Chapter 19

816 95 27
                                    

Mom wurin kalle kalle ta hango Mami na shirin kai Islam wurin su Fauzi, kallon Dad tayi dake magana da abokan shi "Excuse me. " tafada tare da yin sauri da sha gaban Mami.

" Mami Mrs Jones naso tayi maki magana ." tafada tare da nuna inda Mrs Jones take. Mami tace " okay ganinan zuwa jeki ina abu. " kallon Islam Mom tayi sai ta kalli Mami "  Mami she's waiting for you. "

" Nace naji can't you wait for some minutes haba. " Mami tafada cikin fada fada tare da kara matse hannun Islam gam a hannunta. Dad ne yazo wurin yace " Mami zan dan areki akwai mutanen dake san magana dake . " yafada yana jawo hannunta, sakin hannun Islam tayi ta bishi.

Mom ta Kalli Islam tace mata "kekuma bazaki wuce kibar wurin nan ba ko sai na wulakantaki. " tafada cikin halin disga mutum.  Islam kau da batasan mata ba jikin ta yayi sanyi juyawa tayi jiki ba kwari tabar wurin gaba daya ta tafi kitchen inda su Ummi suke bawai saboda tana soron matar tabar wurin ba saboda Mami dan kamar taga suna da dangantaka.

11:19pm

Kallon Farha tayi sai bacci take hankalinta kwance itama haka Ummi amma ita sam batajin bacci, mikewa tayi ta samu kujera ta zauna sai ta fara recalling abinda ya faru to wai wacece wannan matar kuma yarda tayi mata magana cike da sa'na kila kuma haka halinta yake.

Turo kofar library yayi tare da zura fararen kafuwan shi ,cikin daren nan ji yayi karatu yakeson yi  . Sam ya rasa miyasa yaji kamar zai hadu da wani abu wanda zai sosa mai rai, Bookshelf ya nufa ya fara duba Books in dake wurin.  " Electric impulse " shine book in daya zaro. Zama yayi ya bude litafin , zai fara karantawa kenan idanuwanshi suka hango wani Golden Box a saman table in da aka aje newspapers , mikewa yayi yaje wurin table in tare da kai hannu ya dauki Box in.

Ku'ra yaga Box in yayi har ma ya bata mai hannu, da alamu Box in ya dade a aje. kokarin budewa yayi sai yaga sai an saka Key dan a kulle Box in yake. "  where's the Key ." yafada yana kalle kalle ko zaiga Key in , shidai harga Allah Box in ya burge shi baisan miyasa ba yakeson yaga miye a ciki.

Amnah ce ta fito daga dakin ta cikin rigar bacci fara mara hannun ta saya mata iya cinya, dukiyar fulaninta duk a baiyane. Dakin Mr fauzi ta nufa tare da knocking, saida tai knocking sau ba adadi sai kawai ta yanke shawarar ta shiga kawai tunda dama haka Mr fauzi yake Sai mutum yai ta knocking kuma yana ji yaki amsa ka. Shiga tayi ta tarar da ba kowa, fitowa tayi Sai taji mosi a library, da sauri ta nufa wurin tare da tura kofar ta shiga kai saye tana rokon Allah yasa Mr fauzi ne a ciki.

Saye ta ganshi gaban wani table ya bata baya kamar wani abu ke hannunshi, numfashi ta sauke Allah ya amsa addu'ar ta Mr fauzi ne. Masha Allah ta furta a cikin zuciyar ta tabbas Mr fauzi cikaken namiji ne dole mata suyi ta binshi danma baya biye masu da tuni yayi wuf da su,  cikin fararen pyjamas  as always cikin fararen kaya, gashin kanshi yasha gyara kamar kan balarabe sai iWatch dake daure a hannunshi. Cike da yanga tana ranguada jiki ta karaso ta hauda hannun ta a kan kafadarsa.

