Chapter 6

143 2 0
                                    

💫💫💫💫
_*MEE'AD*_
💫💫💫💫
*PERFECT WRITERS' ASSOCIATION*🌞

( WE AIN'T PERFECT BUT WE'RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS 💪)

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P.W.A✍️

*THE BOOK IS WRITTEN*

*BY*

*_HAUWA IBRAHIM MISAU_*

Wattpad __@Hauwancyy44

JINJINA & SADAUKARWA

Gareki babbar Aunty SAFNA ALIYU JAWABI Allah ya kara basira da daukaka ya kuma kareki daga sharrin mai sharri.

*- Page -* 7 & 8

Cikin ikon Allah anyi bikin Hisham an gama lpy Amarya ta tare a gidan mijinta dake cikin gidan yayansa Aliyu," amma kowa da part dinsa 👌 koda yake Hajiya Hindu ce da kanta tabar da umarnin su hadu a waje daya kasancewar tana son taga zumuncin ya'yan nata yayi karfi takance ko bayan raina zanso ku kasance tare waje 1 domin ya'yayenku su taso kansu a hade kuma zanyi alfahari da hakan koda ina karkashin kasa ne 👌 wannan dalilin ya sanyasu haduwa bisa waje daya domin babu abinda suke buri irin ganin farin cikin iyayen nasu, " wannan kenan.

Baban al'amari tin kafin Majeed yakai shekara 6 Amina ta badashi ma yayanta Aliyu kasancewa matanshi bata haifu da wuri ba domin bayan an basu majeed da shekara 1 kafin Hajiya suwaiba wacce suke kira da umma ta haifi diyarta mace kyakkyawa mai kama da mahaifiyarta , "

Tin lokacin da umma ta haifi Amal majeed ya dauki son duniya ya daura ma Amal wacce kullum ke rungume bisa hannu ko kafadar sa yana kaunarta sosai yana matukar bata kulawa fiye da tsammanin mai tsammani Majeed idan yana shirmen sa yakance umma duk wanda ya tabamin Amal dina saina bigeshi Umma takanyi dariya sbd yawancin lokuta idan ya fadi hakan yakan bata dariya sosai. 🤗🤗

Majeed ne zaune bisa falo hannunsa rike da yar kanwar tasa yana mata wasa, Aunty Amarya ce ta shigo falon fiskarta cike da fara'a tana cewa Majeed dan Umma masoyin Amal murmushi Majeed yayi kafin yace Aunty ni dan Umma ne amma ba masoyin Amal ba ai Aunty Amal kanwata ce, Murmushi Aunty Amarya tayi gami da shafa kan Majeed kafin tace to naji dan Umma😊 Majeed ya dago kai ya kalli Aunty Amarya kafin yace Aunty yaushe zaki kawo mana sabon beby ?" Murmushi ta kuma yi kafin tace na kusa kawo muku sabon beby kaji Majeed dina, " A hanzarce Majeed ya tashi ya mikama Aunty Amarya Amal ya nufi dakin Umma yana murna wai Aunty Amarya zata kawo musu sabon beby.🤗🤗

Kwana tashi ba wuya a wajen Allah yau Amal ta cika shekara biyu yayinda Majeed ya cika shekara takwas, A wannan lokacin kuma Aunty Fati wacce suke kira da Aunty Amarya Allah ya azurtata da samun haifuwar ya mace kyakkyawa mai kama da fulanin asali kusan duk wanda yazo ganin Bebyn sai yayi santi tsabar kyan halittar da ubangiji yayima Bebyn 👶 Beby kamar yar larabawa ga kyau ga kyakkyawan bakin gashi mai sulbi ga farin fata kai abin dai sai wanda ya gani.

Samun Bebyn Aunty Amarya yayi dai2 da kara ninkuwan arzikin Alhaji Hisham, Dan kuma tuni ya saya musu sabon gida mai kyan gaske a unguwar Nasarawa Gra dake nan kano, " Kwana 3 da zuwan Beby duniy, baki daya mutanen gidan suka koma sabon gidansu dake unguwar Nasarawa gra, dan nafi tsammanin a sabon gida zasu sha suna.

