CHAPTER FOUR

491 44 4
                                    

      Cikin awa d'aya asibitin ya cika fal da jama'a, y'an uwa da abokan arziki duk sun zo.   Yesmin ce ta d'auki jaririyan tace
"Wow Mashaa Allah tubarakallah tana kama da Yaya Farooq kamar an tsaga kara "
Murmushi Farooq yayi yace "Allah koh Swt sis?"
"Sosai kuwa", sai kawai ga hawaye shar shar yana zuba a kuncin ta, Mummy da take kwance tace
"Sub'hanaAllah Yesmin ya da kuka fa?"
Turo bakin ta tayi tace "Mummy kar Yaya Farooq ya daina ji dani kamar before"
Ammi da Mummy dariya suka yi, Haydar ya girgiza kansa Khaleal kuma yaja guntun tsaki, Farooq murmushi yayi yace
"Don't worry Dear har kullum kece 'yar gaban goshi na kinji?"
D'aga kai tayi tana mai turo bakin ta, Ammi tace
"Ke kam sai gyaran Allah, da k'anwar ki ma kina kishi? Allah shirya ki da shiriritan ki"
  Mummy tayi dariya tace "Yesmin wannan azababben kishin naki Allah sa dai ki rage dan idan kinyi aure mijin ki yace zai miki kishiya ai sai ahankali"
Rufe fuskan ta tayi da gyalen ta ita a dole taji kunya, tagwayen maza kuma duk wani haushin ta suke ji ganin yadda ake b'ata yarinyan, ace warsu yarinya k'arama ana mata maganan miji, Farooq kuma wanda bai ma san suna yi ba sai danne-danne yake da laptop nasa.....
Mummy da take kwance tace
"Nikam Haydar tafiyan ka gobe koh?"
Sosa suman kansa yayi yace
  "Mummy ai yanxu kam tafiya sai bayan suna"
Mummy bud'e baki tayi tace
"Haba dai sai kace mace, dan Allah ka shirya kayan ka tafi, abu wata uku zaka yi ka dawo, a kwana a tashi ai ba wuya"
Ammi tace "Nima dai shineh nagani, d'azu na masa magana yace shi sai bayan suna"
Mummy tace "A'a baza ayi haka ba, gobe kawai ka wuce, abu ka riga kayi booking flight koh bakayi baneh?"
Kansa a k'asa yace "Eh nayi booking, daga Abuja sai ya d'aga zuwa calabar dan babu direct"
"Ohk toh Allah kaimu"
"Ameen"

   Ammi da Mummy suka cigaba da hiran su, Khaleal kuma wani k'aton text book neh a hannun sa yana karantawa, Haydar neh ya matso kusa da Farooq wanda hankalin sa yayi nesa a danne-danne da laptop nasa, Haydar yayi magana k'asa-k'asa yace
"Aboki nah akwai matsala fa, kasan koh complete kwana uku bana iyayi ba tare da na kusance mace ba kuma gashi har wata uku zanyi a can garin arna, sanin kanka neh bana had'a jiki nah da arnaye"
Farooq d'aga manyan idanuwan sa yayi ya sauk'e akan sa, girgiza kansa yayi yacigaba da danne-dannen sa, Haydar d'an guntun tsaki yaja ya taso ya durk'usa a gaban su Ammi da Mummy yace
"Umm ni zan wuce gida naje na had'a saura kayaki nah"
"Ohh toh shikenan mungode sai da safe" cewar Mummy
Ammi tace "Bari ku tafi da Yesmin mana"
B'ata rai yayi yace
  "Ammi nifa ba gida zan wuce direct ba"
Tasan halin sa sarai tunda baya so su tafi tare bazai ma yarda baneh, juyawa tayi wajen Khaleal wanda hankalin sa gaba d'aya ya tattara su akan text book na Physiotherapy a hannun sa tace
"Khaleal idan ka tashi tafiya sai kuje da Yesmin ka ajiye ta a gida"
D'aga kansa yayi yace "Ammi daga nan fa ba gida zan wuce ba"
Bud'e baki tayi duk tana kallon su, zatayi magana kenan sai Farooq yace
"Mummy karki damu idan na tashi zanyi dropping nata a gida"
"Allah maka albarka Farooq"
"Ni daman nafison Yaya Farooq ya kaini" Yesmin ta fad'a tana mai murmushi tana kallon Farooq, Ammi tace
"Tam yayi kyau"
Haydar ya taso yace
"Toh sai da safe"
Duk suka amsa masa banda Farooq da Khaleal dan bai saka ma a ransa zasu amsa masa ba dan duk halin su d'aya....

    Motan sa Ferari bak'a ya d'auka wanda yayi parking a parking space na asibitin, wayar sa ya cire a aljihu yayi dialing number'n Siyama, ringing d'aya ta d'au wayar, yana ganin tayi receiving yace
"Kizo ki same ni a d'aki nah yanzun nan gidan Ammi" ba tareda ya jira ta amsa masa ba ya katse wayan.  Gida direct ya wuce, yana zuwa ya fad'a ban d'aki yayi wanka. Fitan sa kenan sai ga wata yarinya zaune akan gado, fara ce sol amma daga ganin hasken ta na k'ari neh, ba laifi kyakkyawa ce. Tasowa tayi daga kan gadon tayi hugging nasa tace
"My lion I missed you"
D'an ture ta gefe yayi yace
"Ki shiga kiyi wanka SIYAMA"
Shan gaban sa tayi tace
  "Yanzu fa nayi wanka ka bari anjima zanyi" tana mai tsame ruwan dake sauk'a akan eight packs na cikin sa. 
  Wani kallo ya watsa mata, nan take taja da baya ta fara cire kayan jikin ta, ganin haka ya juya baya yaje gaban dressing mirror wanda aka tanada body lotion da designer perfumes kala kala, wani cream mai k'amshin gaske ya d'auko yana shafawa a jikin sa, daga nan ya d'au perfumes kusan kala shida ya fesa a jikin sa, jin an bud'e k'ofan toilet yasa ya juya yana kallon bakin k'ofan. D'aure take da towel a jikin ta ga gashin kanta jik'e ya d'an zo mata har wuya ba laifi, Haydar yana son ganin mace gashin kanta a jik'e dan yana motsa masa da sha'awa. Tafiyan sa yake kamar zaki mai d'aukan hankali har ya kai gaban ta, ruwan dake sauk'a daga suman kanta zuwa k'asa yake kallo, Siyama tsayawa tayi tana kallon Haydar irin kyau'n halintan da Allah yayi masa. Yatsan sa yasa yana murza lips nata dashi, d'ayan hannun sa kuma ya cusa a cikin sumar kanta, d'aukan ta cak yayi ya dira ta akan gado, zare towel d'in yayi ya d'au cream yana mai shafa mata a jikin ta yana murza wa,nan take gaba d'ayan su suka d'auke wuta haka har suka fad'a uwa duniya daga nan kuma aka wuce wajen (wa'iyazubillah)....

NIDA TAGWAYEN MAZA Where stories live. Discover now