Chapter 8

115 2 0
                                    

💫💫💫💫
_*MEE'AD*_
💫💫💫💫
*PERFECT WRITERS' ASSOCIATION*🌞

( WE AIN'T PERFECT BUT WE'RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS 💪)

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P.W.A✍️

*THE BOOK IS WRITTEN*

*BY*

*_HAUWA IBRAHIM MISAU_*

Wattpad__@hauwancyy44

JINJINA & SADAUKARWA

Na jinjina na kuma sadaukar da wannan littafin na gareki babbar aunty SAFNA ALIYU JAWABI Allah ya kara daukaka, basira da kuma fasaha ya kuma kareki da sharrin dukkan mai sharri. Ameeen .

*- Page -* 11 & 12

Zaune suka tarar da Yaya Majeed bisa kan farar kujera hannun sa rike da littafi da 'alama karatu yake, da sallama suka isa wajensa kafin su zauna bisa grass carpet din dake shimfide a garden din, harara Yaya Majeed ya bisu dashi kafin yace sai yanzu kuka ga daman fitowa ? Cikin sarkewan harshe Mee'ad tace Yaya kayi hakuri na sameta tana wanka ne, a hasale Majeed yace to kuma sai nace kuzo ku zube a kasa ko ? A hanzarce suka tashi suna cewa sorry Yaya! Murmushi Majeed yayi kafin yace ku nemo abin zama now karku bata mana time i hope u understand ?" A tare suka amsa da yes! Tare suka nemo kujera suka zauna, Majeed ya fara musu lesson cike da kwarewa.

----------------------------------

Haka kwanaki, sati da watanni sukaita shudewa, bayan tsayin wannan lokacin Umman Majeed ta kara haifuwa ta haifi ya mace mai kama da ita sak! Anyi suna an gama lafiya 👌 ba'a dade da yin suna ba Mommyn Mee'ad ta haifi yan biyu duka maza 'ansha hidima sosai yara sun amshi sunan Abban Mommy da Abban Daddy, gasu masha Allah, yayin da ita kuma Umman Amal bata kara samun haifuwa ba tin daga kan Amal, Amal ya' daya tilo a wajen mahaifanta 2 wannan dalilin yasa Hajiya suwaiba ta shagwaba Amal sosai sai abinda take so ake mata, idan tace batason abu to baza kuma 'ayi wannan abinba duk muhimmancin da yake dashi kuma.

MAFARIN SOYAYYA! bayan kammala secondary skull din Majeed ya fara preparation din tafiya makaranta, Daddyn shi ya samar mashi da makaranta a kasar india domin kuma yasan babban burin dan nashi nason zama cikakken medical doctor kamar babanshi.

" Amal zaune take cikin dakinta bisa gado tana danna remote da 'alama kallo takeyi, Majeed ne ya turo kofar dakin da sallama a yatsine ta 'amsa masa sallaman tana cewa sannu da zuwa Yaya, murmushi Majeed yayi kafin yace Kanwata kallo kike yine ? Shiru Amal tayi kafin tace eh kallo nakeyi, murmushi ya karayi a karo na biyu kafin ya zauna kusa da ita ya kamo hannunta cike da kulawa ya tsareta da ido 👀 kafin yace Kanwata saura kwanaki kadan nabar kasar nan , gaba daya ina cikin damuwa sbd nasan zanyi miss dinku sosai musamman ke da mukafi shakuwa, murmushi Amal tayi kafin tace to dan kawai zaka tafin shine saika shiga cikin wata damuwa ? Nikam banga wani amfanin shiga wani damuwa ba gaskiya 🤔 Majeed ya nisa kafin yace Amal kenan koda na tafi baza kiyi wata kewata bako ? Amal ta tabe baki kafin tace Yaya wai miyasa kk yimin wadan nan tambayoyin ne ? Majeed yace ba komai barina shiga ciki gurin Mommy nasan Umma kam tana sama ko ?

"Gyada kai kawai tayi batace komai ba, cikin hanzari Majeed ya mike ya nufi kofar fita sai da yaje bakin kofar sannan ya juyo yace Amal ya kamata ki daura zance na bisa kan mizanin hankali domin kigane mi nake nufi da 'abinda na fada miki, yana gama fadin hakan ya fice daga dakin Amal tabi bayansa da kallo tana yatsina fiska.

