Chapter 9

112 2 1
                                    

💫💫💫💫
_*MEE'AD*_
💫💫💫💫
*PERFECT WRITERS' ASSOCIATION*🌞

( WE AIN'T PERFECT BUT WE'RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS 💪)

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P.W.A✍️

*THE BOOK IS WRITTEN*

*BY*

*_HAUWA IBRAHIM MISAU_*

Wattpad__@hauwancyy44


JINJINA & SADAUKARWA

Na jinjina na kuma sadaukar da wannan littafin na gareki babbar aunty SAFNA ALIYU JAWABI Allah ya kara daukaka, basira da kuma fasaha ya kuma kareki da sharrin dukkan mai sharri. Ameeen .

13 ~ 14

Ranar sunday 9 o clock gabaki dayansu sun shirya tsaff dan raka Yaya majeed filin jirgi, yayinda baki dayan iyayensu suka shiga moto 1, Majeed, Mee'ad da Amal suka shiga moto daya drive yana driving cike da kwarewa.

Majeed ya dago kai fiskarsa dauke da murmushi yana fadin Amal idan na tafi zamu rinka waya aiko ? Amal ta dan tabe fiska kafin tace haba yaya wani waya zamu rinqayi kuma ? Nikam bani wani son yawan wayan nan gaskiya ,

"Majeed ya danyi jimm kafin yace kiyi hakuri ko a wayar Umma muna gaisawa kinji Kanwata ?

Amal ta gyara zama kafin tace haba yaya dan tsabar rashin kunya sai mu rinka yin waya dakai ta wayar Umma ? Gaskiya ba lallai na iya hakan ba,"

Murmushi Majeed yayi kafin yace idan bamuyi waya da wayar Umma ba da wayar wa zamuyi ?"

"Mee'ad dake gefen Amal zaune sai kallo titi take sai a lokacin ta tanka musu cikin hikima take fadin Yaya duk wannan abin ba wani abun daga hankali bane a iya tinanin gaskiya 🤔 a shawarce mizai hana tinda inada system kuma da simcard a ciki sai ku rinka chat kawai tanan kunga ba wanda zaima san mike tafiya a tsakani koba hakaba ?🤗

Majeed yayi murmushin jin dadi kafin ya riko hannun Mee'ad yace love u much Kawata 😊 gaskiya kinada basira sosai, daga yau kin zama kawata kinji ? Murmushi Mee'ad tayi kafin taci gaba da kallon titi tana mai duba time cikin agogon dake daure bisa hannunta, Majeed yadan gyara zama kafin yace Kanwata kin yadda zamu rinkayin chat dake ? Eh Amal tace tana mai yatsina fiska 😏 murmushi Majeed yayi kafin yaci gaba da danna wayar dake hannun sa.

"Ba wanda ya karayi magana a cikinsu har suka isa airport, jiran yan mintina sukayi kafin jirginsu Majeed ya tashi, suka juyo gida cike da kewarsa dan kuma yan 2 har kuka sukayi dake sun fara wayo sosai.

"Majeed ya sauka a masukin sa gwanin sha'awa 'a kasar India, bayan yayi wanka yaci abinci ya kwanta bisa katafaren gadon dake shimfide a dakin, ya danyi shiru kadan ba abinda yake tinani sai gida da kuma yan kannensa daya bari suna kuka, murmushi yayi a lokacin da zuciyarsa ta tina masa da Amal cikin zumudi ya dauko system dinsa ya kunna cikin kankanin lokaci ya fara typing message kamar haka...

"" Kanwata na iso cikin farin ciki , kuma kasar india kasace mai kyan gaske tare da abubuwa masu kayatarwa , akwai dukkan abinda nake bukata, amma nayi kewar gida bakin daya musamman ke, gaskiya nayi miss dinki sosai 😔 kuma zanso ace ki kularmin da kanki ako wani irin lokaci 🤗 kice ina gasheda Mee'ad babbar kawata, ki kuma gaidasu Umma".

