Chapter 25

954 108 17
                                    

Ranshi ba karamin baci yayi ba , Wai mi ma yasa Mami takawo mai wannan sakarar a masayin PA ? Mikewa yayi ya kira Adeel ta waya yace ya fito su fita gashi nan fitowa , yana fitowa ya kalli kofar office inta , dole ne yaje da ita tunda PA inshi ce zatayi mai amfani . Knocking yayi ta bada izinin shiga ya tura kofar ya shiga , duba wasu takardu yaga tana yi , tana ganin shine ta mike tana tambayarshi " Sir mi zanyi ." Kallonta yayi mai kamar harara yace " let's go." Yayi gaba , handbag inta dake kan table ta dauka tana binshi a baya .

Cikin Rolls Royce taga wani Bodyguard ya bude mai kofa ya shiga , sai Lexus guda hudu ,biyu a gaba biyu a baya duk da tinted windows . Saye tayi ta rasa ya zatayi sai ta hango Adeel yana fitowa daga company in , yana ganinta yace tashiga a cikin daya daga cikin Lexus , sai ta shiga daya daga cikin ta baya . Shikuma Adeel ya shiga cikin Rolls Royce in da Mr Fauzi yake ya zauna a gaban motar .

Nan suka hau hanya , abun ba karamin mamaki yaba Islam ba ganin motocin basa bin ka'idar traffic lights Kuma ga road safety amma basa saidar dasu saima bin motocin da suke da kallo suna daga masu hannu wai su sunga mai kudi , gashi gudu suke kamar zasu tashi sama .

Mansir ya gama hada jirkarshi ta zuwa garin masoyi ,ya fito yayi ba yan gidan bankwana ya hau mashin sai tasha . Ladingo da Talatu ba karamin takaici suka jiba , wai wurin wannan banzar zaije .

Maiduguri Kuma Alhamdulilah , komai lafiya lau . Su Dad da Mom sun dade da komawa Abuja tun ranar da Mr Fauzi ya dawo suma suka biyo hanya suka dawo . Farha na kwance kan gado taji sanyin AC ya mata yawa ta dauki remote ta rage sanyin . Kiran Muhsin ya shigo ta duba Caller ID taga Muhsin ne tai picking tana jin wani irin dadi ganin ya kira ta , " Hello beautiful ." Cewar Muhsin , Farha tai murmushi tare da amsawa " Hi Handsome ."  Shima murmushin yayi mai sauti yace " Hope you're doing good ." Tace " I'm good what about you ?" Yace "Splendid." Shiru ne ya rasa can Muhsin yace " Wanna go out on a date with me ?" Farha tace " Yeah what time ?" Yace " Around 5pm ." Farha tace " Perfect timing ."

" See ya ." Cewar Muhsin tareda ending call in . Ta mike ta bude closet inta ta zaro wata fitted riga warda Muhsin yasa ommaberry tayi mata , contemplating take tasa rigar kokuwa ta duba cikin hadadun rigunan da Mami tasa Amnas closet sukayi mata . " Wannan ma hadada ce " tafada tana kara yiwa rigar kallo . Wurin jewelry box ta nufa ta bude , kallon jewelries in dake ciki tayi sai ta sake bude wani jewelry box in da Muhsin ya bata . Duk sanda zata bude jewelry box inta guda biyu da wanda Muhsin ya bata da wanda Mami ta bata sai tayi wa Allah godiya dankau cikin box in zinary ne kawai . " Bari In dauki necklace cikin jewelry box inda Muhsin ya bani tunda we're going on a date with him ." Tace tana dauko wata sakar gold , haka ta gama hada kayan da zata sa ta ajesu kan gado .

