Chapter 29

70 3 0
                                    

💫💫💫💫
_*MEE'AD*_
💫💫💫💫

***CONTINUE***

*PERFECT WRITERS' ASSOCIATION*🌞

( WE AIN'T PERFECT BUT WE'RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS 💪)

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P.W.A✍️

*THE BOOK IS WRITTEN*

*BY*

*_HAUWA IBRAHIM MISAU_*

Follow me on wattpad
👇👇👇

@hauwancyy44

Facebook page
👇🏻👇🏻👇🏻

Hauwa Misau Hausa Novels.

JINJINA & SADAUKARWA

Na jinjina na kuma sadaukar da wannan littafin na gareki babbar aunty SAFNA ALIYU JAWABI Allah ya kara daukaka, basira da kuma fasaha ya kuma kareki da sharrin dukkan mai sharri. Ameeen .

√√√√√ MEE'AD fan's kuyi hakuri da rashin post akan time, sbd wasu dalilai. √√√√√√



**** Pls don't forget to vote, share & comments 👌 love u fan's 💯%.

🗣️🗣️🗣️🗣️🗣️🗣️🗣️
Ina kuke masu son DATA ? ku taho da hazanri ku saya dan kuma nazo muku da Data a sassaukan rahusa idan kuna bukata

📶 *MTN*📶

*500MB* 👉🏽 *#150*
*1GB* 👉🏽 *#300*
*2GB* 👉🏽 *#600*
*3GB* 👉🏽 *#900*
*4GB* 👉🏻*#1200*

Mai bukata ya tura ta wannan account number
👇🏻👇🏻👇🏻

3142669195 Hauwa Ibrahim First Bank .

Idan ka tura saika tuntubeni ta wannan number
👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻
09039285813.

Ga masu buƙata akwai Glo da Airtel da kuma 9mobile.

Masu bukatan data maza kuzo ga dama tazo muku har gida.

🎃🎃🎃

Thank you for contacting Hauwa Misau! BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE.

I am selling MTN data with cheap price.

MTN DATA PACKAGE
500mb ~ *#150*
1GB ~ *#300*
2GB ~ *#600*
3GB ~ *#900*
4GB ~ *#1200*

Dial *146*4# Check data balance VALIDITY 1 MONTH.

Airtel, 9mobile, Glo also available.

You Can Pay Through Bank Transfer Or Cash
3142669195
Hauwa Ibrahim First Bank.

Call or chat for more information ; 09039285813.

53 ~ 54

Rufa mata baya yayi yana ƙwala mata kira Amal! Amal!! Amal!!! Mi yake faruwa ki saurareni mana, bata tsaya bita kansa ba ta faɗa falo gamida banko ƙofar falon.

Ajiyar zuciya ta sauƙe ta nufi part ɗin Umma tana mai kwala mata kira da baki ɗayan muryar ta ji kake Umma! Umma!! Umma!!! A firgice Hajiya Suwaiba ta fito daga ɗaki tana faɗin na'am wai mi yake faruwa ne ? Kuka Amal ɗin ta fashe dashi ta faɗa bisa kafaɗun Umman nata"

"Daddyn Mee'ad wato Alhaji Usman ne ya banko ƙofar ɗakin Umma yana faɗin ina fitsararriyar nan take ido hudu sukayi da Daddy ya nunata da yatsa fuskarsa fal takaici ya ce ke da ubanwa na ganki tsaye a harabar gidan nan ? Shiru tayi tana rarraba eyes, ba tambayarki nake ba shirun ta kumayi, yace to bari kiji daga rana mai kamar yau ban aminta na ƙara kallonki tsaye da wani a harabar gidan nan ba, dama maganar da mutane suke faɗa akanki gaskiyane ? To bari kiji bazaki mayar damu mutanen banza ba, kuma yanzu a madadina na uba mai bada aurenki na sanya ranar Aurenki da ɗan uwanki nan da sati huɗu daku shirya dama karku shirya na gama yanke nawa hukuncin, yana gama faɗin haka ya fice daga ɗakin ransa 'bace.

Yana fita Umma ta dago kan Amal ta ƙura mata ido tana son jin dalilin faɗan da Daddyn yayi, Ta sauƙe sassanyar ajiyar zuciya ta gyara zama sosai ta ce Umma Abokin Farouq mijin da Laila zata aurane........Nan ta bata labarin dukkan abinda ya faru, taja numfashi tana cewa Umma kinga gayen ya haɗu sosai kuma akwai dala a hannunsa fiye da tinanin mai tinani kuma yafi Majeed kyau da komai Allah, Nikam ma har naji ya shiga raina sosai, "

Shiru Umma tayi daga bisani tace yanzu Amal ya kikeso nayi ? Bazan taba iyaja da abinda Daddynku yace ba kinsan Abba shi baya shiga irin wannan maganar komai yana hannun Daddy, gashi ɗazu mun sami matsala da Auntynku wacce take bamu shawara akan wannan al'amarin.

