Chapter 22

78 2 0
                                    


💫💫💫💫
_*MEE'AD*_
💫💫💫💫

***CONTINUE***

*PERFECT WRITERS' ASSOCIATION*🌞

( WE AIN'T PERFECT BUT WE'RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS 💪)

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P.W.A✍️

*THE BOOK IS WRITTEN*

*BY*

*_HAUWA IBRAHIM MISAU_*

Follow me on wattpad
👇👇👇
@hauwancyy44

JINJINA & SADAUKARWA

Na jinjina na kuma sadaukar da wannan littafin na gareki babbar aunty SAFNA ALIYU JAWABI Allah ya kara daukaka, basira da kuma fasaha ya kuma kareki da sharrin dukkan mai sharri. Ameeen .

√√√√√ MEE'AD fan's kuyi hakuri da rashin post akan time, sbd wasu dalilai. √√√√√√



**** Pls don't forget to vote, share & comments 👌 love u fan's 💯%.

39 ~ 40


Tin asuba data tashi bata koma bacci ba kasancewar yau zataje gidan kakarta Hajiya Hindu sbd jin gidan tayi ya mata zafi sosai, kai tsaye kitchen ta nufa dan karban break fast dinta.

Karfe tara da rabi ta gama shiryawa tsaf cikin riga da siket na' atamfa, tayi kyau sosai sai kamshi take zubawa, gyale ta yafa kafin ta fita waje.

Da sallama ta bude kofar falon Mommy hangota tayi kan sallaya da 'alamar ta idar da sallah.

Shafa 'addu'an tayi sannan ta juyo fuskarta dauke da murmushi Mee'ad kin fiye rigima, na rasa mi zakije kiyi a gidan Hajiya harna tsawon kwana uku, idan ba rigima ba mi hakan yake nufi ?"

Shagwabe fuska Mee'ad tayi Mommy nafiso naje gidan Hajiya na hutane sbd bajin dadin zama ni d'aya 'a gidan nan nakeyi ba!

Dafata Mommy tayi kinga kwantar da hankalinki bani nakar zomon ba, tashi kije Allah ya kiyaye hanya.

Murmushi tayi tace na gode Mommy na bye, Kofar fita ta nufa.

Bin bayanta da kallo tayi fuskarta dauke da murmushi Allah ya shirya min ke kawai tace.

Bata tarar da kowa 'a babban falon gidan ba, kofar fita daga falon ta bude ta nufi harabar gidan.

Sannu Baba ina kwana ya tsufa kuma ? Alhmdlh yayasu Hajiya ?
Lfynsu klau sunce na gaisheka ma, washe baki Baba mai gadi yayi kafin yace na gode sosai.

"Yauwa Baba ina Malam Idi yake yana kwance, amma bari nayo kiranshi.

Bayan sun gama gaisawa da malam idi ta bashi keys din hannunta gashi Malam kayi hakuri ka mikani gidan Hajiya Kaka. Daria yayi ya karbi keys din yace muje kawai hajiya karama! tayi murmushi muje to.

Amal! ki tashi kin kusa makara faah, ta bude ido a hankali Umma ke ce yau kk tashina, lallai yau za'ai ruwa da kankara.

Hingonki kekam ta mata dakuwa! to mijinkine yake jiranki a falo. ta tashi da hanzari ta nufi toilet dan shiryawa.

Daria Umman tata tayi, su Amal masu miji Allah ya kaimu bikinki musha hidima.

Sai da ta gama shiryawa tsaf kafin ta sauko kasa, Kai tsaye darning ta nufa dan yin break fast.

Ta samu darning din a cike kamar yadda ta saba samunsa, good morning all! ta ce sannan ta zauna 'a gefen Majeed ya kake Yaya ? yad'an 'bata fuska klau nake! daga haka bai kara ce mata komai ba yaci gaba da karyawansa.

MEE'ADWhere stories live. Discover now