Chapter 44

390 35 11
                                    


Kallo daya zakai yimai kasan cewa yana cikin damuwa sosai , hankalinshi a tashe yake matuka. Dafa shi a kafada Mom tayi itama tana kallon Nanny Bonel dake cikin Coma , Mr Fauzi yace " What do I do now ? Nanny Bonel is unconscious itakuma Nausheen tana wurin marasa imani, Mom na rasa mi zanyi na rasa ta ina zan fara . Da wane zanji ?  Bansan mike shirin faruwa dani ba don in har na rasa Nausheen I don't know what will happen to me ." Mom tace " kada kace haka karka damu zamu gano ko waye behind all this kuma zai gane yayi crossing in wrong mutane , go home and take some rest kabar komai a hannuna."

" I can't diyata na hannun kidnappers bazan iya samun hutu ba harsai na gano ta , Mom please ki kula da komai anan, zanje in maida Lala gida na tabbatar ta samu bacci nikuma zanyi nawa investigation in ." Gaban Mom ya fadi tace " No my dear kada ka damu police zasuyi aikinsu kaima kaje ka samu Hutu kafin gobe za'a samu cigaba a case innan."  Smiling in daya fi kuka ciwo Mr Fauzi yayi ma Mom yayi mata peck a goshi ya kamo hannun Lala yasa ta a mota suka wuce gida . Bayan fitarsu Mom ta kalli Nanny Bonel dake kwance unconscious tace " bansan miyasa bimbim ya damu dake ba , kefa mai aiki ce amma wai ni yasa na kula dake can you imagine ? Kuma sai faman kashe kudinsa yake don a ceci rayuwarki abun haushi ." Kallo daya daga cikin masu aikin Fauzi Mansion da aka kawo don suyi jinyar Nanny Bonel tayi tace " sai ku cigaba da jinyarta duk abinda ake bukata ku kira chef Halima." Suka amsa da to itakuma tabar asibitin.

Suna isa gida ya wuce da ita dakinshi , ya shiga kitchen ya hada mata coffee yazo ya lalasheta Tasha ya dinga fada mata kalamai masu dadi Yana assuring inta Zuwa gobe Nausheen zata dawo har ya samu ya sata bacci , ya lulubeta ya mike ya shiga dakin Dad ya zauna yana kallon Dad . Yace " Dad Nausheen has been kidnapped..............." bai samu karasa abinda zai fada ba yayi saki baki yana kallon Dad cike da mamaki , Mike hannunsa Dad keyi harya shafa kan Mr Fauzi yace " Ba kidnapping inta akayi ba , it was all planned." Ai Mr Fauzi saboda sananin rudewa bai maida hankali akan abinda Dad yace ba yace " Dad kaine kake magana, kuma ka mike hannunka. How ? When ? Tayaya ?" Da mamaki Mr Fauzi yaga Dad yana mikewa saye , Dad na gama mikewa ya bude hannayensa yace " I'm back son ."

Mr Fauzi yayi hugging insa sosai yana kwalla don ya dauka hallucinating yakeyi saida Dad yayi breaking hug in suka zauna Dad yace " Nasan kada da tambayoyin da kakeso kayi man kafin kayi man duk zan baka amsoshin su amma inaso kayi man taimako guda daya ." Mr Fauzi " wane irin taimako ?"

" Inaso abinda ka gani ya zama secret banaso kowa ya sani including your mother." Mr Fauzi yace " what ? Mom fa kace ?" Dad yace " Eh Sara ." Mr Fauzi ya mike duk ya zama confuse yace " why ?" Dad ya dafa kafadan Mr Fauzi yace " Trust me son promise me bazaka gaya mata ba when the right time comes zan fadama miyasa nace haka." Muryar Mom sukaji tana yima chef Hafsat fada alamun tana tunkaro dakin Dad yai sauri ya koma kan gado ya kwanta ya cema Mr Fauzi " Ka zama spy ka bincike Mom in kanaso ka gano Nausheen." Mr Fauzi yace " What !!!" Da karfi daidai lokacin Mom na shigowa tace " Lafiyarka Bimbim?"

Juyowa yayi ya kalleta saida yayai kamar minti shida yana kallonta sannan ya juya yaga Dad ya koma kwance kamar ba shine ya gama magana ba, shiru yayi yama rasa mi zaice sai kallon Mom da yake. Tunkaro tayi har tazo gabanshi tasa hannayenta kan face insa tace " Are you okay my dear ?" Kallonta kawai yakeyi can yasa hannunshi ya cire hannunta ya fice daga dakin. Binshi tayi da kallo cike da mamaki can sai ta kalli Dad tana zargin anya Dad bai yima Mr Fauzi alamun wani abuba game da ita ? Shiko Mr Fauzi yana shiga dakin ya dinga kai da kawowa yana tunanin abunda Dad ya fada mai, kuma miyasa Dad ya boye ma Mom cewan ya samu lafiya? Shi duk kanshi ma ya daure amma there's something fishy going on in this house wanda bai da masaniya, da sauri ya dauki wayarshi ya shiga kiran number in Muhsin saidai yaji switch off .