Kusan duk wanda yaje yaga sabon katafaren gidan da Alhaji Hisham ya kera sai yayi santi saboda tsabar kyau da tsarin gidan kaima da kanka mai karatu kana ganin gidan kasan nera ya koka.

Washe garin ranar da suka tare a sabon gidan Hajiya Hindu taje gidan saboda ta kara kallon gidan domin kuwa tasan da zaman sayan gidan, sbd tabama ya'yanta tarbiyyan da basa taba yin wani abu ba tare da sanin taba 😊

Pls masu karatu bari nayi amfani da wannan dama nayi tsokaci ma iyayen mu, musamman na wannan zamanin, a iya nawa nazarin ya kamata ko wacce uwa ta zama maijan ya'yayenta a jiki ta nusar dasu yadda ake bin kyakkyawar hanya, yadda wannan nusarwan zai bama mahaifiya daman jan yayanta a jiki har yakai ga duk wani abinda yaronta zai aikata sai ya sameta ya shawarce ta akan abinda yake shirin aikatawa ko yaya 'abin yake, da wannan nake shawartarku yaku iyaye ku zama masu jan hankalin yaya yennaku sbd da kansu zasu rinka fada muku dukkan abinda ke damunsu ba tare da shamaki ko wani abu makaman cin haka ba.

Ranar suna Beby taci sunan Hajiya Hindu, murna a wajen dukkan ya'ya da jikokin gidan bazai misaltuba musamman ita uwar gayya kuma takwarar beby wato Hajiya Hindu, Ansha shagalin suna an gama lafiya yarinya ta sami tarin kaya da sarkoki in takaice maka mai karatu har sarkan gwal Hajiya Hindu ta daura 'a wuyan takawarar nata.

Bayan anyi hidiman suna da 3days Hajiya Hindu ce zaune bisa babban falon dake gidan hannun ta dauke da jaririya, Majeed ne zaune gefen Hajiya Hindu yana cewa Hajiya kiyi hakuri karki tafi mana da Bebyn mu kinji ? Dariya Hajiya Hindu yayi kafin tace kaga rufamin baki zan tafida takwarata nikam idan kana sonta saika biyoni gidana mu zauna tare ko Yaya Majeed ta karasa maganar tana mai shafa kan Majeed dake sanye da uniform din makaranta, Umma ce ta fito daga bed hannunta rike da Amal ta karaso cikin falon a nitse kafin tace Hajiya an tashi lpy ? Hajiya Hindu tace lafiya kalau diyata yaya jikartawa ? Murmushi Umma tayi kafin tace lfynta klau, Hajiya tace yayi kyau, sannan taci gaba da cewa yauwa Suwaiba wai wani suna zaku rinka fadama takwara tace Umma tayi dariya kafin tace Hajiya ai tuni Daddyn ta ya saka mata suna Hajiya tace wani irin sunane haka ? Umma tayi murmushi kafin tace Hajiya sunanta MEE'AD! Hajiya tace wani irin sunane haka wai Mee'ad ? Umma tace nima ban saniba gaskiya amma naji Daddy ya fadi fassaran sunan Hajiya tace kinga mikomin wayata na kirashi yazo ya fadamin fassaran wannan suna dan bazan taba lamintar irin wadannan sunayen da ba'asan asalin suba.......

Kalubale gareku iyayen da suke sakama ya'yayensu sunan da basu masan ta ina aka samesuba, ya kamata muyi karatun ta nitsu a kammu kuma mu rinka sakama ya'yayenmu sunayen da suka halatta ba wadanda suka haramta ba 👌ya zama wajibi iyaye su rinka sanyama yayayensu sunaye masu ma'ana ba marasa ma'ana ba. A matsayinki na mahaifiya mai ilimi bai dace ki sakama yayanki sunan da kema kanki bakisan ma'anonin suba, ya kamata mu rinka bincike kafin mu sakama yaran namu sunaye irin haka 👌





Pls don't forget to read like & share.
Love u much my fans😍😘


Taku har kullum Hauwa Ibrahim Misau 🤗🤗🤗











Pls idan kunga akwai gyara ko yin wani abinda ba dai2 ba ko bada shawara akan wani abu daya shafi wannan littafin pls ku nemeni ta wannan no din. 09039285813 👈👈👈👈👈👈.

MEE'ADWhere stories live. Discover now