Yana gama typing text din ya tura fiskarsa dauke da murmushi bakinsa na furta kalmar ina matukar kaunarki Amal 😍 murmushi ya kumayi kafin ya tsunduma cikin kogin tinanin kanwar tasa wacce ya reni soyayyarta tin tana karama kawo wannan lokacin, yaja dan guntun tsaki mtsww! Kafin yace ai ita har yanzu batama san da zaman soyayyan da nake mata ba, tinda har yanzu bata wani girma sosai ba 😔 yadan bata fiska kafin yace yazama dole na samo mafita dangane da wannan soyayyar, ya daga hannu sama yana mai cewa " YA ALLAH INA MAI ROKONKA KA KAWOMIN KYAKKYAWAR MAFITA CIKIN WANNAN MAKAHUWAR SOYAYYAR DA NAKEYI " Yana gama fadin hakan yace Ameeeeen sannan ya shafa hannayesa bisa fiskarsa.

A can nigeria kuma Mee'ad kwance take bisa kan gado tana danna system dinta sbd tana matukar son karatu ko danna system a ko wani irin yanayi, wannan dalilin yasa Daddy ya sai mata system din, ita kuma Amal tace tafison mp shiyasa Daddy ya sai mata mp mai kyau da tsada, " Mee'ad tana kan danna system dinta yayinda Amal ke gaban dress mirrow tana kwalliya,"

"Mee'ad ta dubi Amal fiskarta dauke da murmushi kafin tace 6ter albishirinki ?"

Murmushi Amal tayi kafin tace goro fari tass "

"Mee'ad ta gyara zama kafin tace yayanki ya tura miki sakoba.anzu, kizo ki karanta tabe baki Amal tayi kafin tace ki karanta dai inajinki Mee'ad ta bude ta fara karantawa kamar yadda ya rubuta tana cikin Karan tawar, Amal tace ke kinga kyaleni da wannan karatun kinji ? Mee'ad tace waike Amal mike damun kine ? Amal ta kara tabe fiska kafin tace kinga tafiyata sai kiyita karanta wannan shirmen zancen idan kin gama saiki masa reply 😲 tana gama fadin haka tayi ficewarta abinta, jijjiga kai Mee'ad tayi kafin tace Allah ya shiryamin ke Amal, ta danyi jim kafin taci gaba da karanta text din da Yayan nasu ya turo tana murmushi 😊.

---------------------------------



Bayan Mee'ad ta gama karanta text din tayi masa reply kamar haka..

" Ina fatan ka isa cikin koshin lpy ? Duk dama jikina yana bani hakan dftan kaci abinci kum kayi wanka kamar yadda ka saba 'a kullum ? Dukkan mutanen gida suna lpy, sai dai kewanka da ya hana kowa sukuni. Kaji dadin kasar India Yayana daga Kanwarka Mee'ad.

"Sai da ta rubuta sunanta tayi wani tinani saita goge ta mayar da sunan Yayartata kamar haka " daga Kanwarka Amal ".

Tayi murmushi kafin ta tura masa text din ba tare da tinanin komai ba," bayan ta tura taci gaba da danne2 ta cike da kwarewa.

Washe gari suna idar da sallan asuba suka fara shirin tafiya skull Mee'ad ta rika Amal shiyawa harta fita harabar gidan sai kuma ta dawo dakin nasu da gudu tana fadin nayi mantuwa,"

"Hararar ta Amal tayi kafin tace ubanmi kuma kika manta murmushi Mee'ad tayi kafin tace na manta ido nane barima kiga na dauko shi,"

"Ta sunkuya ta bude murfin site drower ta rungumo system dinta tana dariya take fadin to kinga idon nawa dana manta din ko 😀

"Tsaki Amal taja kafin tace dalla bani waje mashirmaciyar banza kawai computer ne zaki wani kirashi da sunan ido ?"

" Mee'ad ta kara kyalkyalewa da daria kafin ta sanya system dinta cikin jaka ta nufi kofar fita da gudu tana fadin idan ba kiyi sauri ba zamu tafi mu barki sai ki biyo bus 😋,

Amal ta tabe baki kafin ta rufa mata baya da gudu tana fadin bazanyi saurin ba kuma nafi karfin nabi bus tinda Umma ma ta fadamin haka 😏

"Mee'ad kara gudu tana fadin kanki akeji ai 😅😅😅.

















Pls fans don't forget to read, vote & share to other groups 👌👌👌



Love u much my fans😍😍😘

Pls

Fans

Ku

Nemeni

Akan

Wannan

No din

Dan bada shawara ko makamancin haka 👌haka zalika idan kina/kana son shiga MEE'AD FANS GROUP duka ku nemeni ta wannan no din 👉👉👉 09039285813 👈👈👈






Taku har kullum Hauwancyy Misau 😍😍😍😍😍😍😍😍😍😍😍😍😍😍.

MEE'ADTempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang