Chapter 16

979 81 17
                                    

  Turo kofar dakinta yayi,  zaune take tana karanta Magazine smiling yayi dan Mami akwai karatun newspapers da Magazines. Bataji shigowar saba sai kawai taji ya rungume ta ta baya , kamshin turarenshi yasa tagane shine " Sai yanzu ka dawo ni nayi fushi ." zagayo wa yayi ya zauna kusa da ita tare da shagwabe fuska kamar karamin yaro " Mami am sowwie ." dariya ya bata yanda yayi maganar " Fauzi ko danka ga baka da aure ne shiyasa kakai dare a waje? " Bata fuska yayi dagajin Mami ta fadi maganar aure danshi yanzu kwata kwata aure baya gabanshi .

Murmushi Mami tayi dan tagane mi yake nufi da bata fuskan nan da yayi " Basai kayi fushi ba Fauzi dan inda sabo na saba duk sanda nayi maka maganar aure sai kayi fushi....."Kamo hannun shi duka biyu tayi cikin tausasa murya kamar zatai kuka tacigaba " when are you getting married ? Until I stop breathing....." Da sauri ya katse ta " Mami please don't say that again. " Mami tace " To sai yaushe for how long will you stop being a bachelor?

Mikewa yayi tare da zura hannayenshi a aljihu yana kallon hoton Mami dake a dakin, shidai ba aure ke gabanshi ba Mami ta dade tanamai maganar aure har ya soma gajiya. Yasan Mami ba lafiya ta ishe taba tana fama da heart attack kuma har da rashin yin auren shi ke damunta har blood pressure inta ya dinga hawa, shidai mata suna san shi he's every girl's dream amma shi har yau Allah yasani baiga macen da tayi mai ba , rumse Lemon green eyes inshi yayi ya zaiyi da Mami?

Dafa kafadan shi yaji anyi juyowa yayi ya zuba mata lazy kuma oily lemon green eyes inshi, murmushi ta sakar mai tareda fadin " Fauzi kasan health ina kuma kullum kara kusantar grave ina take I have fews days to leave this world so dan Allah kayi aure. " Maganganun Mami sun saya mai a rai Mami tamkar uwa take a wurin shi, yanzu yazama dole kenan yai accepting Amnah kenan a masayin matar sa tunda itace warda Mom kesan hada shi da ita. Da kyar ya iya bude Pink lips inshi yace " I will get married if that will make you happy. "

Wani irin farinciki ya ziyarci zuciyarta da alama plans inta zaiyi working " Allah yayi ma albarka my Fauzi, I have already chosen a girl for you. " Dum Dum haka yaji gabansa na faduwa oh shi Fauzi yazaiyi da Mami ta zaba mai mata kuma? Fuck after auren dolen da take son yi mashi yanzu kuma harda wani zaba mai mata da bai San ya take ba? Yamusa fuska yayi saikace wanda aka bawa kashi yaci koma wacece ita bazai taba sonta ba.

Kallonshi Mami tayi tace "Baka ce komai ba Fauzi. " Maido kallonshi yayi akanta tareda fadin "Do whatever you want Mami Good night ." tare da ficewa a dakin danshi  koda anyi mai auren to da auren da babu duk daya ne, danyayi alkawari ko kallo bata ishe shi ba ballanta ya hada shimfida da ita.

Da kallon Mami ta bishi zuciyarta fal da farinciki dama gobe birthday inta danhaka gobe zata hada su wato Mr Fauzi da Islam su fahimceni juna kafin tayi masu aure " Allah sarki Fauzi harda fushi dani danko good night peck baka yi mani ba. " tafada tare da jawo magazine inda take karantawa taci gaba da karantawa.