Da mamaki ya wayar hannunshi da kallo shidai yasan tunda yake bai taba kiran Muhsin ba aka ce switch off , zama yayi a bakin gado still idanunshi na kan wayar hannunshi cike da mamaki. Kira ya sake yi nan ma switch off sai kawai ya duba number in Amnah ya shiga kiranta ta FaceTime, bugu uku zuwa na hudu ta daga. " Hello bro how're you?" Mikewa yayi yace " Amnah is Muhsin with you ?" Da mamaki tace " No bro ai ina South Africa fah Muhsin kuma yana nan Nigeria ." Cusa hannunshi yayi cikin sumarsa " shit ,I can't reach him kinsan inda yake kumyi waya ya kashe phone inshi." Da mamaki Amnah tace " No way Muhsin baya kashe wayarsa saidai in wani abun ya sameshi please bro ka bincika am sure hakanan bazai kashe wayarsaba." Ce mata yayi " ki kirasa kuma don't stop calling him keep trying nima nan zan bincika." Yana gama fadin haka ya kashe wayar ya fito straight dakin Dad ya nufa domin ya Dad ya fada masa mike faruwa sai ya tarar da mom a dakin , Murmushi ta sakar mai sai kawai ya juya ya fito . Mamaki sosai Mom tayi tabbas akwai abunda ke faruwa shiyasa zata zauna dakin Dad daga yanzu .

Yana fitowa ya nufa dakin Muhsin sai yaga wata maid tana fitowa daga dakin Muhsin, duka kanta tayi a kasa ta gaishe sa ko kallonta baiyi ba ya shiga ciki . Bai ga kowa ba yai knocking bathroom nan ma shiru ya bude kofar ya shiga babu kowa sai ya fito ya shiga closet insa nan ma bai ga alamun ya dauki kayansa inma tafiya yayi bin dakin yayi da kallo kamar yanaso ya gano wani abu har ya gama bin ko ina da kallo sai ya fito ya nufa dakin Mom .

Yana zuwa bakin dakin Mom ya dunga tunanin anya abunda Zaiyi ya dace kuwa ? Maganganun Dad sun saya masa a rai , yana tunanin anya abunda yakeyi na zargin mahaifiyarsa ya dace kuwa ? Kawai wata zuciyar tace Mai Nausheen fa na hannun mugayen mutane , a hankali ya daura hannunsa kan handle in kofa ya murda jiki a sanyaye. Yana shiga ya dunga bin dakin da kallo sai ya nufa beside drawer inta ya daura hannu kenan zai bude yaji ance " Are you looking for something dear ?"

Kulle idanunsa yayi ya sauki numfashi, can ya bude ya mike ya juyo ya kalleta . Murmushi ta sakar Mai tace " Kamar kanason ka tambaye ni wani abu , go ahead am all ears ." Kallonta kamar zaiyi kuka sai yace " Mom dan Allah ki fada man abunda ya kamata naji wanda bai dace naji gurin wani ba..... please........ please Mom ." Gabanta taji ya fadi saiga kwalla sun taru a idanunta " My dear kana zargi na ? Why ? Why Bimbim? Bayan duk irin son da nayi maka ? I love you more than I ever loved myself, duk abinda kaga nayi is for your own benefit. I'm disappointed in you , I don't deserve this ." Tafada kwalla na zubowa a idanunta da sauri yasa hannunsa yana share mata hawayen ya rungumeta " Dan Allah Mom ki daina Zubar da hawayenki saboda ni , bala'i ne a gurina nayi kuskure ki yafe man you're a mother too nasan kinsan yadda nakeji akan kidnapping Nausheen idanuna sun rufe saboda Nausheen I want my daughter back at any cost I'm so sorry."

Breaking hug in Mom tayi tace " is alright na yafema Allah yayi ma albarka ina fatan kaima zaka gane duk abunda nakeyi saboda I love you so much my son and I want the best for you , a mother can kill for her child right?" Peck yayi mata a goshi ya fito dakin ya nufa dakinsa . Tana ganin ya fita ta zaro wayarta ta kira Faty , tana dauka Mom tace " Bimbim ya fara zargi na yanzu kisa number onga a wayar Islam kuma ki kirashi da number inta yanda zamu maida shi kamar itace mastermind behind Nausheen's kidnapping da kinyi wannan kin gama aikinki kina iya komawa katsina the money will be transfer to your account immediately kin gama ."

Wani dadi faty taji tace " shikenan na gama ? Nagode Madam nagode sosai Allah yaja da ranki."

Minister's Son Where stories live. Discover now