PART 1

12.9K 352 18
                                    

1. MAKABARTAR MU- *****by khadeejah Aminu*****
Tunda na tashi a gidanmu, bama fita, gidanmu kamar makabartarmu take, rayuwar mu bamu san wani hulda da wasu mutane ba kamar yanda ko wani biladama yakeyi a doran kasan nan ba, Makarantarmu a cikin gidan mu mukeyinsa. kuma ma Mahaifiyrmu ce ta koya mana sakamakon wani Malami da Abbanmu ya turo mana dan ya yarda da shi, yana koya mana littattafan Addini da na boko duka. Malamin a yanda zan iya tunawa yana da kirki sosai, Abbanmu ya koreshi daga aiki saboda ya dauki kanwa ta a kan cinyarshi. ni dai zan iya fadan cewa bada wani nufi ya dauke ta ba, dan dududu batafi shekara hudu ba a lokacin. kawai dai Abbanmu ya dauka da zafi ne har ya koreshi kuma yaki kawowan wani Malamin sai Ammin mu ke koya mana.
komai na rayuwa a gidanmu mukeyinsa. Mu hudu Allah ya azurta iyayenmu da. mahaifiyarmu bata zuwa ko kofar gida ne, a duniyan nan tunda na tashi ban taba ganin fitan ta ba, babu zumunci, ba'a bari a zo mata bama ballentana taje. duk da bansan wani luxurious life ba a lokacin amma nasan cewa Mahaifiyarmu tana tsaka mai wuya, duk saboda abu daya ne, tsananin kishin Mahaifinmu a kan ta.
Bazan taba manta lokacin da mahaifiyata take wani irin ciwo, duk da bansan ma'anar ciwon nata ba amma zuciyata tayi bakin ciki dan kuwa bayan ta gama wahalar ta haihuwa tayi. Haka ta santalo kyakkyawan danta Mai kama da Abbanmu, a lokacin ta umurceni da dauko mata wani jaka. bayan ta dauko sai naga da kanta ta yanke cibi. ta janyo leda ta kulle mahaifa. wannan ne ya tabbatar mun da cewa ba yau ta fara irin wannan wahalan ba. ita tayi wa kanta komai. ta shiga wanka, ta wanki dan ta ajiye shi akan gado. haka ta fito daga wanka tasha Magani, Ta shirya sannan naga ta shayarda yaron sannan naga ta kwanta bacci. a lokacinma Mahaifinmu baya gida. Haka naga mahaifiyata takeyi ,duk da karancin shekaruna nima ina tayata kuka. kullum idan naga Mahaifiyata tana kuka sai idan na tambayeta sai tace mun ta tuna da gidan sune, sai in ta jin labarin gidan su a bakin ta, sai inji inama a gidansu nake, idan na tambayeta ko zata kaini gidansu sai tace mun in Allah ya yadda.
Mahaifiyata kullum tana cikin hawaye, zaka dade baka ga murmushinta ba kuma bawai a rashin soyayya bane a'a Illah kawai yawan KISHIN NAMIJI sunan Littafin Khadija Aminu dake fitowa, ku biyoni a Makabartarmu masu kauna ta dan jin karashen labarin da irin illolin da zaman gidan ya jawo wa duka iyalansa. Idan naji comment masu kyau zan iya karasawa. tnx
taku ***** ummulkhairi
2. MAKABARTARMU -**** khadija Aminu***
A halin da muke cikin ne, na samu mahaifiyata dan jin asalin Labarinta da yanda ta hadu da mahaifinmu, a lokacin ina da shekaru takwas a duniya Amma ban mance da abinda ta fada mun ba, dan halinda muke ciki yana damuna ba kadan ba. Tayi kamar bazata fada mun ba sai da taga na dage tukun na ta fara da cemun Batula, sunana kenan, A salinsu 'yan garin bauchi ne a karkashin hukumar Misau a kauye wanda ake kira luggudi, luggudi karkara ne sosai, illahirin rugar nan bafulatanai ne basu da sana'a kamar noma da kiwo. kullum dare samari da 'yan mata sukan fita dandali ayi ta wake wake da sana'a kamar su kafi kaza,gullisuwa,madarar kuka, dan bagalaje, da dai sauran kayan kwalama. garin yana da zaman lafiya sosai dan akwai addinin musulunci. su biyu Inna hauwa ta haifa daga ummina mai suna hafsa wanda ake kiranta da Hansai sai dan uwanta wanda aka haifesu rana daya mai suna Hafizu, Baba karami shine mahaifinsu, yana zuwa ci rani ya dawo, suna zaman lafiyan su sosai da matarshi inna hauwa.
Baba karami yana da wani amini wato makwabcinsa. tare suke fita ci rani, idan lokacin damuna ne kuma suna gida tare ana noma, inna hauwa kuma tana kiwon kaji, da zakaru da talo talo.
kowa dai a kauyen yana da rufin asirinsa dai dai gwargwado. Ana haka ne watarana Baba karami ya tashi da ciwon sanyi. tun daga lokacin baya fita ko ina, da abin da inna hauwa ta samu shi take musu suke ci su sha. aminin Baba karami dayaga dan wahalhalu da ya fara samun abokin shi. sai yayi tunanin ya taimaka masa tunda dai Dan wajensa Hafizu ya dan girma, shine suke zuwa ci rani tare. Bayan shekara biyu Allah yayi wa Baba karami rasuwa, sai ya zamana a rayuwar inna hauwa ko kiwon ma bata yi. dan kudin nata dik sun kare a neman wa baba karami magani, a haka inna hauwa da dadi da ba dadi ta daure ta cije take zaman rayuwa da tawakkali.
