RASHIN HAIHUWA

172 12 2
                                    

RASHIN HAIHUWA

GORGEOUS WRITERS FORUM
G.W.F

Home of gorgeous,intelligent and experts, writers,we are the best among the rest

Written by fateema Adamu Gamawa

BASED ON REAL LIFE

Sadaukarwa

Wannan littafi sadaukarwane ga duk wata mace mai Neman haihuwa ya ilahi Dan darajan mazanka Allah ka basu mai albarka

Page 1-5

Labarina labarine dake cike da tausayi, jimami, hade da Al ajabi

Sunana Ahlam Adamu dangaidam

mu biyu ne gurin iyayen mu daga ni sai yayata Anty Basma
Kasancewarmu mu biyu, iyayenmu suka dauki soyayyar duniya suka daura mana
Amma hakan baisa sunbarmu mun lalaceba

Mahaifina Alhaji Adamu dangaidam
babban Dan kasuwa ne Wanda ake jidashi a duk fadin kasar nan

Mahaifiyata Hajiya kubra sani gurum
Ita full housewife ce Wanda kullum tana gida tana kula da yaranta da kuma mijinta,
rayuwar mu
muke babu ruwan wani da al amarin wani, wato rayuwar turawa

Anty basma tayi aure tun shekaru biyu da suka wuce, yanxu haka tanada yara biyu afeef da afeefa

Halinmu ya banbanta da Anty basma
Kasancewata Mai hakuri, kawaici da kuma kunya
Ita kuwa masifa, neman ayi ga shegen zuciya i wa tsohon kuturu

Atakaice dai ita exactly halin Abbu ta dauko, shiyasama sukafi shiri
Nikuwa halinmu sai yayi daidai dana Ammu na, shiyasa ma tafi jidani

Inada shekara 20cif nagama university dina anan cikin kaduna , inda na karanci
Home management,
Anan fa Abbu yace min nafito da mijin aure,

banida matsala ta wannan fannin domin inada saurayina Wanda muke tareda shi tun Ina secondary school, yana matukar,sona dakuma riritani kamar yanda nima nake sanshi domin har alkawari mukai wa junan mu na aure
Soyayyar mu harta zama abin kwatance agurin mutane, domin tunda nafara makaranta kullum shi yake kaini yakuma da wo dani shiyasa kuwa yasanni da shi

Sunanshi Abdul Hameed amma nakan kirashi da My hameed

Ranar dana fada masa sakon Abbu kuwa saida yakusan goyani tsabar farinciki
Take ya tura iyayensa akai magana aka tsaida ranar biki nan da wata biyu

Nanfa ya Kara kaimi wurin nunamin so da kula, haka yan uwansa ma kullum suna cikin zarya, kamar su cinyeni tsabar so, kasancewarsa namiji daya tsakanin Mata biyar, wannan ne ma yasa duk suka dauki burin duniya suka daura akanshi
Hameeda engineer ne babba Wanda ake matukar jidashi, kyakyawa ajin farko, fari Mai dogon saje da hanji kamar na biro😝gashi very giant and gentleman,

Akwana a tashi ba wuya,gashi yar bikinmu yazo, farinciki gurina da hameed ba'a magana, saika rasa wayema yafi farinciki a tsakaninmu

Taka nas Ammu ta dauko mai gyaran jiki tundaga chad,

aikuwa na gyaru, inda kunga yanda skin dina yake shining, maganunnuwa kuwa ba'a magana, balle kuma kamshi domin ku ta wuri na gifta kamshine kawai ke tashi, Anty basma kuwa dama tun ana sauran sati uku, tadawo gida, haka zata sani a gaba tayitamin huduba, daga kan yanda ake different types na kwanciya, Kissa , rangwada, shagwaba kaini wani abunma har kunyarsa nakeji idan tanamin
Babu abunda yake bani dariya sai kaga Anty basma taje ta sako jeans da t-shirt
Tana rangwada tana juya jiki, tana wani taku kamar bazatayi ba, waifa hakan gwada min take, uhum ni Ahlam wlh ya Khalil ma yabanu😳 (mijin Aunt B)

Ba'ayi wasu event dayawa ba kawai walima akayi sai kuma bridal shower sai, budan kai da za'yi idan ankaini

Daurin auren mu yasamu halattar many a manyan mutane, kamadaga sarakuna, governors, manyan yan siyasa dakuma many a manyan attajirai,kasancewar mahaifin Hameed babban dan siyasa, Amma Allah yayi mishi rasuwa shekaru uku da suka wuce

Ankaini gidan Hameed, Ina kuka ina komai haka Aunt B ta cici beni takawoni tadamkani a hannun Ummah wato mahaifiyar Hameed,
A wannan ranar naga SO domin saina rasa ma tsakanin shi hameed din da yan uwansa wayafi kaunata

Domin kuwa zaunar dani sukai a tsakiyansu, suna ta kallona suna yaba kyau na, suna cewa Zan haifa musu babies kamar ni, Hameed kuwa babu wata kunya haka yazo yazauna kusa dani tareda riko hannuna yana murzawa a hankali .........

Hakika iyayena sunyi matukar kokari wajen yimin kayan daki domin ko yar shugaban kasa sai haka
Gidan Sama da kasane Wanda a kasan akwai dakuna uku haka ma saman sai katon parlor a kasa dawani karami a sama, kai saidai kawai Masha Allah

Haka rayuwa take ta tafiya cike da farinciki dajin dadi, sai nake ganin kamar a haka zan dauwama

Ashe ni bansani ba kaddara tana biye daani, bakin ciki, damuwa duk suna biye dani duk adalilin RASHIN HAIHUWA
***************************************

KO BIYO NI DON JIN YA ZATA KAYA

FATEEGAMAWAH😍😍😍 LOVES U GUYZ

Vote,comments and share

RASHIN  HAIHUWADonde viven las historias. Descúbrelo ahora