Ranar wata juma'a da yamma Mee'ad ce zaune cikin kitchen tana taya Mommyn ta girkin dare albasa take yankawa hannunta rike da wuka, Majeed neya shigo cikin kitchen din yana cewa Mommy yau kenan a kitchen ?

" Mommy tace kwaraima kuwa,"

"Majeed yace Mommy da kinyi zamanki munyi girkin da karamar kanwata Mee'ad ai,

"Mommy tace haka kawai saina barku kuyi girki ko ?

Majeed yace Mummy ai mun iya girki sosai, Hararar sa Mommy tayi kafin tace kaga fice ka bani waje karka sa na kona girkina da wannan surutun naka, murmushi Majeed yayi kafin ya ce sorry Mommy kinga tafiyata ma, ya juya zai fita dasauri Mommy tace kaga zo kana juyamin wannan miyar, zan shiga ciki nayi mantuwa Majeed yace to kawo ina juyawa kafinki dawo ya karbi ludayi ya fara juya miyar cikeda kwarewa dan kuma Majeed gwanin iya girkine domin tin yana yaro kullum yana kitchen musamman ranar da Mommy take girki, Mee'ad zaune take bisa kan kujera sai yanka albasanta take kamar bataji shigowan Majeed ba har suka gama zancensu da Mommy bata tanka musu ba hasalima ko daga kai batayi ta kalli inda suke ba, tinda Mommy ta fita daga kitchen da kusan 5minute ba wanda yayi magana a cikinsu, Mee'ad ta gama yankan albasan ta wanke ta mikama Majeed tana cewa gashi ka zuba 'a ciki Yaya, Majeed ya harareta kafin yace sai yanzu kika san da zamana 'anan ?

"Mee'ad tace sorry Yaya yau banison yawan surutune,

"Majeed yace au hakama zakice ? Toki kwantar da hankalinki nikam ma ranar sunday zanbar miki kasarma,

Mee'ad tace da gaske kk ?

Majeed yace tsaya kallon ruwa kwado yayi miki kafa, Mee'ad ta nisa kafin tace Yaya kace mu fara shirin rakiya kenan ? Majeed yace ke ina zakije da wannan halinki na ustazai din, murmushi Mee'ad tayi kafin tace ko banje can ba zanbi su Mommy rakiya zuwa Airport ko ? Majeed yace idan kinga dama ba 🙄 Mee'ad ta gwale fararen manyan idanunta kafin tace hakama kace ko ? To kasa 'a ranka bazanje rakiyan ba, ta juya a hasale zata bar kitchen din ya riko hannunta yana dariya kafin yace sorry Kakata aiban isa nabar kasar nan bakije rakiya ba Mee'ad tace nikam bazani ba Majeed yace forgive me kakata cox bazan karaba kinji ? Gyadakai Mee'ad tayi tana murmushi kafin tace ya wuce, dariya Majeed yayi kafin yace ko kef ?Qawata ai 'idan kikayi fishi ba kiyin kyau sosai 🤗 Mee'ad ta kyalkyale da daria tana fadin wacece kawar taka Majeed yace gaki, Mee'ad tace haba dai ? Majeed yace da gaske daga rana irin tayau kin zama babbar kawata kawo hannun ki dayan ma mu daura kawance Mee'ad ta mika kasa hannunta dayan sukaci gaba da dariya cike da farin ciki.
Cikin wannan yanayin Mommy ta shigo kitchen ta samesu tadan jima 'tsaye kafin tayi gyaran murya ihm! Ta karaso ciki tana fadin haka 'ake girkin a garinku kun tsaya kunata shashanci har miyar ta fara konewa Majeed ya sake hannun Mee'ad da sauri yana fadin kiyi hakuri Mommy na lallashe tane, Mommy tadan yatsine fiska kafin tace wannan kuma damuwar kune ku fice ku bani waje na karasa 'aikina, Majeed yaja hannun Mee'ad suka nufi falo yana kara lallashinta..........






























Pls fans don't forget to read & share to other groups 👌👌👌








Love u much my fans😍😍😘






Pls

Fans

Ku

Nemeni

Akan

Wannan

No din

Dan bada shawara ko makamancin haka 👌haka zalika idan kina/kana son shiga MEE'AD FANS GROUP duka ku nemeni ta wannan no din 👉👉👉 09039285813 👈👈👈











Taku har kullum Hauwancyy Misau 😍😍😍😍😍😍😍😍😍😍😍😍😍😍.

MEE'ADDove le storie prendono vita. Scoprilo ora