RASHIN HAIHUWA

26 1 0
                                    

RASHIN HAIHUWA

GORGEOUS WRITERS  FORUM
          G.W.F

Home of gorgeous, intelligent and experts Writers, we are the best among the rest

NOT EDITED

Alhamdilillahi Ala ni'umatul islam

Surely time, life and death all belongs to Allah subhanahu wata'ala,we thanks him for making us among those that witness this blessful month of RAMADAN, may Allah accept all our good deeds and forgive our sins,Ameen
Wishing you a very happy eid-al fitr

Page. 14

Uhum hausawa sukace rana  bata karya saidai uwar diya taji kunya domin gashi yau Asabar, ranar  bikin hameed dina da Deena Anty tsila,

Kuka kam nasha shi, domin kulle kaina nayi a daki nasha kukana, abubuwa sun min yawa a zuciyata, kukan shi yadansa naji relief

Da wane zanji da rashin haihuwar danke fama dashi ko da kishiyar da za'a min

Innalillahi wa inna ilaihir raju un shi nai ta maimaitawa sannan nadan samu sauki

Ganin kuka ba fish she ni zaiyiba  even though naji sauki a nauyin da zuciya ta ke min

Nafiloli nayi tayi ina kaiwa rabbi kukana

Hannu na daga sama nafara addu'a
"Ya Allah ya ilahi ga baiwar ka nan ta na neman haihuwa, Allah Kaine  ar rahemu al maliku al qudus al wahab Kaine kadai zaka iya dauke mun larurata
Allah ka yayemun ka kuma bani ikon cinye wannan jarabawar nida duk wasu masu neman haihuwa"
A lokacin fuskata tayi sharkaf da hawaye idona kuwa sunyi luhu luhu

Kwanciya nayi a wurin Ina tasbihi har aka kira sallar asuba sannan natashi nayi sallah

Saida gari yafara wayewa sannan na bude kofar dakin na fita,wacce take a kulle tun jiya

Hameed na gani kwance a kan sofa yana bacci a takure wuri daya , kuma daga gani anan ya kwana sai yanxu nayi dana sanin kin bude masa kofar danayi Ashe a polour ya kwana

Wasu hawayen ne suka kara zubo min
da  sauri naje na rungume shi na nakara fashewa da wani kukan

Tausayin kaina dana hameed ya kara kamani yanzu shikenan yau a dakin wata zai kwana, a wurin wata macen

Kuka nane ya tadashi daga bacci

kallo na yayi yaga yadda idona suka kuma sai tausayina ya kama shi
Ya kara rungumeni yana lallashina
" is okay sweethearts,kiyi shiru kinsan bani son gani kukan ki, please babe kiyi shiru, auren nan fa da zanyi kinsan ba so nake ba kawai zanyi ne saboda ummah"
Fuskata ya dago, ya kalli cikin idona sanann yacigaba
" Ahlam kinsan babu wata macen da zanso sama da ke, babu wata macen zan kara so a duniya, ke kadaice a zuciya, babu wata,to miyasa zaki bi kina damun kanki bayan kinsan hameed naki ne ke kadai, u know I love u beyond word
So I see no reason  why u are stressing ur self, kinga  yadda idanunki suka zama"hawayena ya shiga goge min

Yana cigaba da cewa" and for Allah's sake babe taya ma zanfara son wannan yarinya, fisabilillahi" yafada yana dariya nima dariyar nayi dana tuna lokacin da mukaje

Flash back a little
Ranar da mukaje gurin deena

Wai harda zuwa da bude mishi mota tana wani fari da ido kamar wata  kilaki
Tana wani cewa "barka da zuwa yallabai"

Hameed kowa yana fita yazo ya bude min murfin motar sannan Nima na fita

Kasa boye mamakinta tayi data ganni amma dayake ita yar duniya ce kawai sai ta matse ta nuna kamar ma bata ganni ba
"ranka yadade ka iso " tafada tana wani lankwasa murya
Nanfa ta shige gaba tana wani juyi da rangwada
Hameed kuwa mizai inba dariya ba harda rike ciki

Sukoko ta tsaya tana kallonsa, tana masa irin kallon 'what are u laughing fo' nan

ganin yana kallonta ne yasa ta fara duba jikinta

Nima dariyar nafara coz I can't help it

Ganin muna Mata dariya ne yasa ranta yayi mugun baci tawuce  ciki da gudu tana kuka,

Haka muka dawo batare da anyi zancenba

Aikowa bamujima da dawowa ba saiga kiran Ummah, haka taimin tatas, da masifa kamar zata cinye ni, harce wa take wai boka na yayi kadan baikai ba

Da gudu na wuce dakina nafada kan gado nafara kuka mai cin rai, hameed ne ya shigo, daga bakin kofa ya tsaya yana sauraren kuka na Wanda jiyake kamar ana hura masa wuta a cikin kunnen sa, a hankali ya tako har inda nake,dago ni yayi a hankali ya rungume a fafadan kirjinsa, nikowa saina kwantar da kaina ina shakar kamshin turarensa mai matukar da dadi, ahaka nayi bacci...

Haka suka maida umma remote, yana yi Mata Abu kadan zata kira tayimana tas nida banyi komai bama amma sai tace ai ni nake sashi yayi koma miye

Flash back  end

Ni na taimaka masa yashirya cikin farar shadda mai matukar kyau, sanann na feshe mai jiki da turare, na dora mai zanna bukar a kanshi Wanda tai mai das, wurin mirror yanufa yana gyara watch dinsa, niko na tsaya Ina kallonsa yayi matukar kyau ya fito cas dashi kamar wani sabon ango, uh kodan ma ai angon ne,take naji wasu hawaye masu zafi sun wanke mun fuska
Ido muka hada ta madubi, da sauri na kauda kaina

Ina kokarin share hawayena naji an rike min hannuna, joyawa nayi naganshi tsaye yana min murmushi,tissue yasa a hankali ya share min hawayen, sannan yakama hannuna ya zaunar dani akan gado sannan shima yazauna, ya kama hannu na yafara cewa
"Sweetheart saboda wannan auren kike ta zubda hawayenki,kike ta damun kanki? Umm? Toh idan duk saboda shine toh ki kwantar da hakalinki nafasa" yafada in a serious tone ................

Cliffhanger😂

Hey sweetie's

Happy eid Mubarak to all Muslim

Ya kuke, ya akayi azumi, dafatan Allah ya amsa mana ibadon mu

Fateegamawah na muku fatan Alkhairi

    Fateegamawah
        Finishing

Do me a favor by clicking that star pls

RASHIN  HAIHUWATempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang