RASHIN HAIHUWA

39 5 0
                                    

RASHIN HAIHUWA

GORGEOUS WRITERS FORUM
          G.WF

Home of gorgeous, intelligent and experts writers,we are the best among the rest

Kuyi hakuri da jina shiru wuyana ke ciwo sosai,amma insha Allahu dana ji sauki update sai kun gaji da ganinsu

Page 19

Ahlam na hango ta sakale hannunta jikin na hameed, suna taka matakallan jirgi a hankali,

Rahma tana bayansu kamar wata yar rakiya

Sai kumbure kumbure take, tsaki tayi cikin ranta tareda cewa "dalla ni malamai idan zakuyi tafiya kuyi, ko kuma ku ba masu Wucewa wuri" amma kamar da gini take magana

Bakinciki kamar ya kasheta

Zuwa tayi ta bangajesu ta shige,

Nan ma ko kulata basuyiba haka taje

tazauna a kujerar dake karshe don ita a Nata tunanin ai dole a tsakiya zai zauna , nan tafara shirya abubuwa iri iri aranta

can tayi murmushi tace"uhum tun anan zanfara kunsamiki takaici(Niko nace kodai a kunsa miki ba )

Su kowa koda suka shigo suka ganta kekam a zaune sai harare harare take,

Ahlam ce tafara shigewa ta zauna a bakin window shi kuma ya zauna a tsakiya

Kwantar da  kanta tayi a kafadansa shiko yana shafa mata kai

Sanarwa akayi akan jirgi zai tashi

nan fa gwalgwal aka Fara zare idon munahinci wai ita a dole tsoro take ji, tana jin jirgi yafara tashi tabi ta ririke shi ta shishige jikinshi tana cewa "wayyo my man nifa tsoro nakeji, wayyo zamu fadi, kaji kuwa yanda yakeyi ....."

Nan tafara kukan shagwaba shiko sukuku yayi yana kallonta ,

Ahlam kuwa dama harta Dan fara bacci taji an bigeta bude ido tayi,

Mizata gani Rahma a jikin hameed dinta lallai ma namiji kamar ba dazu yagama yimata dadin baki ba akan shifa ko ganinta bayi son yi .

amma yanzu gata jikinsa

wata zuciyarce ta kwabeta ai koma miye matarsa ce istigfari tayi sanna ta kauda kanta zuwa window tafara kallon sararin samaniya

Hameed kuwa sai kokarin kwace kansa yake amma ina tarirrikeshi kam masifa yafara mata "ke dallah Malama ki cikani " amma ko  gizau bata yiba,

ta cusa kanta cikin rigarshi tana ta masa kukan shagwaba, shiko bakin ciki kamar ya kasheshi tsoronsa kar Ahlam tajiyo tagansu a haka

aikuwa kamar dawasa yajiyo tajiyo caraf suka hada ido murmushi tamasa sannann tajuya shiko kunya kamar kasa ta bude ya shige ciki

Mutuniyar kuwa tana nan takara lafewa,

Jin yayi shiru ya daina kwatar kansa yasata tunanin yasaduda

nan kowa bata San cewa bari yayi saita sake sannan yayi maganinta

Can harsunyi nisa yaji tafara sauke numfashi alamar tayi bacci, saida ya hada duk karfinshi sannna ya tunkudata saigata tana lilo ita bata fadi kasa ba sbod sit bealts din dake jikinta,

tana cikin mafarki waigata nan ita da  hameed dinta sunata shawagi a sararin samaniya, sai kuma taji kamar dagaske ma yawon take,

ai a tsoro ce ta tashi , sai ganinta tayi tana lilo tsakanin kujera (hhhhhh) 

dakyar tasamu takoma tazauna

kana takalli hameed taga yajuya wurin Rabin ransa sunata hira harda dariya da tafawa

Tab amma man din nan yama raina Mata sense wato shiya hankadota
Amma a hankali zaidawo hannunta

A wurin fitowa ma anyi didima domin suna fitowa tayi saurin makale hannunta a nasa wai duk dan taba Ahlam haushi

Itakuwa baiwar Allah murmushi kawai tayi tawucesu taje ta shiga motar datazo daukarsu

Shiko dasauri ya cire hannunta a jikinsa tare da nuna ta da Dan yatsa game dacewa '

"Ke wallahi bari namiki last warning idan kika kara tabani wlh saina babballaki banza mahaukaciya ke idan kinsan yadda na natsaneki da baki kwatanta rabata wlh "

"Abdul nikuma ina sonka so marar musalatuwa kaima da kasan irin sondanake maka da bazakace ka tsanine ba haba Abdul miye ajikin wancar banzar da babu a jikina "

Tsaki yayi ya wuce domin a ganinshi magana da ita bata lokaci ne .......

•••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••

Find me on wattpad at FateemaAdamu

Fatima Adamu Gamawa AKA Fateegamawah

Insha Allahu anjima ma zakujini              

          Finishing😝

RASHIN  HAIHUWAWhere stories live. Discover now