RASHIN HAIHUWA
GORGEOUS WRITERS FORUM
G.W.FHome of gorgeous intellengent and expert writers we are the bear among the rest
Written by fateema Adamu Gamawa
FateegamawahNOTICE
Masu neman Rashin haihuwa daga farko, da Wanda suka min magana ta PC da ta groups sukaga ban tura musu ba kuyi hakuri whatsapp ne sukai banning dina dakyar nasamu na chanza shi
So kuyi hakuri ga nom. Dina sai kuyi min magana insha Allahu zan tura muku
09071339493Comment dinku shine ke bani courage din typing kuna karantawa amma kamar bakwayi haba Dan Allah
Masu mun sharhi gsky ina mugun ji daku kuna raina 😍
Dada da Balki my terrorist sisters
Duk rashin mutum cin ku dai Ina dan sanku(lol) ILYSMPage 21
Tun sassafe tatashi ta hada breakfast,
Sannan tashiga tayi wanka tadawo falon tana jiran fitowarsu amma shiru
Abu kamar wasa har 1 babu su babu alamar su
Zuwa tayi tadaura lunch inda tamusu fried rice wacce tasha vegetables ga hanta a cikin sai ta musu ferfesun kaza da kuma kunu na gyada mai kwakwa don tasan hameed na mugun sun kunu gyada
Harta gama ta kwashe breakfast tazubar domin babu wanda zata ba kasancewar nan bakamar 9ja bane damuke da Almajirai
Kara shirya wurin dinning din tayi kana taje ta kara yin wanka
Wannan karan TV takunna,nan ta tadda ana nuna wani program datake mataukar so wato twist of fate 2
Haka tayi ta kallonta har kusan 3 shiru kake ji tashi tayi ta kashe kayan kallon ta wuce daki tayi sallah sannan ta kwantaRufe Idon ta tayi amma fir bacci yaki zuwa haka tayi ta juyi akan gado
Tana tunanin mai ya hana hameed fitowa har yanxu mutuminda babu sallar dake wuce shi amma yau shine yau babu ko asubahi hakika wannan mata tashi zata kai shiga halaka
Nan kuma tafara tausayin kanta kenan haka kullum zai dinga mata har na tsawon 2 days yau tabanunta
Kuka ne ya kufce Mata
Shikenan anrabata da mijinta hameed dinta sanyin idaniyarta
Hameed din da ko office yatafi bai awaya biyu bai kirata ba amma yau gashi suna gida daya amma tun jiya batasake ganinsa ba
Kamar ba shine jiya saida tai masa wayoba kafin ya tafi
Ko mi matar nan ta masa Allah ne kadai masani
A haka har bacci ya dauketa..Can cikin bacci tafara jin anata dariya kalkal kal
Tashi tayi tareda jin addu' a dariya tacigaba da ji wannan karan harda tafawa
Da kamar ta share amma dai wata zuciya tace taje dai ta duba in abun farinciki ne ai itama tayasu
Tashi ta hada gashinta in a bun sanann tasaka dan karamin gyalenta na rigar
Fita tayi a hankali turus tayi ganin abin mamaki wai Rahma yargwal ce a akan cinyar mijinta wannan mugun gani dama bata hito ba Aradu kamar takuma amma tasan komawanta zaisa Gwalgwal taga kamar zaji haushi ne
Falon ta karasa tayi sallama
Su sai a sannan ma suka ganta
Murmushi tayi harsaida hakuranta suka baiyana ga dimples nata ga lots a (kamar nawa lolz)
Rahma kuwa ba karamin kullar da ita tayiba amma zatayi maganinta
A kujerar da ke facing nasu tazauna kana ta fara magana
"Good morning habeeby "
Tuni shiko ya tsargu duk kunyata bi ta kamashi
Nan take ya rude yafara kamekame
"Morning habit......." Bai karasa ba yar gwalgwal tafara shagwaba
" my man nicefa habibtynka fa" nan tafara buga kafa wai ita a dole shagwaba
Tuni yakara rikicewa yafara cewa
"Yi hakuri kice mana haba Maman big boy( ohhh) kefa u are a mom bai kamata kina kuka ba ko kina so shima yayi kuka ne
Ahlam kuwa baki sake take kallonsu wai Maman baby misuke nufi a jiyan harta samu cikin???? Wai hameed dinta ne wannan ita Rama rasa mizatayi mamaki ko al ajabi oh rayuwa kenan babu mai fitar DA ita cikin wannan masifa
Sake matsewa tayi ta hanyar cewa
" Rahma ankwana lfy ya gajiya"
Ya mutsa fuska tayi tare da cewa
"Lfy klau anty juy."Wai Anty juy nufinta kenan Anty juya uhum lallai wannan saita garawa yarinyan nan zama hakurinta yakare aitama ba ita ke bada haihuwar ba Allah ne
Dagowa tayi taga wayam duba wa tayi sai hangosu tayi a kan dining yanata kokarin zuba mata abinci
"Hameed" tafada cikin sanyin murya
Har zai dago sai kuma Rahma ta dan bigeshi nan fa ya maida kansa kasa .......
^^^^^^^^^°°°°°^^^^^^^^°°°°°°°^^^^^^^^^°°°°°°°^
Kutayani gani wai Maman big boy yau nagata kaina wai namiji da suna Hajara
Follow comment and vote through wattpad @FateemaAdamu
Fateegamawa loves u so much
![](https://img.wattpad.com/cover/181898347-288-k23306.jpg)
YOU ARE READING
RASHIN HAIHUWA
Non-FictionAhlam baiwar Allah ce wanda bata taba haihuwa ba har tayi shekara goma da aure gashi yan uwan miji sun takura mata har sukasa yayi aure cikin ikon Allah kuwa ita matar daya auran ta haihu sai take tama gori da rashin mutumci