Chapter 23

838 101 18
                                    

Dear readers,

Nayi mistake Islam ba secretary in Mr Fauzi bace, personal assistant inshi ce.

"I said pick it up dummy " ta daka mata sawa. Islam kau ji tayi inama ace zata iya wanka ma Lala mari , kallon Card inta dake Kasa tayi sannan ta Kalli Lala dake mata kallon raini, murmushi kawai tayi sannan ta dauki cartinta. Lala tace "Follow me ."

Lala na gaba islam na bayan ta, cak taga sun saya gaban wani glass door, gani tayi Lala tasa hannunta a jikin kofar sannan kofar ta bude. Wato itadai Lala tana da access to duk wani password na office innan lallai Mr fauzi na ji da ita kodai budurwarshi ce? Islam concentrate my subconscious mind told me.

Budewar Glass door in saida ya kusan sa Islam sumewa, tunda take bata taba ganin hadeden office kamar wanan ba dazu ma gurin nan inda Lala ta hanata shiga shine first door in office in, inda personal assistant inshi ke zama amma ita saboda Mami tasa ayi mata office inta daban shiyasa bazata zauna nan ba, inda glass door innan ya bude shine office in oga . "Masha Allah " ta furta a hankali komai fari ne gaskiya mai safta ne kawai ke iya zama gurinan. Zaune yake kan kujerar shi ta CEO yana anfani da MacBook kamar ma typing yake, shikuma Habeeb yana duba wasu takardu ya tatara duka hankalinshi yaba ma takardun mahinmanci.

Sky blue suit in dake jikin Mr fauzi ba karamin kyau yayi mai ba, kamar ka sace shi ga gashin kan shi Masha Allah yasha gyara, medicated Glass in dake idanuwanshi ba karamin kyau yayi mai ba, ashe dama yana anfani da Medicated glass? Lala ce taje bayanshi tare da daura hannuwanta kan kafadarshi tana mai tausa tace " Baby your new PA is here. " shi sam baisan da shigowarsu ba saidai jin tausar da Lala ke mai, dan shi hankalinshi na kan typing in da yake.

Dago kanshi yayi ya kalli Islam dake saye a gabanshi kamar gunki yace " CV . " bude jikarta tayi ta ciro CV in ta ajiye a kan table in gabanshi, yi yayi kamar bazai dauka ba can kuma yasa hannu ya dauka. Wurgo mata CV in yayi bayan ya gama gani sannan yace " I want you to book an appointment for me with Mr Dangote. " kallon shi tayi sannan tace " Okay Sir " sannan ta juya ta fice ta wuce office inta. Lala ta bita da kallon sana itadai batasan mai yasa ba taji batason Islam dukda bata da wani enemy daya wuce Amnah Fauzi amma tanajin tafi sanar Islam akan Amnah . Lala tace " Baby I don't know why but I have a Bad feeling about this girl. " Banza yayi da ita ya cigaba da typing shikuma Habeeb kamar baya cikin office in saboda hankalinshi nakan takardun dake gabanshi, itadai Lala inda sabo ta saba.

Islam na shiga office inta ta kira Adeel bada dadewa ba saiga shi yazo, yana zuwa ta gaya mai abunda Mr fauzi yasata. Nuna mata komai yayi sannan ya tafi. Shikuwa Mr fauzi yana gama typing ya mike ya shiga dakin dake cikin office insa. Yana shiga Lala nabinshi a baya wanda shi baisan tana biye dashi ba, kokarin cire suit inshi yashiga yi Sai kawai yaga Lala na kokarin tayashi . Hannunshi yasa ya cire hannunta daga jikin rigarshi yace " out!!! " tace " Please Baby allow me to...... " ai bai jira ta karasa ba yace " out I said otherwise I will deal the hell out of you. " Da sauri ta fita tana hawaye inda sabo yakamata ace ta saba amma ina.

Habeeb da ya gama aiki kan takardun ya dago yaga Lala ta fito daga dakin Mr fauzi tana kuka, murmushi yayi ya girgiza Kai dan yasan halin abokin nashi ya Mike ya shiga dakin. Yana shiga yaga ba kowa sai yaji karar zubar ruwa hakan ya nuna yana Bathroom, zama yayi ya zaro wayarshi ya shiga Snap chat yana kallon story in mutane. Mr fauzi kuwa yana gama wanka acikin toilet in akwai changing room yashiga ya canza kaya zuwa white T-shirt da aka rubuta " Fauzi " da bakin rubutu sai Milk jeans, fararen snickers ya zaro yasa ma kafuwanshi sai iWatch daya daura a hannunshi na dama sai zobe yana fitowa ya Kalli Habeeb yace " Buddy am going to Habil cafe wanna join ? Yana sa ma kunnenshi apple airpod .

Habeeb ya Mike yace " let's go. " Suna fitowa kallon ya koma kansu, staffs in duk suka sha jinin jikinsu. Adeel already yana cikin mota yana jiransu, zaro bindigar dake acikin suit inshi yayi yasa bullet ya maida cikin rigarshi . Suna fitowa suka fada cikin G wagon, Mr fauzi ya zauna gaba Habeeb ya zauna baya Adeel kuma ya tada mota suka fice. Ba tare da bodyguards suka tafi.

