RASHIN HAIHUWA

15 1 0
                                    

RASHIN HAIHUWA

GORGEOUS WRITERS FORUM
    
           G W F

Home of gorgeous, intelligent and expert writers, we are the best among the rest

Page 16

Asibiti suka wuce

emergency aka wuce da ita a kofar wurin ya tsaya, yanata Kai kumo , Baba haule kuwa tana zaune akan kujera tana ta addu'a cikin ranta

A gida kuwa suna ganin hameed ya fita ummah ta fito daga wurin data rakube tafara balbala Bala'i" wlhi sai na nunawa wannan yarinya nafi karfinta kuma nice na haifi hameed ba ita"kwafa tayi sannan tafita buzum buzum su Anty luba ma haka suka rarrafa suka bita

A asibiti 

Sai bayan awa biyu likita yafito  dagudu hameed yanufeshi yana tambayarsa yaya jikin nata kallonsa yayi fuskarsa cike da damuwa yace "please follow me" binsa yayi harsuka isa office din kujera ya nuna masa yace " have a sit"zama yayi yana allah allah yasanar dashi

Shima likitan zama yayi a kujerar dake fuskantarshi sannan yafara magana
"A gaskiya Mr hameed matarka nacikin wani hali tana dab dakamuwa da ciwon zuciya don haka ayi kokarin gujewa abinda zaibata mata rai, idan wannan karan mun samu nasarar cetota tofa wani lokaci Dakar ne  "

Iya tashin hankali ya shiga domin har wani gumi ke yanko mai
Cikin muryar damuwa yace " yanzu likita miye abinyi"
"Gaskiya tana bukatar hutu kuma arage bata mata rai sosai"
"Insha Allahu zami kokarin kiyayewa"

Hannu ya mika masa  sukayi musabaha sannan ya koma dakin da aka kwantar da Ahlam kasancewar an sauya mata daki, a hankali ya tura kofar dakin kwance yasameta idonta rufe ruf, zama yayi a kujerar kusa da gadon sannan ya riko hannunta yafara shafawa a hankali,

Abinda yafaru yafara tunawa, wasu hawaye masu zafi ne suka zobu masa nan take tausayinta da tsananin kaunarta ya  kara shiga zuciyarsa, fuskarta ya kalla yaga very innocent, magana yafara yi shikadai
"Haba ummah mi Ahlam tai muku ne kuke mata haka, haba ummah haba...." Kuka yahanashi karasawa,

kukansa yacigaba da yi,

Yancikin kukan yaji hannunta yafara motsawa, da sauri yadaga kansa,

a hankali tafara bude idonta, kuma sai tai sauri tarufe saboda haske haka taitayi har sau uku tukun tasamu suka bude gaba daya,  firgigit tayi tana kokarin tashi tana cewa"Dan Allah Anty luba kuyi hakuri, ku min rai,wlh bani nahana shi yafasa ba..."hameed ne ya riketa,ya komar da ita tazauna,

"Hameed Dan Allah ka kaini gun Ammuna, karsu Anty luba susake dawowa" Kuka tafarayi, DA sauri ya rungumeta  yayi shima ya fashe da kukan,haka sukai ta kukansu babu mai bai wani hakuri, Dakar yasamu yayi shiru,sannan ya rarraasheta, Dakar yasamu tayi shiru domin kafewa tayi akan itafa saitaje gun Ammun ta, abinci  yabata taci sannan tasha ruwa, sannan ta koma bacci........

Baba haule yayiwa magana tazauna da ita zaije yadawo

Fita yayi yaje yayi musu booking en flight, Wanda zaitashi izuwa Kasar Dubai da misalin karfe 5 na yamamar gobe

Koda yadawo bata farka ba, kawai sai cewa baba haule yayi tashirya duk kayanta, takuma je ta yiwa yan uwanta sallam don gobe zasuyi tafiya......

•••••

Ummah kuwa tana nan cika ta batse kiris kawai take jira tafashe,

Anty luba kuwa ana nan ana gasa jiki domin ba karamin naushi ya musu ba,

°°°°°°°°°°°°°^°°°°°°°°°°°°°°°°°°°^

Assalamu Alaikum masoya kuyi hakuri kwana biyu banyi updating ba wlh hakan yafaru ne sakamakon ciwon wuya danake fama dashi,

Kuyi hakuri wannan ma dakar nasamu nayi wlh,kuyi managing

Lemme start dancing,munkusa tafiya Dubai(lol) wayaga idon Baba haule a Dubai

Tab amma  ana wata ga wata kuna tunanin Ummah kuws zata yarda da wannan tafiyar?????

Follow,vote and comments through wattpad @fateemaAdamu

I love you wujiga wujiga

RASHIN  HAIHUWAWhere stories live. Discover now