Chapter 3

1.2K 99 0
                                    

Yauwwa komai is ready? Mom take tambayar chef Halima. Eh Madam an gama komai. Inji chef Halima Sai ga wata Maid tazo tace Madam everything is ready.
  Good ! Yanzu duk kuje ku gyara jikinku inaso da ya zo yaga komai neat har ku. Cewar Mom tana gayama masu aikin dake wurin. Mom lafiya naga masu aiki sai kai da kawowa suke? Amnah ta tambaya tana saukowa daga bene.
Baza ki ji komai daga bakina ba it's a surprise for you and Muhsin , already nida Baban Muhsin musan mizai faru !! Mom tace tana farin ciki .

Oops Mom yanda naga mood naki sai farin ciki kike kamar an maki albishirin Aljanna to nasan bazai wuce maganar Bimbim ba okay let me guess hmmm he's coming back!!!

Yes dear my precious son is coming back I just can't wait to hug him tightly!!! Mom tafada harda kwallan farin ciki.

Aww don't cry Mom. Amnah tace tana share kwallan. OK Mom Bari naje nayi wanka I have to look gorgeous in the evening just for Bimbim.

Tam shikenan nima gani nan zuwa amma sai na tabbata komai yayi daidai kafin naje nai nawa.

Mom chill Mom common take a break! For goodness sake tun safe ina jin ki da masu aiki baki sake komawa bacci ba duk sai aiki kike ta sawa ana yi kema kije ki huta mana if Bimbim Was here bazai barki ki gaji haka ba dan haka muje kiyi wanka ki huta. Amnah tace tana jawo hannun Mom. Bayan Amnah takai Mom dakinta sai itama ta wuce nata dakin, tana shiga ta shiga toilet tai wanka sannan tafito da riga fara na towel , ta saya gaban mirror sannan da dauko hand dryer tana bushe kanta. Can someone tell me what's going on in this house? Muhsin ya tambaya yana shigowa dakin Amnah.

Well you should be used to it by now haba Bobo kamar dai bako. Cewar Amnah tana sharce gashinta.

What? Amnah just tell me and stop beating around the bush!

OK you mean to say you don't know what is going on here? The cooking, the decorations, Mom's mood blah blah blah huh?

Oh no what's on my mind that I didn't even notice? Bimbim is coming back yes that's it , Amnah Bari naje na shirya. Muhsin yace yana fita daga dakin.

Too bad for me banso ka gane ba we wanted to surprise you! Cewar Amnah ta ihu dan ya jita.

Dubai

 

         Mr Fauzi (Aslam, Bimbim)

Oops! This image does not follow our content guidelines. To continue publishing, please remove it or upload a different image.

         Mr Fauzi (Aslam, Bimbim)

   Saye yake yana kallon mutane yanda suke kai da kawowa sai yaji SA nashi yace the plane is ready sir. Bai ce dashi komai ba saidai kawai yafara tafiya sai securities suka take mai baya. Sai ga paparazzi da sauri securities nashi suka zagaye shi suna hana su amma gani kake flash sai aiki yake daga masu haukan shi hoto sai masu selfie da video danma securities dinshi na iya bakin kokarinsu. Ahaka har suka isa private jet nashi har ya shige basu bar daukan shiba.

Katsina
  Islam na dawowa gida kai saye dakin Eyah ta tafi. Zaune ta iske ta tana addu'a da alama sallah ta gama, bayan Eyah ta gama addu'ar ta juyo ta kalli Islam sannan tace yaya Mamana?

Eyah wata magana nazo da ita .

Minene fadi mana mamana.

Eyah taimako nake nema dan Allah Eyah.

Haba mamana ina jinki ai an zama daya.

Batun rashin lafiyar Farha ne, za'ayi mata operation dan haka ana bukatar kudi kuma masu dan yawa wurin dubu dari uku.

Subhananlahi cewar Eyah cikin tausayi.

Shine nace dan Allah Eyah in kina dasu ko basu kai haka ba kuma IN kinsan inda zan samu ko zaki samu nama .

Wai ni yanzu mamana kudin da ke gari ni bai kai haka ba ko wurin dan Eyah (dandanta) ma yau yazo yana neman bashi ballanta ince ko shi ya baku to shima duk kan'war ja ce.

Zamu biya daga baya in yaso wanda zai bada kudin In wata zai fida min na hada kudin na bashi. Eyah dan Allah kowa kika sani ki hadani dashi.

Eyah ta mike ta bude wani samira dake kasan gado sannan ta dauko leda a ciki sai ta bude ta mika ma Islam kudin. Gashi Mamana wannan kawai ya rage min Allah ya sani ba wadda nasani wanda zai iya baki wannan kudin, wannan dubu hamsin ce Allah ya kawo mafita kuma ni basai Kin maido Man ba ki dauka  a masayin gudummuwa ta Allah ya bata lafiya ya sa ayi a SA'a.

