Chapter 35

186 8 3
                                    


💫💫💫💫
_*MEE'AD*_
💫💫💫💫

***CONTINUE***



*PERFECT WRITERS' ASSOCIATION*🌞

( WE AIN'T PERFECT BUT WE'RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS 💪)

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P.W.A✍️

*THE BOOK IS WRITTEN*

*BY*

*_HAUWA IBRAHIM MISAU_*

Follow me on wattpad
👇👇👇
@hauwancyy44

JINJINA & SADAUKARWA

Na jinjina na kuma sadaukar da wannan littafin na gareki babbar aunty SAFNA ALIYU JAWABI Allah ya kara daukaka, basira da kuma fasaha ya kuma kareki da sharrin dukkan mai sharri. Ameeen .

√√√√√ MEE'AD fan's kuyi hakuri da rashin post akan time, sbd wasu dalilai. √√√√√√



**** Pls don't forget to vote, share & comments 👌 love u fan's 💯%.

🗣️🗣️🗣️🗣️🗣️🗣️🗣️
Ina kuke masu son DATA ? ku taho da hazanri ku saya dan kuma nazo muku da Data a sassaukan rahusa idan kuna bukata

📶 *MTN*📶

*500MB* 👉🏽 *#150*
*1GB* 👉🏽 *#300*
*2GB* 👉🏽 *#600*
*3GB* 👉🏽 *#900*
*4GB* 👉🏻*#1200*

Mai bukata ya tura ta wannan account number
👇🏻👇🏻👇🏻

3142669195 Hauwa Ibrahim First Bank .

Idan ka tura saika tuntubeni ta wannan number
👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻
09039285813.

Ga masu buƙata akwai Glo da Airtel da kuma 9mobile.

Masu bukatan data maza kuzo ga dama tazo muku har gida.

🎃🎃🎃

Thank you for contacting Hauwa Misau! BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE.

I am selling MTN data with cheap price.

MTN DATA PACKAGE
500mb ~ *#150*
1GB ~ *#300*
2GB ~ *#600*
3GB ~ *#900*
4GB ~ *#1200*

Dial *146*4# Check data balance VALIDITY 1 MONTH.

Airtel, 9mobile, Glo also available.

You Can Pay Through Bank Transfer Or Cash
3142669195
Hauwa Ibrahim First Bank.

Call or chat for more information ; 09039285813.

65 ~ 66

Mee'ad tayi murmushi cikin sanyin hali tace uhmm ba wayayyiyar mace kikace ba ? Touh Allah ya sanyamu a sahun wayayyun mata Amma masu bin dokokin sa ba masu sa'ba masa ba sbd kinsan wayewa tana nufin abu da yawa ta karasa maganar tana kallon Majeeed cikin ido.

Shima murmushin yayi kafin yace kinga 'kanwata next week nakeson zuwanki kinji sbd shirye ~ shirye mu nada yawa sosai, ta sunkuyar dakai cike da kunya uhmm Allah ya kaimu next week d'in, Ameeen yace gami da kamo hannunta yana murmushi.

Ta mirror moton Amal ta hangosu cike da takaici taja dogon tsaki mtswww! Marasa kunyar banza kawai, latsa wayarta taci gaba dayi ta lalu'bo sunan Areef ta kirashi bugu d'aya ya d'auka ai kuma ta shagwa'be murya ta Fara masa shagawa'ba kamar babu mutane a moton, wannan kenan.

"Karfe hud'u daidai jirgin su Majeed ya tashi zuwa Yola bayan sunyi sallama driver ya dauke su suka kama hanyar gida.

Akan hanyarsu ta komawa gida Amal ta dubi driver cike da izza ta bashi umurnin ya biya dasu ta zoo road sbd tanaso tayi arba da farin cikinta, Mee'ad dake zaune a baya bata ce komai ba har suka isa wajenda Amal d'in tace suje.

A bakin wani 'kofar gida tace su tsaya cike da izza ta sau'ka a moto ta bud'e ma Mee'ad 'kofa sannan tace ki fito mu shiga ciki kinga saiku gaisa dashi, a hankali ta sau'ko daga motan sannan ta 'kura na Amal ido cike da takaici tace haba sister mi kuma zakije kiyi a gidan mijin da zaki Aura bayan kinsan hakan bai dace ba, kiyi ha'kuri mu tafi gida kawai domin kuma ni bazan shiga gidan Areeef ba ta 'karasa maganar tana hararar yar uwar tata.

"Amal taja numfashi cike da 'kaguwa tace kin gama shegen 'korafin naki ? Touh idan kin gama sai ki koma moto ki zauna bari na kirashi idan yaso yazo mu gaisa kinga sai mu wuce gida ko ? Murmushi Mee'ad d'in tayi yauwa ko kefaah! Au kinga na manta yau kince Mommyn Areef zataje gida ko ? Kinga mu tafi kawai saboda babu dad'i ace tazo bama nan. Laah kinga na mance da zancen zuwan nata ma maybe harda King d'in suka tafi dama nace mu biyo tanan saboda nayi surprised d'insa ne, Amma tinda hakan ya kasance muje gidan kawai, a hanzarce ta shiga moto suka nufi hanyar gida.

