Chapter 13

80 1 0
                                    

💫💫💫💫
          _*MEE'AD*_
                   💫💫💫💫
*PERFECT WRITERS' ASSOCIATION*🌞

( WE AIN'T PERFECT BUT WE'RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS 💪)

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P.W.A✍️

*THE BOOK IS WRITTEN*

*BY*

*_HAUWA IBRAHIM MISAU_*

%% wattpad__@hauwancyy44 %%

 

        JINJINA & SADAUKARWA

Na jinjina na kuma sadaukar da wannan littafin na gareki babbar aunty SAFNA ALIYU JAWABI Allah ya kara daukaka, basira da kuma fasaha ya kuma kareki da sharrin dukkan mai sharri. Ameeen .
                       
                 
                          
                         

                   

                   
  

                           21 ~ 22

, , , , , , , , , CIGABAN LABARI, , , , , , , , , , ,

          Karfe 4 dai2 agogon dake daure bisa hannun Mee'ad ya nuna dago kai tayi ta kalli Amal dake driving kafin tace Bloody 4 faah ta cika!

"Ta juyo ta kalleta kafin tace aike kika jaa har wannan lokacin tayi, sunkuyar dakai Mee'ad tayi kafin tace toya muka iya kawai sauri zakiyi mu karasa mubama Umman Amrah sakon kinga saimu juyo da wuri ko ?

Harararta tayi kafin tace ke kin gama naki uzurin na kuma jiraki shine kike son ki hanani aiwatar da nawa uzurin to hakan bazai yiyu ba gaskiya 😟, 

"Murmushi Mee'ad tayi kafin tace nasan uzurin naki bashi da wani karfi ne shiyasa nace hakan, yatsina fuska Amal tayi kafin tace wannan kuma keya dama nima saina gama nawa uzurin kinji zancen gaskiya ko ? Shiru Mee'ad tayi bata kara cewa komai ba sbd tasan halin Bloody nata.

Suka danyi shiru na yan mintuna kafin Amal ta juyo tace waike agogon da kika sa muka bata lokaci wajen sayansa mawa kika sayawa ? Naga kamar na mazane ko ? Murmushi tayi kafin tace na sayama Mu'az na course din mune inaso nayi masa bazata ne,"

"Mtswww! Shirmen banza dai kawai zakiyi inji Amal."

"Sunkuyar dakai Mee'ad tayi bata kara cewa komai ba".

30minute after 4 dai2 suka isa gidansu Amrah,  horn Amal tayi mai gadi yazo da sauri ya bude get din, ta shiga tayi parking, cikin zumudi suka fita daga moton baki dayansu",

Amal tana sauri dan taje su zanta da kawarta Amrah, yayinda Mee'ad take zumudin haduwa da Umman Amrah sbd tana koyon abu da yawa tare da Umman musamman girke2 da kuma dressing da sauransu,"

Da sallama suka shiga cikin falon gidan ai kuwa sunzo a sa'a dan kuma Umma na zaune da 'alamar kallo takeyi da gudu Mee'ad taje ta fada jikin Umma tana daria,"

"Fuskar Umma cike da farin ciki ta dago kai tana cewa yau mutuniya tace a gidan namu ai Hajiya ta kirani take tambayata kokun iso! Ashe kuna kan hanyane abinku daria sukayi baki dayansu kafin su gaishe da Umman cike da girmamawa, Umma ta 'amsa tana daria Amal ta mika mata sakon da Hajiyarta ta basu su kawoma Umman,  kafin tace Umma ina Amrah ?"

Murmushi tayi kafin tace Amrah tana bed din...bata karasa maganar da take ba Amal ta tari numfashinta da cewa bari naje na sameta, bata jira jin amsar Umman ba ta shige ciki bata zame ko ina ba sai dakin Amran.

MEE'ADDonde viven las historias. Descúbrelo ahora