RASHIN HAIHUWA

64 5 0
                                    

RASHIN HAIHUWA

GORGEOUS WRITERS FORUM
G.W.F
Home of gorgeous, intelligent, and expert writers, we are the best among the rest.

WRITTEN BY FATIMA ADAMU GAMAWA

Don naga an fara samin sunan tsufi

Habeeba😍😍 ta dandalin mum khady
Note:masu cewa wai nike neman haihu,
Kugane cewa, am a writer, zan iya rubutu akan komai, kuma ai shi writer yana taba bangarori dabam dabam, bawai sai abinda yafaru da shiba ko abinda ke faru dashi so note(Maman zaidu ga amsankinan)

Fans Ina godiya sosai,cikin kankanin lokaci wanga book yasamu karbuwa😍
Inasonku sosai da sosai, dana kusa Dana naisa😘

Fans yaba'a sharing😌😌😌😌

Page 11

Hawayene masu zafi suka zubamin a fuskata, Amma dana tuna da maganar Ammu na sai nayi sauri na goge su, tasha fadamin cewa "Ahlam never show them your weakness,karki yanda ki nu namusu kinyi weak,wannan ne zaibasu damar cigaba damiki kuma miye, always stay strong, Ko yaushe kituna cewa Allah yana tare da ke"

Sauka nayi daga kan gadon nace wa baba haule "Baba haule muje kasa muyi breakfast ko" domin idan dai hameed baya gari tofa tareda baba haule muke cin abinci, kamar kakata haka na ke ganinta ,

Kasa muka sauka amma me, tundaga kan stairs na hango Anty luba zaune
Tadaura daya akan daya tana kallo
A hankali na sauko, na isa parlor sannan nacewa baba haule ta dakko mana da abincinmu
nikuwa sai nasami daya daga cikin kujerun palon na zauna
Mikewa naga tayi zazo gabana ta tsaya tana huci kamar wata zaakanya
Magana tafarayi " to munafuka kingama munafurcin naki ko ,ga dodo kingani shine harzaki wani fara addu'a, yo ai kanki yakamata kiyiwa addu'a Allah ya rabaki da wannan juyancin naki ,shegiya Mai farar kafa, ni wlh banga abinda hameed yagani anan ba haryaje yadebo wa kansa..." Duk yanda nayi kokarin maida hawayena, basu maidoba saida suka zuba, tsaye natashi na hada hannuwa biyu Ina kuka Ina cewa"Anty luba wai Dan Allah minayi muku, haihuwar nan fa Allah ne mai bada ita, ku mafa Mata ne ......"katseni tayi da cewa" daka ta malama , ba wa'axi nace kimin ba domin tunkafin a haifi uwar ki muke zuwa isalamiyyah, annamimiya kawai kin wani ware baki kina bacci, dama ai aikin kenan aci asha ayi kashi,......dama gargadi nazo namiki, kiyi gaggawar sama mana yaro agidan KO kuwa kiyi waje,don duk mu dangin mu babu juya saike,shegiya mai kashin tsiya .....ai naga alama sai naci uwar ki ......."

Ji mukai ance saidai uwarki ba uwartaba .....maganar daga bakin kofa ta fito, kallon wurin nayi😧 wa Zan gani AUNTY BASMA

Karasa shigowa tayi ciki, sannan tazo gaban Anty luba ta nunata da dan ya tsaya, kamar zata cire mata ido tafara cewa" toh sai dai uwarki badai tata uwarba banza marar mutunci kawai tsohuwar ala kwankwan kawai😏 " baki ta bude takasa magana , uhum tasamu daidai ita😂

"Oh toh marar kunyar duniya, jikar shedan" Anty luba tafada tana rike kunkumi,
Zaro ido Anty b tayi tare da cewa "nice kanwar shedan din ai ko yau zakici uban ki, idan kinyiwa Ahlam ta kyaleki
Toni,sai naci uwar ubanki😨(astaqfurullah) gyalenta tacire tadaura a kunkuminta ta shake, sanna taja baya , tareda dunkule hannu kamar wata mai shirin zuwa dambe😡
Nanfa su Anty luba aka fara susa keya aka fara korar kunya da hauka, kuma dama ance tabarmar kunya da hauka
ake nadeta, nanfa tafara cewa " oh yaran zamani Allah ya shiryeki, yakawomiki miki sauki," sumi sumi ta wuce
Tafita kamar wata tsohuwar munafuka kodan muna fukarce ma ai

Nanfa Anty B tadawo kaina tafara min bala'i nima
"Ke kam Ahlma Kinyi asara, da rashin zuciya, nikam Anya ma ke jini nace, haba saikace wanda kare ya lashe miki zuciya, wlh danice dana dade dacin uban ubanta 😂😂" .........

*************************************
Short but sweet

Ina team Anty B😂😂 yau tamin maganin Anty luba

Comments.....put a smile on my face
Share .......kunji masoya
Vote.......love ones
@fateemaAdamu

Fateegamawah loves u

RASHIN  HAIHUWAKde žijí příběhy. Začni objevovat