Mr fauzi dake saye yana nazari to ina zai gano Key din yaji an dafa shi , kamshin humra take sai tashi yake. Gashi kamshin turaren shi ya hade dana humra inta sai ya bada wani kamshi mai masifar dadi, Cike da yanga ta soma yi mai magana tana shafa kafadarshi " Baby what are you doing at this hour of the night ?" hannunshi yasa ya cire hannuwanta a jikinshi " Amnah I wanna be alone ."

Bata ji dadi daya fada mata haka ko dayake haka halin sa yake " okay goodnight. " tafada tare dayi mai peck a kumatu. Yana ganin ta fita ya juya yana kallon Box in can kuma ya cigaba da duba Key in .

Dad ne zaune a parlo shi kadai cikin duhu light a kashe ba Wanda zai ce da mutum a parlon . Abunda yasa Dad wannan zama cikin duhu ba komi bane face damuwa ,fuskar macen dabazai taba iya mantawa da ita ba ke mai yawo a idanuwanshi , macen da ya aikata abunda ba wanda ya taba tunanin zai aikata akan ta, macen da zai iya komai akanta to top it all macen da ita ce first and last Love inshi wato Afrah. Shi yanzu itakadai yake so ya kasance tare da sai kuma jininshi wato Aslam da Muhsin. Shi yanzu so yake Mom ta fita daga rayuwarsa, tasa shi ya aikata abubuwan da basu dace ba dalilinta ya aikata abunda koshi baya iya yafe ma kansa tabbas Mom ba mutuniyar kirki bace , tashigo rayuwarsa ta ida jagula mai komai " to heck with her. " yafada cike da haushinta yana tusa hannuwanshi cikin gashin kanshi irin na larabawa , yana fida numfashi cike da takaicin biyewar da yayi ma Sarah . "Karma is a bitch."


Wani sohon akwati yahango kusa da Book shelf, zuwa yayi ya sugunna gaban akwatin, hannu yakai zai bude akwatin Sai kuma ya fasa saboda akwatin yayi ku'ra da alamu ya dade a aje kuma ba'a kula da shi, "to mai yasa" ya tambayi kanshi . Hannunshi ya zura cikin farin aljihun sweatpants inshi ya zaro farin hanky ya daura a hannunshi yadda ku'ran bazai taba mai hannu ba ya bude akwatin.

Gabanshi ne ya fara faduwa sai kuma kirjinsa daya fara mai ciwo, Books da hotuna sai kuma hoton papers irin na siyasa wanda ake likawa a bango ya gani, ba abunda yafi tada Mai hankali kamar hotunan mutumin daya gani.

Daukar hoton paper yayi guda daya ya fara karantawa bakin shi na rawa " Vote for Khalifa Fauzi for senator..... " kasa ida karantawa yayi saboda zafin da kirjinshi ke yi masa, dafe saitin kirjinsa yayi .Tabbas wannan ko ba a fada masa ba Twin brother in Dad ne saboda fuskar su iri daya da manyantan banbancin su shine dimple shi Wannan mutumin daya gani Mai suna Khalifa yana da dimple Dad kuma bashi dashi  .

Bai san mike faruwa dashi ba kokuma abunda zai faru dashi shidai ya sinci kanshi da wani irin masifafen son Khalifa , yes ko ma yace yafi san twin brother in Dad fiye da kowa kuma da komai. Hannun yasake kaiwa ya dauki hoton Khalifa, shafa fuskan Khalifa yashiga Yi to mi yasa yaji all of a sudden yana masifar San Khalifa kuma miyasa su Mami da Dad suka boyemai Khalifa?  What's  happening to his family?  "Everything about this family is now mysterious, who's this mystery man? " yafada wasu hawaye masu zafi na zubo mai, rabon da yayi kuka a rayuwarsa har ya manta is hardly kaga yayi kuka .

Assalamu alaikum,

How are you all?

Good insha Allah.

Ya lock down May the Almighty Allah guide us from this deadly Viruse , Ameen ya Allah.

Ramadan Kareem to y'all May Allah accept our ibadah may he forgive our sins and may he continue to protect us from all evils,

A sha ruwa lafiya.

Hurairaytu 🍸🍸🍸🍸🍸🍸🍹🍹🍹


Minister's Son Where stories live. Discover now