Chapter 33

914 105 30
                                    

  Tunda ta kira shi taji wani dan sanyi a zuciyarta saboda ta fara suspecting Mr Fauzi ya fara son Yarinyar nan dan haka zama sam bai ganta ba. Fitowa tai daga dakin nata taje kitchen nan ta iske masu aiki wasu na wanke wanke wasu na chopping vegetables sai masu baking da cooking. Wurin coffee machine ta wuce ta hada mai black coffee ☕️ sai third floor, ko da ta isa bata kowa a sitting room ba sai ta wuce dakinshi ta turo kofar ta shiga, kwance ta iske shi a resting chair ya rike remote na dstv yana flicking channels in. Murmushi kwance a fuskar sa, "miyasa kake ta murmushi mood inka tunda ka dawo kake farinciki what happened?" Kallon Mom yayi dake saye a gefenshi rike da coffee ya kamo hannunta "Mom zan fada maki komai amma ba yanzu ba I want to surprise you." Daga gira Mom tayi itama sai tayi murmushi ta dauka ko batun aiki ne miko mai coffee tai "oya tunda da alamu baci abinci zakayi ina nan har sai kasha coffee innan." Karba yayi ba gardama ya kai baki yai sipping sai ya kalleta " Mom yayi dadi sosai." "Yau na fara hada maka coffee ne da zakace yayi dadi koko duk cikin dadin da kake ji ne?"

"Nop Mom kullum yana dadi." Hannu tasa cikin sumar shi ta yamusa gashin kanshi ta fice tana "good night my lovely son ." Shima da "sleep tight my first love." Ya bita, wayarshi dake gefenshi ya dauko ya shiga tura ma second love inshi text message ."

Islam dake zaune kan gado Farha ta kwantar da kanta kan cinyoyinta tana fada mata yanda rayuwarsu take a office sukaji karar shigowar text message, cikin zumudi Farha tace "Adda ki duba maybe Future brother in law ne ." Daukar wayar tayi ta duba sai taga yana cewa Good night love. I love you ❤️ kiyi mafalki na kinji? Dan dariya tayi ta aje wayar Farha na fadin "soyyaya dadi"

Washe gari ta tashi ta shiga wanka ta fito ta shirya cikin black suit inta tana daukar wayarta taga notification na text message in Mr Fauzi Good morning love . How was your night? Cool insha Allah, I love you ❤️ kulle Idanunta tayi tana mai jin soyayyar mr Fauzi cikin zuciyarta tafito sukayi breakfast dasu Ummi tai masu bankwana ta fito,tana fitowa taga bunch of flowers 💐 masu kyau masha Allah sai wani dan kati ta bude ta karanta kalaman soyyaya daga Mr Fauzi aje flowers in cikin gida tayi ta wuce office.

Ba karamin farinciki yayi ba da kiran da Mom tayi mai shi zaice mutuwar Mami yasa zai samu Islam? Mutuwarta rabo ce kenan? Saboda da tana raye to tabbas ba zata bari ya auri Islam ba.Hada kayanshi ya fara yi dan zuwa Abj ya kamashi .

Cabinet inta ta zauna da gangan yau tanaso ta gwadashi dan bazata je office inshi gaishi shi ba kamar yanda ta saba. Mr Fauzi kuwa yau tunda wuri ya shigo office dan yaga love of his life yaji shiru staffs ba karamin mamaki sukayi ba ganin shi da wuri amma har yanzu baiji ta shigo gaishe shi ba itakuwa da gangan tayi hakan . Haka ya jira yaji shigowarta amma Sam ba alamanta mikewa yayi ya fito,da mamakinsa ya ganta zaune tana aiki a desktop. Folding hannunsa yayi ya saya a kanta itakuwa tana jin scent in turarensa sai tayi kamar batasan da mutum a kanta ba. Shikuwa kallonta ya saya yana yi yaga ko zata dago da yaga bata da alamun kula sa yasa yace " love I know you're pretending baki ganni ba" dagowa tayi ta kalleshi tace "wa'alaikumussallam I'm fine Alhamdulilah." Smiling yayi yace "Nima am good Alhamdulilah." Amnah ce tashigo dukansu kallonta suka shiga yi tace "Hello Baby I wanna talk to you privately." Tafada tana hararan Islam, ya lura da kallon banzan da take ma Islam yace "Look at me kifada abunda za kice and leave." Batayi mamaki ba amma abun yadan sosa mata rai saboda gaban wannan banzar zai mata haka? "Haba mana I said privately."

" Kinsan mi ? Idan ba zaki fadi abunda kikazo fadi ba then just leave!!" Wani haushi ya kamata wai miyasa zai dunga disga ta a gaban wannan banzar? " I want us to have lunch together ." Kallon Islam yayi datayi kaman tana typing a wayarta sai ya maido da kallonsa wurin Amnah yace " I appreciate amma I have other things to do with Islam." Haba ai Amnah ji tayi kamar ya mareta wani kallo da tayi ma Islam sai ta fita fuuu . Bin Amnah yayi da kallo har ta fita ji yake inama ace zata yarda subar relationship insu a masayin brother and sister the moment he trie getting close to her a masayinshi na brother inta a lokacin zata gwada mai other way round so dole yake mata haka ko zata hakura ta kallashi a masayin brother inta. Cema Islam yayi "love zan shiga office na dauko abu ki shirya we're going out."

Minister's Son Where stories live. Discover now