RASHIN HAIHUWA

78 1 0
                                    

RASHIN HAIHUWA

GORGEOUS WRITERS FORUM
          G.W.F

Home of gorgeous, intelligent and expert writers, we are the best among the rest

My mommah ....my everything
Sadaukarwa

Ga duk wata mace mai Neman haihuwa a fadin duniyar nan
Allah ka dubesu da idon rahma kabasu masu Albarka👐

Page 5-10

Bayan wata tara da aurena da hameed

nakamu da rashin lafiya, zazzabin dare nake,kuma safiya tanayi saiya sauka ga Amai kamar mi, abinci kuwa ko ganinsa bani sonyi, nanfa duk suka zata ciki ne, abin kwadayi kuwa ta ko ina aiku min akeyi, kama daga gidan mahaifiyarshi, gidan yayunsa dadai sauran gidaje

Hameed kuwa ko nan da nan baisu yaga naje, har mai aiki yasamamin, wata dattijiwar Mata maisuna haule, amma ni nakan kirata Baba haule,

Aiki ma daina zuwa yayi saboda dokin cikin,hakika nima nasha cikin ne dani,

Haka dai jinya taki ci taki cinyewa harta kwantar dani,shi kuwa hameed wai yaki muje asibiti, wai don kar ataba masa yaronsa😏
Dakyar dai ummah ta lallaba shi mukaje
Nanfa aka tabbatar muna cewa baciki gareniba ,
hameed  nafara kalla  sai naga fuskarsa tanuna alamun baiji dadi ba, nima kam banji dadi domin harna fara shirya sunan dazan saka wa Dana,

Ummah kam cewa tayi karyane ina da ciki saidai zubewa yayi, ko likitan baisan aikin shiba,saida mukaje asibiti kusan uku kafin ta yarda banida ciki

Amma ni nasan cewa lokacin haihuwar ne baiyiba,

Haka nacigaba da addu'a Allah yabamu masu albarka

Yau da gobe sai Allah

Yanzu aurenmu da hameed shekaru uku kenan kuma ko  batan wata bantabayi ba, tsakanina da hameed babu abunda ya sauya, soyayya hadi da kauna ga tsantsar kulawa domin yasha cemin shiko ban haihuwa ba bashida damuwa
(Amma inaaa deep down nasan yana matukar son yara, Kafin muyi aure yasha gayamin yanda yakeson yara , harcemin yake shibaiga anfanin family planning ba, donshi soyake yaga gidanshi cikeda yara)

Bangaren yan uwansa kuwa nafara ganin canji sosai da sosai don yanxu sainayi wata banga kuwa yazuminba
Ko naje sama sama sukemin
Amma ni bantaba nuna musu naji haushi ko wani abuba

Tun ana zaqina abayan idona har aka fari agabana, haka kawai zasuzo suyita min habaici, suna harbin iska
Nanfa nafara shiga damuwa domin abun har yafara wuce tunanina

Niko banida wata kawa  wanda zan iya gayawa damuwata,a yanxu dama kawata dayace Aafrin kuma Allah yayimata rasuwa tun muna kanana, a yanxu kowa banida wacce ta wuce mahaifiyata sai kuma Mijina

Mutum biyun nan sune nakejin bazan iya boyewa komai nawaba

Ammu nakira nasanar da ita halin da nake ciki

Hakuri tabani hadeda kara bani wasu shawarwari sannan ta kwantar min da hankalina

*************************************
PRESENT

Ina kwance kan sallayar danayi sallar asuba ina bacci kasancewar hameed baya gari suntafi yin wani aiki a illorin amma yau muke tsammanin dawowarsa

Jinayi an buga kofar dakin da karfi,har sai danayi wata irin tsorita, wlh alokacin xuciya ne kadai ban hadiya ba  saboda nayi matukar tsorata
"Subhanallahii.....innalil....wala hau......." Nafa a matukar tsorace

Ihu na saka domin idanuna sun rufe, jinayi an wanke ni da Mari, wanda hakan ne yayi sana diyyar dawuwata hayyacina daga kaina nayi sai naga Anty lubabatu tsaye a kaina(babbar yayar Hameed, sai Anty kaltum, Anty haseenah,Anty kursum,sai ya hameeda sai kuma hameed duka suna da aure dakuma yaransu)

Tsawa ta daka min Wanda ta kara tsoratani
Masifa tafara min niku banma san mitake cewa ba
Kawai dai ina ganin bakinta na motsine

Ganin banida niyyar bata amsa sai kawai tafara jana kamar wata kayan wanki, haka tayi tajana a tsakar daki, nikuwa nayi shiru ina jinta domin kwata kwata brain dina ta tsaya cak bana tuna komai, jinayi an bugamin kaina a jikin wani abu, aikuwa bankara sanin yanda nakeba.........................

A hankali na bude idanona, naganni akan gadona,ga baba haule a kusa Dani zaune

Sannu tamin sannan ta miku min robar ruwa nasha
Nan fa abinda yafaru yashiga dawomin
Innalilahi wa inna ilahair raju una
Mai ke shirin faruwa Dani mai nayiwa Anty luba haka ................

*************************************

Boring😞 right sorry love

Comments....... My dearie
Share.......sweetheart
Vote..........darling
Love...........me
@fateemaAdamu

RASHIN  HAIHUWADonde viven las historias. Descúbrelo ahora