chapter 1

739 16 1
                                    

💫💫💫💫
          _*MEE'AD*_
                   💫💫💫💫
*PERFECT WRITERS' ASSOCIATION*🌞

( WE AIN'T PERFECT BUT WE'RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS 💪)

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P.W.A✍️

*THE BOOK IS WRITTEN*

*BY*

*_HAUWA IBRAHIM MISAU_*

Wattpad__@hauwancyy44

_____GODIYA

Dukkan yabo da godiya su tabbaga  Allah madaukakin sarki mai kowa mai komai daya bani ikon rubuta wannan littafi tsira da Aminci su kara tabbata ga fiyayyen halitta Annabi Muhammad S, A, W.

 
        JINJINA & SADAUKARWA

Na jinjina na kuma sadaukar da wannan littafin na gareki babbar aunty SAFNA ALIYU JAWABI Allah ya kara daukaka, basira da kuma fasaha ya kuma kareki da sharrin dukkan mai sharri. Ameeen .

*Page* 1️⃣

______Zaune take bisa kan kujera a falo hannun ta rike da cup da alama tea take sha. sanye take cikin wata doguwar riga mara nauyi mai launin ruwan ganye.

fiskarta ɗauke da murmushi wayace rike a hannunta kirar infinix hot 10  tana dannawa da alamun chat take yi, fuskarta sai fitar da wani kyakkyawan murmushi yake kallo ɗaya zaka mata ka fahimci tana jin daɗin chatting ɗin da take sosai.

Batayi auni ba taji an ɗaka mata duka ta baya, a hansale ta juyo kasancewa abin sa tafi tsana kenan a rayuwarta.

" Ke wai mike damun kine ?" kin girma, amma kin kasa gane hakan, to bana son irin wannan wasar dan haka karki ƙara "

Cike da mamaki Amal ta taɓe fuska  tace" *MEE'AD* ba'a taɓa yi miki abin arziki wallahi kullum sai kin gwale mutane, karki mance na girme miki nisa ba kusa ba, dan haka zancan girma ma ki aje shi gefe sai kace ban girme miki ba," ta

Kawar da fuska gefe tayi gefe dan kuwa  kamar zatayi kuka take ji tace" Ni dai kawai wasar ne bana so dan Allah ki daina, kinji Yayata?"

Murmushi Amal tayi tace" Albishirin ki"

" Goro fari tas"

"Gidan su Amrah zamu tafi yanzu"

"Tsalle tayi cikin zumuɗi tace "Dan Allah?"

"Wallàhi kuwa  Hajiya zamu karɓowa saƙo"
mu"
"Kai wallahi naji daɗi bara na nayi wanka"

"To sarauniyar azarɓaɓi ba yau bane ba sai gobe"

Taɓe fuska tayi tace"Kai amma banji daɗi ba, wallàhi na ɗauka yau zamu tafi"

"Idan da rai ai gobe zata zo, amma wai drive ne zai kai mu"

"Kash Kinji Hajiya da wani irin magana kuma ko?"

"Rigimar ki da yawa take, to ƙwantar da hankalinki da kaina zan kai mu in sha Allah"

" Gaskiya naji daɗin hakan kinga bari naje na kwanta, dan so nake na tashi da wuri"

da wuri dan na tashi da wuri muji dadin

Rike da hannun juna suka shige cikin suna masu farin cikin gobe zasu ga Amrah......

MEE'ADWhere stories live. Discover now