Amal taɗan zaro ido Umma yaushe kuka samu matsala da Aunty ? Gaskiya banji daɗin hakan ba ko kaɗan ki samu ki lalla'bata ku shirya kawai keda kanki kinsan kanta yana matuƙar kawo wuta amma har zaki iya faɗa da ita gaskiya akwai sake Umma,"

"Murmushi Hajiya suwaiba tayi domin tinaninta ya fara bata cikakken amsa kan abinda ya shige mata duhu, ta dawo da dubanta kan Amal ɗin kwantar da hankalinki zan shawo kan matsalar da yaddan Ubangiji," Tsalle Amal tayi gami da faɗawa kan Umman ta fashe da dariya. Hmm Allah shi kyauta.

Areef kuma tin lokacin da Amal ta rufo ƙofar falon saboda tsoro juyawa yayi ya nufi moto zuciyarsa cike da saƙe ~ saƙe haɗe da tinane ~ tinane, ba tare da tsammani ba yaji anyi masa magana ta baya juyowan da zaiyi yayi arba da Alhaji Usman fuskarsa ɗauke da murmushi risinawa yayi ya gaisheshi fuska a sake ya amsa Areef ya duƙar dakai Abba ni Abokin Amal ne kuma tare muka dawo da ita daga school, murmushi Alhajin yayi mun gode amma ban lamunci wani ya rinƙa ɗauko min yara daga school ba sbd munada ishessun direbobi a gidan nan amma mun gode sosai kuma dan Allah a kiyaye gaba,

"Yana gama faɗin haka ya juya zai wuce Areef yace Abba bakaji ba! Fuskarsa fal mamaki ya tsaya ya ƙura masa ido, taku ɗaya zuwa biyu Areef yayi ya isa gareshi ya kuma duƙar dakai a karo na biyu Abba ina ƙaunar Amal sosai kuma da Aure nake sonta Abba ku taimakeni ku bani auren Amal ko hankalina zai kwanta, Alhaji Usman yayi shiru naɗan wani lokaci yace tabbas yadda na ganka da kuma yanayinka kai mutumin kirkine sai dai kash kalamanka sunyi kama dana yaran zamani, dafa kafaɗarsa yayi karka damu insha Allahu zanyi nazari a kanka da kuma halayyarka harma da kalamanka idan na gama nazari zan sanar da wacce tayi maka jagora zuwa gidannan ta sanar dakai abinda na yanke kaga saƙo zaiyi saurin shiga kunnen ka kuma a sauƙaƙe," Godiya Areef ɗin yayi kafin ya shiga mota yayi mata key ya fice daga gidan fuskarsa ɗauke da murmushin jin daɗi.

Acan part ɗin Majeed tin lokacin da yayi arba da Amal tsaye da wani ƙato tana fira ya shiga part ɗin fitowan dabai sakeyi ba kenan a wannan ranar saboda tsananin kishi ya kasa kwanciya idan ya samu ya kwanta kasa bacci yakeyi da zarar ya rintse idonsa murmushin da Amal takeyima saurayinta yake gani, rintse idonsa ya ƙarayi tashi yayi zaune ya ɗauko wayarsa number Mee'ad ya kira bugu ɗaya ta ɗauka sallama tayi, sassanyar ajiyan zuciya ya sauƙe kafin ya amsa sallaman ya kk ƙanwata ? Ina Hajjaju kuma ? Tayi murmushi lafiyanta klau yanzu ta shiga part ɗinta yaukam shiru bamu ganka ba, gyara zama yayi kina da labarin na fara shirye ~ shiryen wucewa ko ? Eh nasani ka manta da jiya ka faɗa mini, Yaja dogon numfashi ya kira sunanta 'a hankali Mee'ad kinsan abinda yar uwarki tayimin yau....... Nan ya faɗa mata dukkan abunda ya gani shiru tayi kafin ta ce ka ƙara haƙuri Yaya ka kuma ƙarayi mata uzuri tinda kasan ba haka halinta yake a daba....lallabashi taci gaba dayi tana faɗa masa muhimmanci haƙuri da kuma zumuncin dake tsakaninsu, ta ƙarayi masa alkawarin zuwa Yola da zarar ya koma can ɗin, Fira sukayi sosai har dare ya raba.

Washe gari bayan sun idar da sallan asuba suna dawowa daga masallaci Alhaji yake faɗama Majeed ya yanke auren su nanda 4weeks fuskarsa fal mamaki ya dubi Alhaji ya ce Daddy dama inaso na tafi yola ranar sunday Ah ba matsala Allah ya kaimu ya kuma kiyaye hanya, jiya munyi waya Dr na shaida masa ranar bikin dana yanke shima yayi farin ciki sosai, nan sukaci gaba da fira har suka shiga gida.

Misalin ƙarfe 10;30am Majeed ne zaune a falonsa hannunsa riƙe da waya da alama chat yakeyi, yaji ana bugun ƙofar falo ƙarfi ransa 'bace ya nufi ƙofar falon ya buɗe yana mita yana buɗewa Amal ta turo ƙofar da ƙarfi har tana shirin tureshi, shigewa tayi ta kama ƙugu tana juya eyes irin na rashin kunyar nan, ta nuna Majeed da yatsa kai tace kai Malam! nasan dukkan shirinka akan auren mu da Daddy ya sanya nan da 4weeks dan haka nake umurtanka dakayi saurin janye auren nan idan kuma ba haka ba.......kafin ta ƙarasa taji sauƙan mari a kuncinta ji kake taass! taass!! taass!!!.


pls

Follow

Share

Vote

Comment

Fisabilillah 🙏🙏🙏.

MEE'ADWhere stories live. Discover now