Chapter 20

80 1 0
                                    


💫💫💫💫
_*MEE'AD*_
💫💫💫💫

***CONTINUE***

*PERFECT WRITERS' ASSOCIATION*🌞

( WE AIN'T PERFECT BUT WE'RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS 💪)

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P.W.A✍️

*THE BOOK IS WRITTEN*

*BY*

*_HAUWA IBRAHIM MISAU_*

Follow me on wattpad
👇👇👇
@hauwancyy44

JINJINA & SADAUKARWA

Na jinjina na kuma sadaukar da wannan littafin na gareki babbar aunty SAFNA ALIYU JAWABI Allah ya kara daukaka, basira da kuma fasaha ya kuma kareki da sharrin dukkan mai sharri. Ameeen .

√√√√√ MEE'AD fan's kuyi hakuri da rashin post akan time, sbd wasu dalilai. √√√√√√



**** Pls don't forget to vote, share & comments 👌 love u fan's 💯%.


35 ~ 36

Ummace tsaye ke surfa masifa ido rufe, ba musu Mee'ad ta nufi kofar fita daga falon.

Harara Umma ta bita dashi, kafun ta dawo da dubanta zuwa kan Majeed hade rai ta karayi cike da izza tace kai miye tsakaninka da waccar yarinyar ?

Dumm yaji kansa yayi, gyara zama yayi fuskarsa cike da fargaba yake fadin Umma kiyi hakuri nina tsayar da ita.

Dogon tsaki taja kafin ta nufi kofar fita daga falon zuciyarta cike da sake ~ sake.

Bin bayanta da kallo yayi kafin ya girgiza kai cike da mamakin abinda Umman tayi.

Mee'ad tana fita daga falon Majeed kai tsaye cikin kayataccen lanbum dake bayan dakinta ta nufa zama tayi kan farar kujera ta fara tinani kamar haka! waishin mi yake faruwane ? mi nayima Umma da har yasa ta mini irin wannan korar daga wajen Yaya Majeed ? bata da amsar dukkan tambayar ta, taja dogon ajiyar zuciya, kafin ta kara nitsawa cikin dogon tinanin.

A hankali ya karaso cikin garding din, kusa da ita ya matso yana mai karema fuskarta kallo, murmushin takaici yayi kafin ya zauna bisa kujerar dake gefenta handkerchief ya zaro daga cikin aljihunsa ya mika mata, karba tayi ta share hawayen dake zuba daga idaniyarta.

Ido ya zuba mata kafin ya ce kiyi hakuri Kanwata, nina janyo dukkan abinda ya faru kuma nayi nadama akan hakan. amma ina mai kara baki hakuri, pls kiyi hakuri kinji Kawata ya karasa maganar yana mai marai ~ raice murya.

Tuni ta nemi dukkan damuwa da bacin ranta ta rasa, murmushin jin dadi tayi kafin tace Yaya ka kwantar da hankalinka domin komai ya wuce.

Murmushin kwanciyar hankali yayi cike da tsokana yake fadin kinga yanda hankalina ya tashi sbd zubar hawayenki kuwa ?

"Girgiza kai tayi da alamar bata gani ba.

Murmushi ya karayi kafin yace hankalina ya tashi badan komai ba sai dan kina matukar bani kulawa kuma kinsan abinda nakeso fiye da yanda Bloodynki Amal ta sani.

Dogon numfashi yaja kafin yaci gaba da cewa na rasa wani irin canjawa Amal tayi tin lokacin dana dawo kasar nan bata wani bani kulawa kamar da, kwata ~ kwata na kasa gane kanta, in takaice miki koda daddadan text din da take tura minima ta daina.

MEE'ADWhere stories live. Discover now