RASHIN HAIHUWA

30 2 4
                                    

RASHIN HAIHUWA

GORGEOUS WRITERS FORUM
           G.W.F

Home of gorgeous intelligent and experts writers, we are the best among the rest

This page goes to

Zahra Maman Abba ta SON ZUCIYA HAUSA NOVELS FACEBOOK kullum INA ganin comments naki kuma sosai nake jin dadi

Thanks for the nice comments I really do like it Fateegamawah tana godiya

Page 25

Uhum oh ni naga abin mamaki kam

Haka Anty lubsy ta gyara su nikuma na gyara gurin duk jikin mu a sanyaye yake
Nikam dama nasan za'a rina

Nikam tunda uwa ta  ta haife ni ban taba ganin jaririya baka ba sai diyar Rahma abinda ya kara tada  hankali Anty luba ma kenan domin shi hameed  fari ne tas babu ko sirki itakuwa wannan baka ce silik babu ko alamun zatayi fari nan gaba kai natakaice muku zance dai babu wani abinda yahada su da hameed

Ferfesu naje nahada mata da tea mai dan  kauri kamar yadda Anty luba ta umarta

Kaima tanayi amma me ina isa bakin kofar naji suna ta cacar baki

"Rahma bana wasa dake kifada min wannan diyar waye domin ina da tabbacin wannan ba jinin hameed bace"

Cike da tsiwa ta maida mata

"Ke lubabatu kowa makike kiji ni da kyau wlh kika kara sheganta min diya saina miki rashin mutumci domin nima number one ce a wannan fannin"

Tsabar mamaki kasa magana tayi sai can tace

"Yanzu Rahma ni kike gayawa magana nice fa Wanda tayi miki hanya hameed ya aureki amma wlh daba dan haka ba  Wlh da ko kallo baki isheshi ba " kwafa tayi sannan ta cigaba hade da nunata da Dan yatsa
" ke zaki fada min diyar waye wannan ko saina tattaki daga ke har wannan shegiyar yar taki mai kama da shedanu "

"Ke luba wlh kifita idona na rufe idan kika kara kiranta shegiya wlh sainamiki abinda baki tunani "

Ganin abun nasu bana kare bane yasa nashiga dakin da sallama

Duk juyowa sukayi suka kalle ni nikuwa na sadda kaina kasa naje na aje ina kokarin fita naji Anty luba tace

"Shegiya karuwa  wlh ki gagawar fara hada kayanki keda wannan shegiyar yartakii masa kubarmana gida "

Dariya ta kalkale da ita tare da tafa hannu kana tace "uhum zamuga ni da ke waye zai bar gidan nan banza marar hankali da tuna..."

Ai kafin ta rufe bakinta Anty luba ta wanketa da wani irin  mari babu tantama taga taurari na yawo a sama 

Kokarin kara mata take amma caraf taji an rike mata hannu

Juyawa tayi taga wani ubanne ya rike mata hannu sai kuma tags hameed

"Hameed sakeni na ci uban wannan yarinyar daga ita har shegiyar diyarta "

Tsabar masifa na cinta bata ma lura da halin da yake ciki  ba sai dataji saukar wani lafiyayen mari a fuskarta

Ido tazaro cike da tsananin mamaki da Al ajabi

Nuna kanta tashiga yi tana kokarin magana amma takasa  tsabar wani tururi daya turnike zuciyarta 

Takusan dakika goma a haka kafin tasamu tayi magana

"Hameed ni ka Mara akan wannan ballagazar wanda take kokarin lika maka shegiya marar uba marar ....."

Tsawa yadaka mata "Anty luba tun muna shaida juna kidaina sheganta min diya domin da uban ta "

"Lallai hameed Wuyanka yayi kwari to wlh yau sainaci uban yar nan a gidan nan " nan fa tayi kanta fuuuu

Shiko cikin zafin nama ya kamota ya wullah gefe ai da gudu na bar dakin kar a dawo kaina can ina rakube a jikin labule naga ta fito tana dingisawa da alama dai an ji jiki, dariya ce take kokarin kwace min amma na danne

Dakinta ta wuce wanda ke jikin nawa

Nima nawa dakin na nawuce  nayita dariyata harsaida naji cikina yafara ciwo sannan na dakata uhum Allah ya fara ramamin

Can ina zaune naji surutu a falo ai a tamanin na fito kunsan mi nagani ko wa??

Hameed nagani  rike da a kwatin Anty luba a hannunsa yana ja

dayan hannunsa kuma Anty luba ce yake ja a kasa kamar wata bola

itako sai masifa take tayi tana zaginsa "hameed Dan ubanka nikake ja a kasa, zaka cika ni kosaina tattaka ka anan kuma wlh bazan bar gidan nan ba saina  yi maganin waccen shegiyar "

Shiko ko a jikinsa hasalima janta yacigaba dayi har yakai bakin kofa sannan ya wurgata daga ita har akwatin ta sannan ya cilla mata kudi ya rufe kofar ............

~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~

Eyeeeeeee wlh I can't stop laughing hhhhhhh

Ai Allah ba azzalumim bawansa bane

Taku Fateegamawah

RASHIN  HAIHUWAWhere stories live. Discover now