Chapter 10

98 2 2
                                    

💫💫💫💫
_*MEE'AD*_
💫💫💫💫
*PERFECT WRITERS' ASSOCIATION*🌞

( WE AIN'T PERFECT BUT WE'RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS 💪)

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P.W.A✍️

*THE BOOK IS WRITTEN*

*BY*

*_HAUWA IBRAHIM MISAU_*

Wattpad__@hauwancyy44






JINJINA & SADAUKARWA

Na jinjina na kuma sadaukar da wannan littafin na gareki babbar aunty SAFNA ALIYU JAWABI Allah ya kara daukaka, basira da kuma fasaha ya kuma kareki da sharrin dukkan mai sharri. Ameeen .





15 ~ 16







Rarfe 1:30am yayi dai2 da lokacin tashin su Mee'ad a skull, driver ne yayi parking a bakin kofar skull din yana jiran su fito, Mee'ad ce ta fara karasowa ta bude kofar baya ta zauna tana cewa Baba an wuni lfy ? Baba direba yayi murmushi kafin yace lfy klau yarinyar kirki ina yar uwar taki ta tsaya yau din ? Murmushi Mee'ad tayi kafin tace tana nan isowa, kafin ta rufe baki Amal ta karso ta bude kofar moto ta zauna kusa da Mee'ad kafin tace Baba mu tafi ko ? Jijjaga kai Baba direba yayi kafin yayi ma motar key ".

" Tafiya sukeyi shiru ba wanda ke magana, Mee'ad ce ta katse shirun nasu da cewa Amal dazu Yaya ya sake turo sabon text faah! Amal ta dan harareta kafin tace ba nace karki kara fadamin magana 'akansa ba ? Daga yau banson na karajin maganar data shafi wannan text din nasa na banzan kina ganewa ko ?😒

"Mee'ad ta dan bata fuska kafin tace ke kika sani kuma daga yau bazan karayi miki maganar saba insha Allahu, tana gama fadin haka taci gaba da duba littafin dake hannunta, Amal itama tabe baki tayi taja jiki zuwa bakin windon ta zuge glass ta fara leka waje tana daria.

"Bayan isar su gida da yan mintuna suka shirya tsaf dan tafiya islamiya, Baba direba ne ya kara kaisu ya kuma dauko su cike da kulawa.

---------------------------------

Mee'ad ce kwance bisa kan gado hannunta rike da system dan kuma tin ranar da Yaya Majeed ya fara turo text take rike da system din sbd tarinka mayar masa da 'amsa cikin kulawa da kaunar juna domin a iya tinaninta shidin Yayanta ne kuma zuciyarta bazata taba so ko kaunar Majeed din da soyayya ba🙄 wannan kenan 👌.

Amal ce ta shigo fuska a daure ta nufi kan gado kusa da Mee'ad ta zauna kafin tace ke wai mike damun kine ? Naga 'a yan kwanakin nan kullum kina rikeda system kamar sabuwar kamu, murmushi Mee'ad tayi kafin tace kinsan ina yawan yin game aiko ? Amal ta yatsine fuska kafin tace wannan kuma damuwar kine ni kinga tafiyata ta juya baya cike da isa tayi ficewarta.

Mee'ad ta bita da kallo kamar yadda ta saba kafin ta girgiza kai ta fara typing message ma Yaya Majeed kamar haka....

"" Yayana dafatan kana cikin dadda dan yanayi cike da koshin lfy kamar yadda nake, su Umma suna gaisheka harda yar uwata Mee'ad babar kawarka, Yaya dama inaso na fada maka Daddy ya canja mana skull kuma Mee'ad ce tazo na daya kasan tanada kokari sosai, kuma kusan kullum sai munyi hirarka da ita, ka kula da kanka sosai yayan mu, har kullum ina maka fatan alkairi da kuma cin nasara 'a rayuwarka Allah ya kiyayeka da kiyayewarsa." Daga Amal.