A kwana a tashi ba wiya a wajen Allah, Hansai da hafizu su na da kimanin shekara sha uku. sun dawo da ga gona suna hanyar komawa gida kamar da hantsi sai Hansai ta taka kaya mai dafi, sai ta fara salati tukun na tace Hafizu kafa na. tana kuka ne sai hafizu ya duba kafan a take yace mata Hansai zauna anan, tukun sai ya cire mata kayan yace mata bari yaje ya samo itatuwa masu kashe dafi. Sai hansai tace a'a kar kaje kawai ka dawo mu tafi haka kasan jejin nan yana da mugayen abubuwa, gwara kazo mu tafi gida, a take yace mata in Allah ya yadda ba abun da zai faru, ya dauki kafan sa yayi gaba, hansai dai kafa sai kumburi take amma hafizu shiru har kusan goma na dare, da hansai taji jejin ya fara bata tsoron sai ta fara addu'oi wai ita a dole jiran hafizu takeyi.
Inna hauwa taji shiru yayi shiru 'ya'yanta basu dawo ba. kawai sai ta zuri mayafi, tafiya takeyi cikin jejin nan sai ta fara kiran sunayen 'ya'yNta har tayi sa'a hansai taji sai ta amsa. a inda hafizu ya tafi ya barta anan ta sameta ta na kuka wai ita sai ta jira hafizu ya dawo. anan dai inna dakyar ta roketa tukunna ta tashi ta bita suka tafi tare.
dingishin da inna hauwa taga hansai nayi shi yasa ta tambayeta abin da ya sameta, bayan ta fada mata da sauri inna hauwa ta daga hansay suka koma rugarsun nan sai gidan wata mai magani, anan aka fara mata jike jike.
inna hauwa sai ta bar hansai a gidan baba binta mai jike jike tayi gidan Aminin baba karami marigayi Allah ya jikan rai(ameen). Daga shiganta gidan sa sai ta fara masa bayanin cewa bata ga hafizu ba, anan ya dinga bata hakuri sannan yace mata bari suje dubo shi, tayi godiya sannan ta koma gidan baba binta. Baba binta ce ta sanar mata da cewa InAllah ya yadda nan da sati daya hansai zata warke, a haka ta dauke ta sukayi gida, hansai dai ita ba ciwon kadai ya dame ta ba. a'a wai ita sai dai hafizu kawai za'a kira mata. da kyar ta samu tayi bacci.
Inna hauwa kuwa tun tana addu'an har itama ta karaya ta fara kuka abun dai ba dadi.
yau kwana biyar da batan hafizu, kullum idan hansai ta tambayi inda yake sai ace mata wai yaje ci rani. inna kuma kuka. Haka har hansai ta gane cewa dan uwanta bata yayi.
(ALLAH YA RABA 'YA'YA YANMU DA BATA,AMEEN.)
A kwana a tashi kunsan hausawa sunce zara bata barin dami. duk illahirin kadarorinsu da suka tara ya kare, kawai sai inna hauwa ta yanke shawaran barin rugar nan da hansai. Inna hauwa ta sayar da gonan wajen Baba karami dama gidan da suke zaune bukka ne, sai ta bar wa wata mata wanda a cikin bunu take kwana. kunji masu taimako.
Dama lokacin da suka bar garin baba karami baya nan, ya tafi ci rani. basu sauka a ko ina ba sai Misau gidan Sarkin malamai. A dakin amaryarsa wai sunan ta hajiya iya. Duka zuri'an gidan Allah ya basu Mutunci da kirki da tsoron Allah. Ana zaman lafiya sosai a gidan.
Hajiya iya ce ta amshi Inna hauwa da hansai hannu bibbiyu dan tasan daga inda tazo, saboda lokacin suna ruga tare kawaye ne sosai da inna hauwa. Inna hauwa ta bawa hajiya iya duka labarin abubuwanda ya samesu mai dadi da marar dadi. Hajiya iya ta tausaya musu sosai har tace mata zata sama musu aiki.
A gidan sarkin Misau aka samawa Inna hauwa Aiki na wanke wanke, sai ta bar 'yarta a wajen hajiya iya tace mata ta barmata ita Amana dan ta yarda da Malamar sannan ta samu hansai tayi mata fadan yanda ya kamata ta zauna da Hajiya Iyan sannan tayi mata Addu'an Allah ya tsare ta. kullum idan inna hauwa ta zauna ba wanda take tunani sai hafizu, da ba don kar tayi sako ba da tace Dama Allah gawan Danta ya nuna mata ba batan sa ba, sai hajiya iya ta kwabe tane take yin shiru. Haka dai rayuwa ya cigaba inda hajiya iya taji tana son Hansai a ranta sosai dan irin kulawar da take bata duk da karancin shekarunta, tana mata gyaran daki, share share da wanki. sai ance ta zauna ta huta tukunna take dainawa, tana koya mata karatun Alqur'ani da lissafi, da turanci. a haka har hajiya iya ta gane cewa hansai na da ilimi sosai, sai ta sakata a makarantar da yake kusa dasu wato central primary skul.
Bayan shekarar su biyu da zuwa ranar inna hauwa ta tashi da ciwon ciki. Bayan kwana biyu ta koma Ga ubangijin ta. ( Allah ya jikanta da rahama). Ameen
Hansai tayi kuka ba kadan ba kuma duk wani mai sonta sai da ya tausaya mata. Mahaifiyarta ma ta samu yabo daga guri davan daban. A ranar jumma'an aka kaitaa MAKABARTARMU aka sata a gidan ta na gaskiya da fatan allah yayi mata rahama, Amin.
nan ne mafarin inda hafsat ta fara samun Matsala a rayuwarta masu karatu ku biyo ni dan jin labari mai rikitarwa na rayuwa kamar a makabarta.

HAUSA NOVEL (MAKABARTARMU)Where stories live. Discover now