Bayan sun fito daga meeting in ya fada mota itama ta shiga cikin warda ta shiga dazu , kallon jotter in da tayi jotting in important issues in da Mr Fauzi yayi discussing da Dangote tayi , maida jotter in tayi cikin handbag inta ta maida kallonta kan titi . Gani tayi an bude gate in wani Mansion sun shiga , kamar tayi magana sai Kuma tai shiru ta fito lokacin da aka faka motocin . Gani tayi ogan ya shige bodyguards in Kuma sun saya nan waje . Adeel yace mata " Shigo ." Binshi tayi a baya suka shiga , tana shiga saida numfashi ta ya kusa dauke wa , wato akwai irin gida jen nan da take gani a tv , Adeel ne ya ce mata ta zauna shikuma ya haye bene ya tafi wurin Mr Fauzi dake third floor.

Wata maid ta kawo mata cinnamon rolls sai Chapman , daukar cinnamon rolls in tayi tana ci ba karamin dadi yayi mata ba . Mom da fitowarta kenan ta shirya zata je Villa wurin kawarta First Lady , ta sauko first floor mi zata gani ? Badai diyar Afrah bace ko tace diyar Khalifa , zuwa tayi har gabanta dan ta tabbatar ma idanuwanta , Islam kuwa gani tayi wata mata kamar tasan fuskar oh wannan matar ce warda suka hadu wurin kofar dakin Mami mara mutunci nan .

Gaishe ta Islam tayi " Ina wuni ." Harara Mom ta wasa mata tace " Who gave you the permission to sit on that chair ." Mikewa tayi tace " Kiyi hakuri Adeel yace na zauna ." Mom tace " Adeel kuma ? Tare kuka zo ne ? "

" Eh tare mukazo ."

" Maiyasa yazo dake nan ?" Mom ta tambaya tana hade jira . Islam tace " Mr Fauzi yazo nan dani ." Mom batasan lokacin da tace " What !!!"

" Daga wurin meeting muke so sai ya tafo nan ." Mom gabanta ya shiga faduwa Wai mike faruwa ne tace " Mi yasa zai tafi wurin meeting dake ?"

" PA inshi ce ni ." Mom ta sake cewa " What the hell ." Da karfi tana hucin takaici tace " Shi ya ganki yayi employing inki ?" Islam tace " No Mami ce tasa a bani masayin PA inshi ." Mom ta runse idanunta sai ta bude sai da gaban Islam ya fadi ganin yanda ranta ya baci , Mom cikin bala'i tace " Fitar min daga gida tunda ba gidan ubanki bane ." Islam ta juya ta fita , tana fita ta kira Mr Fauzi dan taji in aikin ta na yau ya kare  .

Adeel na zaune a dakin Mr Fauzi yana chatting yaji wayar Mr Fauzi ya dau kara , har ta gama ringing ba'a dauka ba sake kira Islam tayi , Adeel kuma ganin an sake kira ya duba Caller ID in yaga num , karar rife kofa yaji ya juyo yaga Mr Fauzi ne ya fito daga Wanka towel daure a ugunshi . Miko mai wayar Adeel yayi yace " Anata kiranka ." Wayar ya karba yayi picking , Islam tace " Sir na kira naji in aikina na yau ya kare ." Wai wannan wace irin sakara ce ya fada cikin zuciyarshi yace " What sh**t are you talking about ? Okay na gane tunda you're a zombie I have to tell you in lokacin aikinki ya kare ! Hy zombie are you  listening to me go home we're done for the day ." Yana gama fadar haka yai ending call in , Islam kuwa danne zuciyarta tayi kamar yarda Mami ta fada mata she has to be strong ta fice ta koma office ta dauki motarta ta tafi gidanta .

Kamar ta fashe saboda bacin rai wato Mami tanaso ta dawo da family in Khalifa kenan lallai Mami tana wasa dani . Wayarta ta dauka ta kira kawarta ta fada mata tareda fadin " Kema kinsan bazan bari aikin da na dade Ina yi ba ya tafi a banza it took me 18 years kafin nasamu abinda nakeso kema kinsan yanzu I won't backup . " Kawarta tace " kwantar da hankalinki Sarah sai ki tura Mami inda kika tura Khalifa shine kawai solution ."

Wani murmushin mugunta Mom tayi tabbas wannan shawarar zata dauka , zata tura Mami inda ta tura Khalifa .

Kuyi hakuri muna biki .

Minister's Son Where stories live. Discover now