Tana gama rubutawa ta tura fuskarta dauke da murmushi kamar yadda ta saba 'a kullum.

Ranar Sunday da safe zaune suke cikin shiga iri daya suna tsalle2 su kamar yadda suka saba, Amal ta dubi Mee'ad cikin kulawa kafin tace kanwata kinsan wani abu ? Girgiza kai Mee'ad tayi da 'alamar bata saniba Amal ta gyara tsayuwa kafin tace kinsan mi Amran Aunty ta fadi jiya a skull ? Kara girgiza kai Mee'ad tayi dan kuma bata san mi Amran tace ba,"

"Amal ta yatsine fiska kafin tace to wai cewa tayi Yaya Majeed yana burgeta kuma wai idan inada picture nashi na tura mata 👌murmushin jin haushi Mee'ad tayi kafin tace ke kuma sai kika ce mata mi ?

Amal tace ni ce mata nayi taje wajen Aunty ko Umma ta karbi no dinshi saita fada mishi, Mee'ad tayi yake kafin tace kin kyauta dama Amrah tana da wayane ? Amal tace tin yaushe Mom dinta ta sai mata,'

"Mee'ad ta danyi jimm! Kafin tace shikenan ya wuce bari naje nadan kwanta kaina ya fara ciwo kinsan yau munsha wahala a skull ko ? Amal tace kije ki kwanta kawai karki wahalar da kanki kinji kanwata ? To Mee'ad tace kafin ta wuce cikin dakin zuciyarta fal haushi.

Mee'ad tana shiga bed bata zame ko ina ba sai wajen system dinta ta dauko ta cikin sauri ta fara typing text ma Yaya Majeed kamar haka...

" Dafatan Yayana ya wuni cikin koshin lfy ? Yayana yau banga text dinka ba ko lpy ? Allah dai yasa ba wani abune ya same kaba sbd idan wani abu ya sameka bazan tabajin dadi ba. Yauwa Yayana dama inaso na rokeka wani alfarma idan har zaka iya yimin a matsayina na kanwarka da kk ji da ita! Yaya dama inaso na fada maka wata magana dana dade ina yawo da ita a raina kuma na kasa fada maka ita! Idan harka yadda na fada maka tozan fada idan kuma baka yadda ba nima na hakura da fadan, sbd nafison farin cikinka fiyeda nawa, daga Amal. Tura masa text din tayi ta kuma zauna tana jiran reply.

Har karfe 10:30pm bataga reply dinsa ba, tuni yanayinta ya canja ta kasa cin komai ta kuma kasa sukuni sai tinane2 banza takeyi,"

" Mai karatu karka manta da Mee'ad da take tinanin babu soyayya tsakaninta da Yaya Majeed sai abota da kuma yan uwantaka 😎 anya kuma tinaninta ya bata gaskiya 🤔 ?" Mai karatu shin mi kk tinanin zai iya kasancewa tsakanin Mee'ad da kuma Majeed ?" Muje zuwa dai mai karatu ko zamu iya gano miye gaskiyar abinda ke cikin zuciyoyin su!😍

Karfe sha daya dai2 agogon dakin Mee'ad ya nuna wannan lokacin yayi dai2 da shigowar sakon Yaya majeed cikin system din Mee'ad.......



Mai karatu ka biyoni danjin mi sakon ya kunsa😍😍😍😍.

























Pls fans don't forget to read, vote & share to other groups 👌👌👌










Love u much my fans😍😍😘


















Pls

Fans

Ku

Nemeni

Akan

Wannan

No din

Dan bada shawara ko makamancin haka 👌haka zalika idan kina/kana son shiga MEE'AD FANS GROUP duka ku nemeni ta wannan no din 👉👉👉 09039285813 👈👈👈





















Taku har kullum Hauwancyy Misau 😍😍😍😍😍😍😍😍😍😍😍😍😍😍.

MEE'ADWhere stories live. Discover now