Chapter 22

1K 104 28
                                    

Kallon Mami take dake mata magana hawaye na bin fuskar ta, Mami itama kukan take ta sake rike hannun Islam gam " ki yafemani Islam....." Da sauri Islam ta daura yasanta kan bakin Mami " Shhhh Mami say no more ni bakiyi mani wani laifi ba kuma bansan mi ya faru sakanin ki da Ummi da Abby ba amma ni nasan bakiyi mani wani laifi ba. " Girgiza kanta Mami ta shiga yi ma Islam tana so ta fadi abu amma kuka yafi karfinta, hannu Islam ta daura a bayan Mami tana lallashin ta itama hawayen take. Da kyar Mami ta iya magana " Ban baku hakkinku ba kuma na kasance ba kaka ta gari ba na fifita yayan Khalid fiye daku alhalin duk daya kuke a gurina na hada kai da Sarah wurin musguna ma Afrah sannan kuma na cuci Khalifa da'na kuma shine wanda yafi mutuntani da sona fiye da Khalid amma dayake ni am a bad mother I end up hurting him....." Kuka yaci karfinta .

Allah sarki Islam wani daci taji a cikin zuciyarta kenan Abby shine wanda yafi son Mami da kula da ita da yi mata duk wani abu da da na gari zaiyi amma shine ta yaudareshi daga karshe wayyo Abby inta mutumin kirki tasan kafin ya mutu ya mutu da bakin ciki haba abun da ciwo, share hawayenta tayi ta kalli Mami dake ta kuka " Mami I'm dissapointed frankly speaking how can you do this to your son your very own blood? "

" ni yanzu haushin kaina nake ina dana sanin zama uwar Khalifa be cancanceni ba da wani ido zan kalli Afrah in nemi yafiyarta. "

" we are made to make mistake, zaki iya neman yafiyarta. "

" What about Khalifa? How can I ask for his forgiveness? "

" Abby is a good person am sure he already forgave you before he passed away ."

Kallon glass in motar Mami tayi sannan ta Kalli Islam tace " kije yanzu ba da dadewa jirginku zai tashi. " hanky ta zaro a jirkarta ta goge hawaye , kallon Farha tayi dake zaune a gaban motar tayi shiru ta kulle idanuwanta hawaye nabin fuskar ta, ta sani sarai kuka take saboda maganganun Mami da taji tasan Abby take ma kuka.

Dafa kafarta tayi " Farha zan tafi take care of yourself and Ummi harda Mami kinji? " Girgiza kanta Farha tayi alamun to sannan suka rumgume juna. Cike da so, kauna, shakuwa sukayi breaking hug in. Bude motar tayi ta fita driver ya rakata cikin airport in da akwatin ta sannan ya dawo ya tada mota suka fice.

Abuja, Nigeria.

Zaune take cikin BMW a gaban motar Muktar , Muktar yana daya daga cikin manyan yaran Mami, shi umarni ne yake bi Mami ta bashi hidimar daukar Islam a airport da kaita masaukinta da duk wani hidima .

Brain and Hammers

Shine sunan estate in da zata zauna, kallon apartment inta tayi Masha Allah so breathtaking gaskiya Mami tayi kokari. Muktar ya kalleta yace " If you need anything don't hesitate to call me. " Murmushi tayi mai " Okay I will, thank you. "

" You're welcome. " yana gama fadar haka ya fice.

Shiga tayi cikin daki ta cire kayan jikinta ta shiga Bathroom ta sakar ma kanta shower. Bayan ta fito ta bude handbag inta ta zaro wayarta tasan Farha ta kira , tana duba wa taga ta kira sau biyar sai na Ummi sau uku, zama tayi ta fara kiran Ummi sannan Farha.

Yaune ranar farko da zata fara zuwa office , saye take gaban Mirror ta gama sa black suit sai tayi rolling in bakin gyale , Sidebag ta dauko mai hannun chain Red Sai Cover shoes inta Red 😍😍 ( Readers Islam fa tayi kyau batason raini ne) zaro car Key tayi warda Mami ta siya mata yau tun safe Muktar yasa aka kawo mata. Car inta kirar Mercedes Benz jib .

A parking lot tayi parking, tana fitowa sai taga wata Orange Lamborghini ta taho a guje, birki wanda ke tuka motar yayi, cike da masifa ta fito itakau Islam kallon motar ta saya yi dan da alamu wanda ke tuka Lamborghini in nan so yayi ya banke ta ko kuma ya bugar mata mota . Fararen kafuwanta dake cikin high heels Pink suka fido kansu daga cikin motar, rigar dake jikinta iya cinya ta saya sai gashin kanta Wavy brown hair , hannunta sanye da agogon Gucci sai zoben gold dake a hannunta, cikin isa ta tako har gaban Islam sannan tace " How dare you park your car at my parking spot. " Cike da Mamaki Islam ta kalleta ita kuma wannan wacece inka na da rai kaga mutane iri iri, Islam tace " Excuse me are you talking to me ."

