji ya mamaye ta, tun da tana son zuwa aka hana ta yanzu kuma da bata son zuwa wai taje. Abigail ce ta matso kusa da ita tace
"Lola I thought you'll be happy about this?"
Dogon tsaki taja tace "I am and I am not?"
Abigail ta bud'e baki tace "Azin how?"
Jan textbook na physics tayi tace
  "Just forget it". Abigail tana son k'ara wani magana tace
"Shhhh please, just read"
Ja da baya Abigail tayi tace "Ohhkk ohhhh"

   Washegari Lola ta had'a bags nata sai hanyan tasha, daga nan kuma tashiga motan da zai kaita Abuja.........


    Kano

Farooq, Khaleal da Haydar suna zaune a k'asan carpet, Ammi kuma da Mummy akan kujera. Mummy tace
"Yanzu kaje kasan yadda zakayi da principal na makarantan, koh nawa neh ka biya sa"
Kan Haydar na k'asa yace
"In Shaa Allah Mummy"
Ammi tace Farooq kai kuma daga Abuja zaka wuce lagos koh?"
"Eh In Shaa Allah Ammi"
"Toh Allah kiyaye hanya"
Duk suka amsa da Ameen Ameen. Haydar d'aukan jakan sa yayi, Yesmin ta taso da saurin ta zata d'aga jakan Farooq amma sai ta kasa, wani irin kallo Khaleal ya watsa mata yace "Idan banda rigima irin naki ina ke ina d'aukan wannan bag d'in, maza ki sauke" Tura bakin ta tayi tana k'ananan maganganu, Haydar ya d'an ja guntun tsaki yace
"Zan buga dogon bakin kin nan idan an miki magana sai ki wani turo shi koh kyau ma baya miki" Ya juya yana mai kallon Farooq yace
"Kaga ni please don't waste my time ka d'au bag naka mu wuce"
Farooq basar dashi yayi kamar wanda ba dashi yake ba, ganin haka Haydar ya d'an ja guntun tsaki ya fita Khaleal ma yabi bayan sa. Mummy da Ammi suka tashi duk suka shige ciki jin kukan Samha...
  Yesmin wanda ranta duk ya b'aci har hawaye sun cika a idon ta taja da baya ta zauna akan cushion, Farooq durk'usawa yayi a gaban ta yana mai murmushi wanda ya bayyanar da fararen hak'oran sa da dimples nasa suka lutsa ya k'ara fidda asalin kyawun shi,  shafa fuskan Yesmin yayi yace
  "Smile Swt sis, it's a sunnah"
Ji tayi har b'acin ran da tagwayen maza suka cusa mata take ya tafi, murmushin sa ya wanke mata duk wani b'acin rai da take ciki, murmushi ta maida masa tace
"I am gonna miss you Swt broh!"
Shima murmushin yayi yace
"I'll miss you more more". Sauk'ar da idanuwan ta tayi dan bara iya jure kallon sa sabida yayi mata kwarjini. Tasowa yayi yace
"Bye do take care"
Murmushi tayi tace "Allah kiyaye hanya"
"Ameen Swt Sis " Ya fita. A lokacin su tagwayen maza suna cikin mota suna jiran sa. Yana shiga motar yana rufe k'ofa Khaleal ya tada motan sai hanyan airport. Wallet nasa Farooq ya cire a aljihun sa, ta bayan ya bud'e ya kurawa hoton yarinyan da kullum sai ya ganta wato Khadeejah 'yar uwarsa.... Suna isa airport da minti goma sha biyar jirgin su ya d'aga zuwa Abuja, Khaleal kuma ya juya ya koma gida.....

    Abuja......


Don't forget to vote!

Share to your watsapp group, friends and family. 

Shi zai bani k'arfin gwiwa...

Luv y'll

I am not perfect you might come across many many many typing errors or wrong grammers. ..

That's because I am too busy I can't cross check sai dai after nagama book d'in will edit In Shaa Allah.....

Thanks

Vote

Vote

Vote

NIDA TAGWAYEN MAZA Where stories live. Discover now