RASHIN HAIHUWA

11 1 0
                                    

RASHIN HAIHUWA

GORGEOUS WRITERS FORUM
          G.W.F

Home of gorgeous,intelligent and experts writers, we are the best among the rest

Written by Fatima Adamu Gamawa
 

                  Fateegamawah

Nagode sosai DA addu'ar ku Allah yabar zumunci

I dedicated this humble page to

*Mrs sulaiman, ya Allah kashare wannan baiwa taka hawayenta kabata diya masu Albarka wanda zasu taimakawa musulunci da musulmai Ameen

*Zainaba Md  I really really love ur comments dear, thank u

*Bouncer faridatou I really appreciate it

Page 17.

A wurin ya kwana, akan kujera rike da hannunta, motsi kadan yaji saiya duba ko wani abun ne yasameta ,

Da asuba shiya taimaka mata tayi alwala tayi sallah,

saida Baba haule tazo sannan yatafi, gida ya wuce direct yadibar musu  kayansu sannan shima yayi wanka, ya shirya,
gidan ummah ya wuce domin yamusu sallama,

A kofar gidan yayi parking na motarshi, fitowa yayi ya shiga gidan fuska a dakile, a falo ya tadda ummah tana shan fruit

"Assalamu Alaikum" daga kai tayi da niyyar balbale shi da masifa, amma ganin yanda shima duk ya fada,ya rame, sai tayi sanyi kunsan tsakanin da da uwa, tuni tausayinsa yakama ta "Wa alaykas salam" ta amsa ba yabo ba fallasa, shiga  yayi yazauna a gefen gujerar da take, "Ummah Ina kwana" ya fada cikin sanyin murya wanda tai nasarar kara sa ranta sanyi

"lafiya klau Hameedu,ya aiki"
"Alhamdulillahi ummah"
"To madallah"

Sai duk sukai shiru, ko wannensu  da  magana a bakinsa amma yarasa ta inda zaifara,sai can yadan yi gyaran murya hade da cewa
"Ummah dama nazo ne namiki sallama, zamuje dubai za'a kara duba lafiyar Ahlam"

Tunda yafara magana ta tsare shi da ido tana tunanin lallai ma ya raina mata hankali

"To bazakuje ba " tafada in an ordered voice
Cike da tashin hankali ya dago  da kansa yace
"Ummah harfa nayimana booking din flight yau da karfe biyar zai tashi,kuma ummah dama akwai wani aikin dazanyi acan din na tsawon shekara daya, kinga kuma babu dadi bantafi da iyalina......"

"Kai dallah rufe min baki iyali ko juya , toh hameed idan fa kaga kayi tafiyar nan tofa da mata biyu katafi,nidai nagayamaka"

Cike da damuwa yace
"Umma Dan Allah kiyi hakuri,  tafiyar nan tana da matukar mahimmaci"

Dan jim tayi kamar mai tunani, shiko harya fara murna
Sai yaji tace "to ai tazo gidan sauki ma, jiya mukai magana da Hajiya kubra,  akwai yarinyar wurinta wacce mijinta yarasu,tana da yara biyu,kaga shikenan sai a daura auren anjima, kaga saika tafi da matarka, tunda dama ni kawai suke jira"

Tab Ana wata ga wata gaskiya bai kamata yayiwa Ahlam haka ba, magana

yafarayi cikin nustuwa

"Aure kuma ummah, gskya ummah idan akai haka ba'ayiwa Ahlam adalciba"

Ido ta zaro hade da dafe kirji sannan tace "hameed ni kake cewa banyiwa matar ka Adalciba , hameed ni" tafada tana nuna kanta,
Cigaba tayi da cewa
"Oh ni Zainabu, ashe akwai ranar da hameed zai fadamin magana,nashiga uku,wannan baiwar Allah tagama Dani,  yanzu kokari ma take tarabani da yaron nawa" nanta Fara matsar kwallar munahinci

"Kiyi hakuri ummah ni banfada da wata niyya ba, amma gani nayi ita da bata da lfy tana asibiti ai bai kamata ayi mata haka ba,amma kiyi hakuri,sai afasa tafiyarma " yafada yan dukar da kai kasa

"Hameed baka isa ba dazakayi tafiyar nan DA bazaka yitaba dole ne sai an daura auren nan a yau kuma ,kuma Dan Allah idan kafasa zuwa kayi canceling din auren kamar yadda kayi wancan baka cika dan halak ba nikuma zan nuna maka ni na haifeka ba kai ka haife ni ba"

Harya bude zaiyi magana tayi saurin Katseshi

"Yi min shiru, bansan jin wata magana masa kaje kashirya karfe biyu za'a daura maka aure da Rahma" sannan ta tashi ta wuce daki,
shiko ya dade a nan yana tunanin da wane ido zai kalli Ahlam,mizai ce mata,cemata zaiyi ana shirin daura masa aure da wacce ko saninta baiyiba, kuma wai a yau,kai innalillahi wa Inna ilaihir raju in, rasa ma yadda zaiyi yayi,
haka dai ya rarrafa ya isa wurin motarshi yajata,dakar ya isa asibitin don saura kadan yabuge wani yaro kawai dai Allah ne ya kiyaye,

A zaune yasameta tanata dariya a abinda baba haule ta fadi mata

A bakin kofa yatsaya yanata kallonta,  jiyake inama ta dauwama a haka, itace ta dago idonta aikuwa caraf suka hada ido wani kayataccen murmushi ta sakarmai wanda take yamanta ma dayana cikin wata damuwa,

karasawa yayi cikin dakin yazauna a gefenta,hade da riko hannunta, baba haule kuwa tana ganin haka tayi waje

Kallonta yafarayi har na tsayin wasu mintuna kafin ya sauke wata ajiyar zuciya mai nauyi sannan yafara magana
"Ahlam inaso kiyi hakuri,kisani cewa duk abunda yafaru da bawa to dama Allah ya kaddara zai faru ne, zan gayamiki wani abu but please try to understand it" kara rike hannunta yayi gam
Murmushi tayi hade da cewa
"Don't worry I will definitely understand it insha Allah just say it"
"Ahlam kiyi hakuri kawai zanyiwa mahaifita biyayya ne , Ahlam zanyi aure  yau da misalin karfe biyu na rana...................

•••••••••••••••••••

Hey dearies

Kuna tunanin Ahlam zata karbi wannan auren kuwa???

Am seriously having writers block😢 please who will tell me what will happen next😝

FatimaAdamu@wattpad

Fateegamawah taku..

RASHIN  HAIHUWAOpowieści tętniące życiem. Odkryj je teraz