Wani haushi ya kama Lala anya wannan yarinyar tasan wacece ita? Itafa ce Lala Thomas warda take competition da Amnah Fauzi akan Mr fauzi, sannan babanta shine Vice president na kasar Morocco da alamu wannan Middle Class girl innan batasan ko ita wacece ba. Lala cikin bala'i tace " hey don't you dare act smart. "

Murmushi Islam tayi sannan ta shiga kallon inda tayi parking motar ta tace " I can't find your name. " Ai dagowar da Islam zatayi sai taji saukar mari tasss . Islam ta dafe inda Lala ta mareta tana fadin " How dare you! "

Lala ta daka mata sa'wa " Shut up idiot and move your car to another spot. " Islam kau abinda yasa bata rama marin ba saboda bata son rigima kuma yaune ranar ta na farko kar ace daga zuwanta harta fara fada kuma bata san masayin yarinyar nan ba da alama ita din babban masayi gareta a nan maybe zata iya sawa a koreta daga aiki kuma in Mami taji she will be disappointed .

Shiga mota Islam tayi ta Parker wani spot in , sannan ta fito ta nufi hanyar building in.

Fauzi Company

Tundaga wurin shiga Identity Card inta ya fara amfani . Building in yakai Hawa 35 , Number in Adeel ta shiga nema Mami ta turo mata tace ta kirashi in tazo. Itadai Islam duk a takure take , mutanen wurin kuma kowa sai harkar shi suke. "Hello Miss Islam. " taji muryar Adeel acikin dodon kunnenta , " Good Morning gani nan a First floor. "

" to ki taho 25 floor sai ki kira ni. "

" Okay tam. " tace tareda ending call in, wurin elevator ta nufa tareda shiga.

Tana isowa 25 floor ta danna mai kira, shikuma yana ganin Call inta ya fito daga office in dayake, yana fitowa ya hango ta ta manna waya a kunne tana kiranshi, karasowa yayi gabanta " karki dameni da kira. " yace cikin zolaya itama murmushi kawai tayi sai ta kashe kiran. Adeel yace " Muje ko. "

The CEO'S Personal assistant.

Shine sunan da ta gani a gaban Office in da suka shiga , Adeel yace " Miss Islam hope you like your office. " kada mai kai tayi sannan tace " Wow it's so beautiful thank you. "

Adeel yace " I think I should get going in case you need help I'm a phone call away. " harya tafi sannan ya tuno da wani abu ya juyo yace "saikinyi hakuri da ogan namu zai baki attitude Sosai ." yana gama fadar haka ya fice.

Kallon office in ta shiga yi ko a mafalki bata taba sammanin zata zauna acikin irin office innan ba talk less of ace Nata ne. Wayar ta ta dauka ta kira Farha ta Face Time. Nan ta shiga nuna ma Farha office inta , Bayan ta gama Face Time da Farha tai deciding zuwa office in Mr fauzi dantai introducing kanta kuma Maybe yana da aikin da zai sakata. Tana fitowa taga ansa CEO's Office a jikin kofar dake kallon nata office in. Door bell in tazo dannawa sai taga yarinyar nan ta dazu tazo ta danna password kofar ta bude ta shiga, itama da sauri ta bita zata shiga kenan yarinyar ta juyo ta tare mata hanyar shiga tana fadin " Where the hell are you going? Don't tell me you're coming in !!"

Islam kau acikin zuciyarta cewa tayi Ni Islam na shiga uku badai wata jarabawar ba kuma? Habeeb cikin Black suit ne yazo shiga yaga abinda ke faruwa yace " Lala what's happening here ." Lala tace " she wants to come In and I won't allow her who's she to come in. "

Habeeb yai Murmushi yace " Lala it's too early for you to start looking for trouble. " yana gama fadar haka Lala ta masa mai ya wuce ciki . Islam ta zaro cartin ta tace " Take a look I'm the CEO's New personal assistant ." Yamusa fuskarta Lala tayi sannan ta bude handbag inta ta zaro hand gloves tasa sannan ta karbi cartin Islam tana gama karantawa ta Saki cartin ya fadi kasa ta Kalli Islam tace " Bend down and pick it up. " cike da mamaki Islam ta saya tana kallonta ina ma ace zata iya wanka mata mari. Lala ce ta daka mata sa'wa " I said pick it up dummy. "

Hurairaytu 🍸🍸🍸

Minister's Son Where stories live. Discover now