Sosai yake zabga bala'i a sakar gidan,waishi dole sai an fada mai Ina Islam take . Eya tace" in na fada ma binta zaka yi?" Sauke ajiyar zuciya yayi sannan yazo gabanta ya sugunna yace"Eya kinsan ina matukar son Islam da gudu zan bita inda Suka tafi na maido ta nan muyi aurenmu." Ladingo ta kalli Talatu tace"Tirrr da kuwa kayi asara Mansir." Shikuwa banza yayi musu ya cigaba da rokon Eya inda su Islam suke.
Eya da taga ya takura mata tace" Suna Maiduguri gidan Kakarsu "

" Adreshi fa ? "

" Da kace gidan Fauzi kowa yasan gidan." Wani farinciki yaji,godiya sosai yayiwa Eya sannan ya fice. Eya kuwa dole take fada mai saboda tasan halin Mansir Sarai ba mutumci ke gareshi ba yanzu ya tada fitina in bata Gaya Mai ba .

Habil Cafe

Mariam na ganinshi ta tashi ta rumgumo shi tana fadin"Af where have you been?" Shima hugging inta yayi danko yayi missing in friend inshi yace" I missed you." Breaking hug in yayi sannan ta rumgume Habeeb ,duk zama sukayi sannan tace ma Habeeb"Aishi Habeeb ko jiya mun hadu dashi amma kai Af ka boye." Kallonta yayi yace" I was busy , so how's your husband?" Smiling tayi sannan tace"He's good how about you? Kar kace man you ain't dating any girl." Shiru yayi mata kawai saima bude bottle in wine dake gabanshi da yayi ya zuba a cup ya Fara sipping , Habeeb yace " He isn't dating anyone, munyi munyi har mun gaji talk some sense into his head ,excuse me ." Ya mike yabar wurin ya danna ma Jidds kira ta waya. Mariam ta maido kallonta kan Mr Fauzi Wanda Shan wine inshi yake hankali kwance saikuma Waka da yake ji a airpod in dake kunenshi. Shikuwa Adeel yana chan wurin buga game yana game da wasu . Hannunta ta hauda kan nashi tace" listen to me please ." Kase wakan yayi ya cire airpod in yace " Inajinki ."

"Af I would like to advise you ka bude heart inka , ka Fara soyaya....." Ai bata Ida ba ya kaseta" Enough! Say no more !!! Karki Kara kawo wannan topic in understand?"

"Yes." Tace tasan dama za'ayi haka . Can Kuma tace " Ina Muhsin it's been awhile "
" Yana Maiduguri." Haka taita janshi da fira .

Itakuwa Islam tayi mai booking appointment , number in telephone in office inshi ta danna a nata telephone in , kiranshi ta shiga yi amma bai daga ba . Kawai sai ta yanke hukuncin taje ta same shi a office inshi . Tana zuwa tasa pin in da Adeel ya bata , tana shiga taji shiru , tunkarar second door in tayi Shima tasa pin ta shiga , sai gani tayi baya nan , juyawa tai da niyyar ficewa sai taga Amnah Fauzi saye da alamu shigowarta kenen ,cikin Riga handless black mai kallikalli fitted sai ji'ka mai hannun chain rataye a kafadarta , takalmin kafafuwanta black high heels ne , gashin kanta Kuma curly hair style . Kallon Islam takeyi daga sama har kasa irin kallon rainin nan sannan tace " Who are you ? And what are you looking for?ko sata kika zo yi ." Gaban Islam ya fadi karfa ta kulla mata sata tace " No Ma'am am looking for Mr Fauzi I'm his new PA ." Kara kallon raini Amnah tayi mata saita juya taje wurin telephone ta danna wata number ta kira , ana dauka sai tace " Come here now !!" Islam juyawa tayi zata fita saiji tayi tace " Ke Ina zaki ?"

" Zan koma office Ina."

" Dawo ki saya saina ce ki tafi !!! Islam ta dawo ta saya kamar yarda Amnah ta umarce ta . Amnah ta zauna tare da daura kafa daya kan daya , karar door bell suka ji Amnah tace "Come in " saiga security ya shigo , Amnah tace " Inspect her I think she stole something." Da sauri Islam take ja da baya tana girgiza Kai ganin security in ya nufo ta .

" What the fucking hell is going on here !!!" Suka ji muryar oga , ai cak security in ya saya wuri daya daga bin Islam da yake yace "Sir Ma'am called me and order me to inspect this woman ." Mr Fauzi ya kalli Amnah , Amnah ta taso tazo gaban Mr Fauzi tashiga yi mai shagwaba da kulla ma Islam shairi " Baby na shigo naganta itakadai a nan so I got suspicious of her , tayi kama da barauniya , for how long have you known her ?" Wani kallo yayi ma Islam har ta sorata ta sha jinin jikinta .

Kuyi hakuri .
Ina da tambaya ,
Wai da Lala da Amnah wace tafi wulakanta Islam Kuma wace tafi baku haushi ?
Wayyo Islam baiwar Allah In kece akayi wa haka on your first day wurin aiki zaki sake komawa 😪?ko da yake ai neman kudi ne .

Minister's Son Where stories live. Discover now