RASHIN HAIHUWA

13 0 0
                                    

RASHIN HAIHUW

GORGEOUS WRITERS FORUM
       G.W.F

Home of gorgeous,intelligent and experts writers, we are the best among the rest

Written by fateema Adamu Gamawa

       Fateegamawah

Wai yane naga commentes yafara kasa ne

Page 23

A hankali na bude idona

a kasa na ganni  kwance

Tashi nayi hade da karewa falon kallo tunani na shiga yi shin mai yafaru naganni a nan ganin nakasa tunawa ne yasa na daga kafata daniyyar intafi dakina

Wani abu na taka kamar jini tunani na Shiga yi ina kuma na hadu da jini

Cak na tsaya sakamakon tunani abinda yafaru Dana yi nan gumi yafara keto min jikina yafara rawa innalillahi wa inna ilahir raju una shi kawai nake maimaitawa falon nashiga zagayewa

Tsabar tashin duk lakar jikin mutuwa tayi tsayiwar ma gagarata tayi zuciyata kuwa sai bugawa take da tsananin karfi haka na dafe kirjina kamar raina Zai fita  ina zaune a wurin naji a kiran sallah ni a tunina Nina asuba ce ake kira, agogo na kalla ga mamakina sai na ga ya nunamin karfe bakwai ahhh toh sallah yaushe ake yi yanzu karfe bakwai gabana ne yafadi kaddai yaron Rahma ne ya mutu za a sallah ceshi nashiga ukuna

Kat kat kat jikina ya Shiga rawa, bugun zuciyata kuwa sai karuwa yake  nanfa tari ya sarke ni a wurin

aman jini nafara can kuma idona yafara rufewa na fara ganin duhu but am not ready for dat ina so na San yaron  Rahma yamutu ko bai mutu ba amma ina inaji haka duhu ya mamamye ni "Rahma Rahma Rahma  .........

*******

Jinayi an watsa min ruwa mai tsananin sanyi a firgice na tashi ina cewa " Rahma RahmaRahma........"

Wani mari naji akan fuskata tas kafin nafarkon ya gama register a brain dina nasa
ke jin wani  tuni na dawo hayyacina domin wannan yamafi na farkon 

Tashi nayi tsaye duk da jirin sake dibana dago kaina nayi domin naga Wanda yamin wannan aika aikar wazan gani

ANTY LUBA

Ido na zaro ina kallonta ina  tunanin mai kuma ya kawo Anty luba Dubai

toh kodai mun dawo 9ja ne amma Dana kalli falon saina  gane har yanzu dai muna dubai , kenan zuwatayi tab nabano masifa kan masifa yau ni Ahlam INA ganin RAYUWA

Katse ni tayi daga tunanin dana Lula ta hanyar  cewa "toh bakar makira, muguwa yar gidan Azzalumai burinki baki cikaba domin cikin bai zube ba "

Wata irin ajiyar zuciya mai nauyi na sauke nan naji zuciyata tadan fara sanyi Allah na godemaka dan idan hameed ya sake ni bansan makumataba rayuwata bata da wani anfani in babu shi nasan dayawa zasuji haushina idan suka ji abinda nayi amma da hameed ya sakeni na kwammace  ayita yankan naman jikina kullum domin komai yayi min nasan ba a hayyacinsa yake ba

Jirin Dana ke jine yake kokarin kadani Sauri nayi na tsugunna tareda fashewa da wani kuka Wanda tun jiya nake so nayi amma yaki zuwa sai yau

Salati naji Anty luba tanayi tana tafa hannu  hadi dacewa

"Yau ni lubabatu naga ikon Allah wato dan nace miki cikin bai zube ba shine harda wani kuka kai wannan ya' kin cika shedaniya toh ta Allah bataki ba kuma kina cikin gidan nan za'a haifo mana jariri "

Tashi nayi na barmata wurin na wuce dakina domin idan na tsaya zuciya  zata iya tunzurani nayi abinda zanzo INA dana sani  nakasance mai tsananin hakuri amma fa idan raina ya baci bani da kyau ko kadan

dan  akwai lokacin da muna primary wata yarinya kullum saita tsokane ni, sai ta tara yara suyi tabina a baya suna tsokanata aikuwa ranar datakini bangu uhum doka namata na fitar hankali ko malamai kasa karbanta sukai domin wani karfi ne yan zo min

saida  naga bata numfashi sannan na barta faga nan kowa tsaorona take domin su duk sunsha Aljanu gareni ko malami daina suka sukayi itakuw a wannan yarinyar Allah ne kawai yasa dasauran kwanan ta domin dakyar  ta rayu wannan ne yasa Abbu na yahanani fada koda wasa Yakuma ce duk ranar da nakumayin fada tofa shidai ba Abbu na bane saidai na nemai wani

Amma lallai watarana sainayiwa Anty lubama haka
****************

Waishin ya zaman Ahlam da Anty lubsy Zai kasance

Insha Allahu zuwa dare Zaki sake jina

Fateegamawah taku ce

RASHIN  HAIHUWAWhere stories live. Discover now