Chapter 34

729 80 23
                                    



Koda suka shiga cikin mota itadai Islam Batace komai ba shima haka , tada motar yayi suka fara tafiya. Wakar Try again by wande coal ne yake tashi a cikin motan, ganin da yayi shirun yayi yawa yasa ya kashe wakar Yai parking ya kamo hannunta yana murzawa a hankali, yace " How're you feeling right now love ?" Kallonshi tayi cikin ido sai ta dauke idanunta tace " Gabana har yanzu yana faduwa, love Inajin soro." Sa gudan hannunsa yayi ya kamo gudan hannunta " Baby Zaki yarda dani idan nace maki babu abunda zai faru da yarda Allah, Amnah bata isa ta cucar dake ba insha Allah.ki fida duk wani soro ki kwantar da hankalinki kuma ki kula da kanki  , please Babyyy ." Ya fada please Baby cikin sigar lallashi. Smiling tayi tana fadin "Insha Allah." Yace "I love you so Much love." Itama ta mayar mai da " I love you too." Tana dukar da kai, murmushi yayi ya cigaba da driving yana mamakin kunya irin tata. Can ta saki jiki suka cigaba da fira irin ta masoya.

Mom ce take kai da kawowa ita kadai a daki tana tunanin yanzu ya kamata tai proceeding plans inta. Can kamar ance mata wani abu kawai ta dauki hand bag inta da key in mota . Haka ta fito ta wuce Dad dake zaune yana karatun newspaper dukda shima hankalin ba kwance yake ba ganin abunda ke faruwa, sunanta yashiga kira amma ina ko sauraronsa batayi sai tafiya take yi , da yaga bata da alamun sayawa ko sauraronsa yasa ajeyi jaridar ya tashi ya bita a baya . Har ta fito yana binta bodyguards inta ne suka shiga binta ta juyo tace daka masu sa'wa " stop following me fools." Sai ta shiga nuna sauran bodyguards inda ke compound in tamkamemen gidan tana fadin " where are the rest ? Micheal go and call the rest right now !!!" Da gudu Micheal ya ruga kiran sauran sai tasa Obinna ya kira sauran wada basu kusa ta waya yace duk Suzo yanzu. 

Kasancewar gidan baban gida ne zai kusan yin unguwa daya , obinna ya kira wasu ta waya da duk suna cikin gidan amma sunyi nisa da suzo wurin main parking lot Madam na kiransu. Dad ne ya maso kusa da ita a hankali yace " wai mi kike shirin yi ne sarah? You seem to be tensed , the best solution shine ki koma ciki na kwantar maki da hankali banga amfanin tashin hankali ba my dear ." Cikin daga murya da fushi tace " Toh cemaka akai ina bukatan ka kwantar man da hankali? Ko kana nifin banda hankali ne? Baka ganin abunda ke faruwa ne wai? Oho ni na manta aikai bai dameka ba ko ?" Gudun fitinarta yasa Dad cewa " waye yace maki ban damu ba? Ni ina yin abu ba tare da wani tashin hankali ba?"

Wata dariyar rainin hankali Mom tayi tace " daga baya kenan inji Malam Bahaushe , listen to me carefully Khalid......" sai ta rage volume muryarta yadda shi kadai zai ji abunda take fadi " 18 years back kasan ko kai wanene a lokacin, kasan ko ni wacece kuma har gobe nice Sarar da ka sani 18 years back, kafi kowa sanin what am capable of doing huh? So ina baka shawara da ka goya man baya kamar da kokuma ka gane ba ayi bani wani da zaiyi crossing ina ba. Dan har kai bazan kyale ba I won't spare you my dear." Sai ta masa daga kusa dashi ta shiga kallon bodyguards in wurin taga duk an kira kowa harda bodyguards in Mr Fauzi dama bada su ya fita ba ,da masifa ta shiga yi masu magana " ku bakusan aikin ku bane? If you're not being careful you will surely loose your job!!!" Bodyguards in Mr Fauzi ta kalla tace masu " especially ku innan, wawaye kawai tayaya zaku bari wancan banzar tazo kusa da da na har tai manipulating inshi ta fara soyyaya dashi? Imbecile, fools ungrateful idiots kawai!!! Salon gobe ku bari tazo kusa dashi kuga abunda zan maku mumus ku bace ku bani wuri." Bodyguards in Mr Fauzi suka bar wurin, sauran bodyguards in ta kalla suma ta daka masu sa'wa " dan ubanku ku bace ku bani wuri." Suna tafiya Dad shima ya juya ya koma ciki jikinshi duk yayi sanyi .

Tafiya tayi taje gaban motar da zata shiga ta zaro key zata bude motar drivers inta kusan su biyar da gudu suka zo wurin wata harara ta wasa masu tace " uban wa ya kira ku?" Da sauri suka bar wurin, shiga tayi cikin mota kirar Mercedes G class black mai tint, ta tada mota ta shiga driving gate man ya wangale mata gate da wani irin masiyacin guda take driving.

Koda Mr Fauzi ya kawo Islam gida saida ya shiga ciki ya gaida Ummi har sukayi dan fira da Ummi harda Farha, sosai ya saki jikinshi dasu haka suma. Har Ummi ta hada mai coffee ☕️ yasha abinci kuma sukai mai tayi yace bayajin yunwa, ba yadda Ummi batayi dashi ba amma yakici yace next time in ya dawo. Haka yadan jima yai masu sallama ya tashi ya fito zai tafi Islam ta biyo bayanshi zatai mai rakiya saiga Farha itama ta biyo, harararta Islam tayi Farha tace " Stop eyeing me nima zan raka Brother in law na ." Mr Fauzi yace " let's go don't mind her ni ai saboda ke na zauna mukai fira." Islam tace" kuyi ku gama na gaba yayi gaba." Mr Fauzi cikin zolaya yace " ko yayi gaban wani zai iya kamo sa ." Farha tai dariya tace " Brother in law ashe kana jin hausa sosai ?" Yace " ke yarnan Hausa ne dani kamar jakkin kano." Dariya sukayi itakau Islam sai cika take wai ita bai kyauta mata da yace Farha zata iya kamota, yace " sister in law next in zan dawo zan taho maki da wasu novels you will like them ." Farha tai salle tace " you the best , you're my favorite." Yace " give me five." Suka kashe I mean high five . Farha tace " bye favorite." Shima yana mata waving yana " bye bye my girl ." Harsai da yaga Farha ta shige sannan ya kalli Islam da ta gama cika, ai yana ganin mode inta yace " Allah ya huci zuciyar Hajiya, mi kuma ya faru." Islam tace " Au baka san abunda kayi ba?" Girgiza kanshi yayi alamar eh tace " bye bye." Ta juya da niyar komawa cikin gida taji ya kamo hannunta ya maido ta, yana murza hannunta a hankali yace " forgive your Favorite love , in Favorite ina na fushi dani ya zanyi?" Dan bugu ta kaimai a kirji yace ouuchhh tace " I forgive you amma nice your girl not Farha okay?" Kada kai yayi " I love you my girl ." Itama tana smiling tace "I love you my favorite." Yace " I love you more my girl ." Sai itama ta kamo hannunshi tana murzawa a hankali tace " I love you the most ." Mr Fauzi yace " I love you more than me ." A haka sukayi bankwana ya shiga mota ya tafi sai da tabar ganin motarsa sannan ta shiga ciki.

Minister's Son Where stories live. Discover now