Ameen Eyah nagode sosai Allah ya bar zumunci.

Ameen mamana.

Tana fitowa ta iske su Ladingo zaune a kan tabarma suna cin gyada ita da maman Aisha sai taje wurin su dukda mugun kallon da Ladingo ke binta dashi. Sallamu alaikum ina wunin ku.

Mstwww da bamu wuni lafiya ba da Kin ganmu eyeh? Ladingo tafada tare da zabga mata uwar harara.

Haba Ladingo miye na bata rai haka? Wallaikumul salaam yata ya kike ya jikin Farha? Cewar Maman Aisha .

Lafiya lau jiki kuma da sauki. Islam ta amsa mata.

Toh Allah ya kara sauki anjima insha Allah zan shigo. Inji maman Aisha.

Allah ya kaimu dama nace operation din da za'ayi ma Farha yana bukatan kudi har dubu dari uku shine nazo dan Allah ko bashi in zan samu ko basu kai haka dan Allah a taimaka zanyi kokari na biya ku.

Tabb wane asaranren zai baku bashi nan ko abinda zaku ci ya kukeyi ballanta har a baku bashin dubu dari uku ai sai wanda bai san abinda yake ba, Fara take ko wa yauwa Farha wai ita bata mutuwa ko kun huta?tabb!!! Ladingo tafada tana kunfar baki saboda bala'i.

A'a Ladingo ita rayuwa ba'a haka shi mutum ba a wulakantashi, in kinsan bazaki basu ba sai kice baki da shi ko wani abu zaki da kudin amma ba'a haka. Ke kuma Islam dan saya bari naga abinda zan iya yi. Maman Aisha tace sannan ta mike ta shiga dakinta.

Tabb!!! Shegiya yanzu haka karya kike Yi dan kawai ki amsa kudin mutane ki gaki barauniya shiyasa saboda bakin hali har yau Kin kasa aure to ko kince zaki aure wa ke so? Mtsww a haka za'a kare dai!!! Cewar Ladingo tare da daukar gyada tana ci. Itadai Islam tayi mata shiru kasancewar ta Mace ce mai gudun fitina.

Islam saidai hakuri ni dubu talatin ya rage man har buga ma Baban Aisha nai inga ko Za'a samu shine yace shi dubu ishirin ke gareshi ni kuma inada goma kinga talatin kenan yace kuma kiyi hakuri bai da shi da ya baki amma shi ba sai Kin maido mai ba ki karba a masayin gudummuwar shi kuma nima haka Allah ya bata Lafiya ya sa ayi a SA'a sai mun shigo anjima . Maman Aisha tafada tana fitowa daga daki tare da mika ma Islam kudin.

Nagode kice ma Baban Aisha mun gode Allah yabar zumunci. Cewar Islam tana tashi daga zaune domin tafiya.

Ameen Islam.

Islam na fitowa sai ta dinga tafiya kafin takai bakin titi don samun napep kawai sai ta afka duniyar tunani yanzu ita ya zata yi? Oh ni duniya Allah ya kawo mana sauki. Yanzu ko Sun hada nasu kudin bai wuce a samu dubu hamsin ba In kuma sunce su saida Furniture dinsu still kudin bazai kai dubu dari uku ba . Yanzu miye mafita ina  zamu samu wannan kudi? Kuma in bamu samu baza suyi mata operation dinba sanadiyar haka Farha na iya mutuwa. Sai kawai kwalla ya zubo daga idonta no no insha Allah we won't lose Farha, I have to get this money I have to , Abbi ya tafi ya barmu yanzu kuma Farha? No Islam kibar wannan tunanin zuciyarta ta fada mata. Bata ankara ba sai taji horn na mashin dasauri ta dago ta share hawayenta sannan ta fara kokarin ba mai mashin din hakuri.

Ya hakuri malam.

Ke dalla gafara inda yanzu na banke kifa sai ace laifi nane amma kina wani tafiya kina tunani sai hawaye kike zubar wa in duniya tai maki zafi kije ki nemi mafita mana !!! Mai mashin din yace tare da tada mashin dinshi ya fice.

Ki kwantar da hankalinki Islam Allah na tare da bawansa. Zuciyarta take fada sai kawai ta karbi shawarar zuciyarta ta cikaba da tafiya har ta iso bakin titi.  Prado ce a sakiyan jibs din da alamu convoy ne sai taga Sun parka gabanta,  hankalin mutane kowa ya koma a kanta da motocin. Islam kuwa ji tayi gabanta na faduwa.

Long chappy huh?
Hurairaytu🍸🍸🍸🍸🍹🍹🍹

Minister's Son Where stories live. Discover now