Chapter 17

70 1 0
                                    

💫💫💫💫
          _*MEE'AD*_
                   💫💫💫💫
*PERFECT WRITERS' ASSOCIATION*🌞

( WE AIN'T PERFECT BUT WE'RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS 💪)

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P.W.A✍️

*THE BOOK IS WRITTEN*

*BY*

*_HAUWA IBRAHIM MISAU_*

%% wattpad__@hauwancyy44 %%

 

        JINJINA & SADAUKARWA

Na jinjina na kuma sadaukar da wannan littafin na gareki babbar aunty SAFNA ALIYU JAWABI Allah ya kara daukaka, basira da kuma fasaha ya kuma kareki da sharrin dukkan mai sharri. Ameeen .
 

√√√√√ MEE'AD fan's kuyi hakuri da rashin post akan time, sbd wasu dalilai. √√√√√√

         
     
**** Pls don't forget to vote, share & comments 👌 love u fan's 💯%.
          
                         

               

                   
  

                          29 ~ 30

_____ Fuskarta a daure ta karaso wajen da suke tsaye, binsu da kallo tayi kafin ta kyalkyale da daria tace kun tsorata ko ? Dama cewa nayi barina tsorata ku,"

Murmushi Mee'ad tayi kafin tace no wonder abin ya danyi surprise dina, Majeed ya jaa dogon numfashi kafin ya janye hannun daya mikama Mee'ad din, murmushi yayi kafin yace shine kika wani dagama mutane hankali ko ? Daria Amal ta karayi kafin tace ai yazama dole na daga muku hankalin ne shiyasa nayi hakan,"

"Daria sukayi baki dayan su kafin Mee'ad tace kunga nikam bari naje nasha tea nafara jin yunwa tana gama fadin hakan ta nufi kofar fita ko juyawa bata yiba sbd ji take zuciyarta na mata zafi sosai.

Fitan Mee'ad keda wuya Amal ta juya itama zata rufa mata baya ji tayi an rike hannunta ta baya, a hankali ta juyo ido hudu suka hada dashi kafin ya sakar mata da wani lallausan murmushi yace Amal kinsan zuciyata tana matukar kaunarki, kuma bazan taba juran rashinki a tare daniba 'amma tinda na dawo na kasa gane kanki, baki daya kin wani canja min sabanin da da bana zaune a kasarnan, Kanwata inaso kiyi hakuri mu koma kamar yadda muke a daacan kinji ?

A hankali ta bude baki take fadin naji dukkannin abinda kace kuma nayi maka alkawarin daga yanzu zan canja na koma kamar yadda muke adaa din, Murmushi yayi zuciyarsa cike da farin ciki yace yauwa ko kefaa, muje mu karya now kuma anjima zamu fita tare jinjina kai tayi hade da murmushi kafin tace Allah ya kaimu anjima, hannunsa yasa ya lakace hancinta kafin yace muje ko ?

"Tare suka jero suna fira har suka isa darning, inda suka tarar da mutanen gidan suna yin break gaishesu sukayi kafin suka zauna, fara karyawa sukayi suna fira, yayin da MEE'AD ke can gefe hannunta rike da cup tana shan tea a falo, lokacin da suka shigo kallo daya tayi musu taci gaba da shan tea dinta bata kara kallon inda suke ba kasan cewar zuciyarta na mata zafi, haka ta daure ta gama shan tea din kafin ta dauki wayarta ta haura sama.

Bayan sun gama karyawa kowa part dinsa ya nufa dan ya huta, Amal da Majeed kawai suka bari a falo sai fira suke irinta masoyan nan.
             

                   %%%%%%%%%

Karfe hudu da rabi dai2 Majeed ya gama shiryawa cikin wata ash din dakakkiyar shadda yayi matukar kyau sosai jikinsa ba abinda yake fitarwa sai wani dadda dan kamshi, key din moto ya dauka ya nufi cikin gida,"

Da sallama ya shiga Umma ya tarar zaune a falo tana danna waya, murmushi tayi kafinta amsa sallaman cike da kulawa zama yayi a kujerar dake gefenta kafin yace Umma barka da yammaci, murmushi tayi kafin tace barka dai dana ya yinin bakunta kuma ? Alhmdlh yace kafin ya dauko wayarsa number Amal ya kira! Tadan jima tana ring kafin ta dauka 'a hankali ya furta ina jiranku a falo, ok tace kafin ya kashe wayar suci faba da fira da Umma.