Harta fara karantun magazine ta tuno bata hada mai night coffee ba, mikewa tayi tare da jawo golden sandarta ta fito ta sauko daga bene ta nufi kitchen, coffee Machine ta nufa ta fara hada mai coofee bayan ta gama ta hada mai a tray tare da sa mai chocolate biscuits a dankaramin farin plate. Harta hayo bene ta tarar da Islam a kofar dakinta tana kokarin shiga " Gani nan Islam. " Islam ta juyo ta kalli Mami dake tahowa tare da tray a hannunta da sandarta a gudan hannun tana tafiya da kyar, da sauri taje ta karba tray in " Haba Mami mi yasa kikesan gajiyar da kanki bayan ga masu aiki a gidan. "

Smiling Mami tayi tace " zan iya yin komai akan Fauzi. "  Islam ta jinjina kai lallai taga soyayar Mr Fauzi a idanun Mami shagwabe fuska tayi " Am jealous Mami. " Murmushi Mami tayi tareda cire glass inda ke idanunta ta dafa kafadar Islam tace "Dan Allah kaima Fauzi dakinshi bacci nakeji. " Islam tace "To Mami sai da safe. " Mami ta bude kofar dakinta tare da fadin " Allah ya kaimu. "

Gabanta na faduwa haka ta tunkari kofar dakin shi, hannunta na rawa ta danna door bell shiru taji ba a bata izinin shiga ba kara danna door bell in tayi shima shiru, haka taita danna wa amma shiru kamar ba mutum a dakin. Tura kofar dakin tayi sai taji ta a bude, zura fararen santala santala kafafunta tayi, yau ma hasken dakin a kashe yake Sai bedside lamp dake kunne. Ajiye tray in tayi a center table na glass harta juya na nufin ta bar dakin sai ta tuno abunda tagani a can table in, a hankali kamar wata barauniya tadawo wurin table in, tabbas ba gamo tayi ba kwalbar wine tagani kuma alcoholic ce, bata san sanda tace "Inalillahi wa ina ilaihi raji'un ." da karfi, haske taga ya gewaye dakin, Mr fauzi zaune a kan gado ya jingina bayanshi da gado wata kwalbar Wine a hannun shi ba riga a jikin shi.

Zaro ido Islam ta fara yi ganin Mr Fauzi yana shan Wine alcoholic kuma ga Tattoo a kafadanshi na dama anyi mai zanen maciji da kunama , tunda take bata taba ganin Tattoo ido da ido ba saidai a jikin turawa a waya ko TV wannan wani bala'i ne? Zuba mata Lazy green eyes inshi yayi wacece ita kuma wannan da zata saya tana kallonshi "Ke get out of my room. " yafada da karfi yana nuna mata kofa, aiko da gudu ta fice zuciyarta ba dadi.






Washe Gari.

Yau sai kai da kowawa akeyi a Fauzi's Mansion dake maiduguri. Gardin in gidan akayi decorating warda shaharariyar mai decorating wato bluevelvetmarquee mai hoto kuma big studio dj kuma iamdjgabby mocktails kuma cocktailsinandout catering kuma simplyelegantparties sai drinks picadilly events sai Dessert kuma kayspastries duk daga Abuja suke .

Mai makeup kuma tuni Mami tasa an kawo mata Lbv makeup itama daga Abuja ta zane fuskar Islam.

Mami kuma tayi hakane dan ta fito da Islam yarda Mr fauzi zai yaba (Nikau nace Haba Mami kamar baki san Mr fauzi ba 😂) kai har Farha ba a barta a baya ba

Oops! This image does not follow our content guidelines. To continue publishing, please remove it or upload a different image.


Mami kuma tayi hakane dan ta fito da Islam yarda Mr fauzi zai yaba (Nikau nace Haba Mami kamar baki san Mr fauzi ba 😂) kai har Farha ba a barta a baya ba.

Itama Amnah tayi tata irin tasu slay queen .

Itama Amnah tayi tata irin tasu slay queen

Oops! This image does not follow our content guidelines. To continue publishing, please remove it or upload a different image.


To ku biyoni muji kwalliyar manya 🤓

Minister's Son Where stories live. Discover now