" Bayan isarsu gida kai tsaye part d'in Mee'ad suka nufa kasancewar sunyi arba da ba'kin motoci har guda biyu a harabar gidan kuma suna tsammanin Mommyn Areef ne ta iso.

Isarsu cikin d'akin keda wuya Mee'ad takai dubanta zuwa ga yar uwan tata kafin ta ce Dear kiyi maza ki shirya nasan Mommyn Areef zata bu'kaci ganin In-law d'inta, bari naje na sanar da Umma kina part d'in nan saboda susan mun dawo gidan, bata jira taji abinda Amal d'in zatace ba tayi wucewar ta kai tsaye part d'in Umma ta nufaah.

Zaune ta tarar dasu kamar yadda tayi tsammani da sallama ta shiga falon, bayan sun amsa sallaman ta zauna a d'aya daga cikin manya ~ manyan kujerun dake kewaye a falon ta sunkuyar dakai Umma barka da gida, dama nazo na sanar dake mun dawo ne ko za'a nememu, Murmushi Umma tayi cikin jin dad'i tace kinga jeki kice da Amal ta shirya ko sirikar tata zata bu'kaci ganin ta. Laah Umma ai na barta tana wanka ne yanzu ma zan d'auko mata kayan da zata sanya a jikin tane, Yauwa d'iyar albarka kije ki d'auko mata kaya masu kyau kinsan halin manyan mutane sai a hankali, Murmushi Mee'ad tayi kafi ta tashi da nufin zuwa bedroom d'in Amal, Umma ta dakatar da ita kinga d'iyar nan bari naje na za'ba mata kaya masu kyau kinji ? tashi tayi ta nufi kofar fita daga falon, Mee'ad ta bita da kallo fuskarta cike da farin ciki.

Bata dad'e da tafiya ba ta dawo hannunta d'auke da kaya kinga yi maza ki kai mata ta shirya da wuri saboda sun dad'e da isowa, kar'ba tayi ta nufi part d'in da tabar Amal.

"Karfe 5:00 jirgin su Majeed ya sauka a cikin birnin Yola yana sau'ka yayi arba da 'kannen sa tare da driver, Hanan ce ta fara hangoshi laah Afnan kinganshi caan! Fuskarsa cike da farin ciki ya 'karaso kusa da 'kannen nasa ya rungume su yana cewa Hanan anya kunyi miss d'ina kamar yadda nayi naku kuwa ? Yaya munyi miss d'inka sosai faaah bazaka gane hakan ba sai munje gida kawai ka shiga moto mu tafi gida tin jiya Ummi take ta farin ciki inaga ko bacci isashshe bata samu ba tana ta zumud'in ganinka, Majeeed murmushi yayi gami da lakuce kumatun 'kanwar tasa touh muje ko ? Ya kama hannunsu suka nufi moto, driver ya risina cike da girmamawa barka da isowa Alhaji 'karami murmushi yayi kafin yace barka dai Baba muje ko ? Ya bud'e musu 'kofar suka shiga kafin ya shiga kai tsaye suka nufi unguwar Malare dake cikin garin Adamawa Yola.

"A kano kuma gidan Alhaji Hisham Mee'ad kai tsaye part d'inta ta nufa da kayan Amal d'auke a hannunta da sallama ta shiga bedroom d'in zaune ta tarar da Amal hannunta ri'ke da waya da 'alamar chat takeyi, kinga tashi ki sanya kayan ashe tin d'azu suka iso suna falon Daddy.

"Ihuu ta saka wooooooh! Kikace tin d'azu suka iso ? Ta dubi kanta a madubi cike da zumud'i take fad'in Amal kinyi kusa zama Amarya kema zaki auri had'ad'd'en guy mai kud'in gaske hutu zaici 'kaniyar nada caan, ta saka tsalle kafin ta dawo da kallonta kan Mee'ad dake zaune sai Murmushi takeyi,"

"Tace Mee'ad shin kema kina murna da Auren Majeed kamar yadda nake murna da Auren Areef kuwa ?

"Shiru Mee'ad d'in tayi Uhmm ai ko banyi murna saboda ina son Yaya Majeeed ba zanyi murna saboda shid'in d'an uwa nane ta 'karashe maganar tana kallon 'kasa.

Amal ta gallah mata harar gami da jan dogon tsaki mtswww! A zuciyarta tace kajimin yarinya da kinibibin tsiya ? Ihmmm zan koya mini hankali akan wannan dabbancin naki zaki ganene......

pls

Follow

Share

Vote

Comment

Fisabilillah 🙏🙏🙏.

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Jan 05, 2023 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

MEE'ADWhere stories live. Discover now