" Yau wacce rana naga harkin gama shiryawa Amal ta fadama Mee'ad dake tsaye bakin room dinta sai murmushi take, kallonta Amal tayi daga sama har kasa kafin tace wow kinga yadda kikai kyau kuma ?,

Gyara tsayuwa Mee'ad din tayi kafin tace ke banison tsokana faah! Dftn kin gama shiryawa ko ? Jijjiga kai Amal tayi da ' alamar ta gama shiryawan, murmushi tayi kafin tace to muje ko ?

Tare suka jero izuwa falon suna fira dukkansu sunyi kyau sosai, idan Majeed na kansu har suka iso cikin falon Umma ta kallesu cikin farin ciki da jin dadi kafin tace Masha Allah yarana kunyi kyau sosai musamman mai sunan Hajiya 😊

Amal ta tabe baki kafin tace to nida ba'ace nayi kyau din bama nace ma kaina nayi kyau din ta karasa maganar tana bata face 😔,

Majeed yace wama ya isa yace gimbiyata ba tayi kyau ba ? Daria Amal din tayi kafin tace fada musu dai Yaya, Mee'ad dake zaune a gefe tana danna waya a dago kai a hasale tana fadin kunayi kuna duba time dai,"

Yaya Majeed yace au Nina manta da dare ya fara ma, kuzo mu tafi ko ? Yana gama fadin haka ya nufi kofar fita daga falon, sallama suka yima Umma kafinsu rufaa masa baya.

A motor park suka taddashi zaune cikin moto, Amal ta zauna a kujerar dake gefen drive din, yayinda Mee'ad ta zauna a bayan moton hankalinta nakan wayar dake rike a hannunta.

" Cike da nitsuwa da kuma jin dadi Majeed yake driving din, sau tari yakan juyo ya kalli Amal dake zaune a gefensa sai yayi murmushi yaci gaba da driving din,"

Allah sarki baiwar Allah Mee'ad dake seat din baya shiru tayi ta kasa ci gaba da danna wayar, zuciyarta sai kuna take mata sbd kishi, jijjiga kai tayi kafin taci gaba da ambaton sunayen Allah kuma tana rokon ya kawo mata dauki a halin da take ciki, zuciyarta ce ke fadin tabbas ina kaunarka Yaya amma babu yadda na iya dolena koyi jure rashinka a kusa dani na kuma koyi kawaici sbd yar uwata.

Basu wani dade suna tafiya ba suka isa wani kayataccen wajen shan ice cream, parking moton yayi ya fito, gefen da Amal take ya zagaya ya bude mata marfin kofar murmushi tayi kafin ta kalleshi cikin kulawa tnx u My Yaya! Murmushin shima yayi kafin yakai dubansa ga Mee'ad data dade da ficewa daga moton har takai bakin kofar dazai sadata da cikin wajen,"

Murmushi yayi cikin zuciyarsa kafin yace hmm Mee'ad kenan har yanzu bata daina wannan miskilancin nata ba ? Jijjiga kai yayi kafin ya riko hannun Amal su rufama Mee'ad din baya.

Sai 6pm kafin suka bar wajen shan ice cream din, ShopRite suka nufa danyin shopping masu Umma.

" Basu wani bata lokaci a ShopRite dinba suka nufi gida kasancewar magariba ta gabato.

A hanyarsu ta komawa gida Majeed ya riko hannun Amal cikin kulawa yake fadin, tabbas naji dadin kasancewar mu tare a wannan ranan, kuma nayi matukar samun farin cikin da kwanciyar hankali domin na hango dumbin soyayyata shimfide a cikin kwayar idanunki domin.... Kafin ya karasa fadar maganar Mee'ad dake baya ta galla musu harara ta cikin mirror moton ta kuma kwada wani hargitsatstsen ihu tana fadin innalillahi wa inna ilaihirraji'un.....







Mai karatu biyoni kasha lbr 💯


Pls vote, comments and share Fisabilillah 🙏🙏🙏🙏🙏.

MEE'ADWhere stories live. Discover now