Part 18

3.2K 81 2
                                    

30. MAKABARTARMU~~ KHADIJA AMINU
Malamin Nan duk abun da Yake yi wa Batula Ihu kawai takeyi Amma bata motsi, sai da ya dauka kurani tukun Na Yana karanta Ayaturruqya. Dakyar aka samu Ta Fara Motsi tana Tari Dan jin warin turaren da ake Mata. Malamin ne ya tambayeta ke wacece, sai tace Ni ka daina abun da kukeyi bana so, Ai wannan iskanci ne da zalunci irin Naku, ku kyale yarinya ta huta, idan ba Haka ba zan tarwatsa ku. Malamin ne yace, wallahi Baki isa Ba, Ai jikin biladam kika shiga, Kuma sai mun kona ki sai kin zama kamar Toka. Allah Ai bai halicci Mutum da Aljani Dan su cutar da junan su ba sai Dan su Bauta MASA. Wallahi sai kin Fita. "Baxan Fita Ba, Kuma ka daina damu na, Ai bani bane na Fara cutarwan ba nima Ramawa Nayi." Me tayi miki? " Wayyo!!! Ka kashe kur'anin zan Fada yace Baza a kashe ba sai kin Fada sannan ya Watsa Mata ruwan da yayi addu'anfa sai ta sake yin ihun Da tayi Daxu sai da ya razana Sergernt.
Kashe kira'an akayi ana tambayanta ta Fada abun da tayi Mata. Sai tace wai Ai Taka Maka Kan yaron ta tayi sannan Kuma ta watsar Mata da shanyar kayan da Tayi, shi yasa Ta shiga jikin ta sai tace hukuncin Ta Kuma shine a Rabata da duniya ko a nakasar da ita.
Anyi Anyi Aljanar nan ta fita a jikin Batula Amma taki sai da akayi da gaske lokacin tayi kokarin Fita Amma By Mistake ta fita Ta kunnen Batula. Bayan ta Fita Wani Aljani ya sake zuwa wai karan ta ne ya dameshi shine ya shigeta. Bayan wannan ma Wani yazo wai Ai tayi Mishi kyau ne shiyasa ya shigeta. Bayan wannan Ma Wani ya zo wai shi Taimakona Zaiyi Nan ma kiranshi a kayi akace Masa Taimakon Allah kawai take Nema. Haka aka tayi Ana ciresu sai da aka cire kusan 27 a jikin ta sannan aka Ga tayi shiru, ko da ta bude ido ma kawai bin Malamin takeyi da ido Amma Bataji Sai dai gani, da ta bude Bakin ta zatayi Magana sai Taji Bata iyawa. Kawai Hawaye ne kebin kuncinta.
Malamin ne yace yau abarta Haka Amma idan wannan turaren ya kare a barbada Wani ya Gama Kuma kar a kashe kira'an Dan zasu iya shigowa. Dan ma akwai Bushasshen Tafarnuwa a cikin turaren da Yake sawa a turarawan.
Daddy dai Bai Kara Magana ba sai kallo kawai da yakeyi yana tunanin Rayuwa da yanda take zuwa wa Dan Adam.
***** Salim dama da suka ISO gidan General bai shiga bama ya Kama Hanyar Gidan sa, yana isa bakin gate zuciyarshi sai bugawa yakeyi yana tunanin Yanda zaiyi idan yaga Zahran shi gawa ce.
Yana zuwa suka gaisa da Maigadi sannan ya shiga ciki, yana zuwa ya bude kofan gidan, sai yaga Ko Ina a bude Farin ciki ya Fara Dan yasan kafin ya Fita sai da ya rufe ko Ina Amma dai duk da Haka zuciyarsa Na bugawa, yana shiga daki sai yaga babu kowa a Dakin Kuma yanda ya tafi ya Bar kayan Haka yazo ya same shi komai intact. Ya leka ko Ina baiga Zahran shi ba. Ya kira sunan ta yafi a kirga da yaji Ba amshi sai ya Rude, ya tafi kofar Maigadi Yake Tambaya ko yaga wata yarinya ta wuce. Mai Gadi bai Gane ba yace A'a Amma da ya Kara zuwa yayi mASA kwatance sai Mai gadin ya gano Sai ya fada mASA cewa Ai tun washegarin Ranar da ha tafi yarinyar Ma ta fita. Salim A'a kawai Yake Fada yana, zahra Baza ta gudu ta Barni ba, bazan iya ba. Da sauri ya shiga gida jiki ba kwari yana Neman Mafita. Ya shiga dakin yana watsar da kayan dakin kamar Wanda aka mishi Alluran sojoji yana cewa No!!!! Zahra u can't leave me. Kwanciya yayi yana Mayar da Numfashinsa dake Fita a hankali, yana tunanin yanda Rayuwarshi take kafin Haduwa da Zahra da Kuma yanda ya canxa Bayan Haduwarshi da ita.
Da daddare Salim yana ta juye juye ya Rasa inda zai sa Kanshi Ban San meya tuna ba kawai ya tashi yana ta bincike a Dakin Da Yake.
Yana janye bedsheets din Gadon Zahran sa sai ya Ga Hoton nan da ta Hana shi kallo tun lokacin da ya sameta. Yana dagawa zai bude sai yaji wayan shi tayi ringing. Da sauri ya je ya dauka yana ganin Hoton Popsynshi yasan cewa yayi laifi shi yasa Yake neman shi. Da Kyar ya daga wayan jiki ba kwari, yana sawa a wayan shi ya Fara cewa Popsy......, kafin ya karasa Magananshi popsyn ya katse shi yana cewa "Ba Wani popsyn nan, kayi mun shiru da Bakin ka,ka ISO Gari Amma ko kazo ka gani, ba ruwanka da Familynka kayi gida ko? Ba ruwanka da mamyn ka ma ko? Ba kason kanwar ka ko? Sannan baka son su Uncles dinka ko? Toh zaka zo ka sameni. Kafin Salim yayi Magana har ya katse wayan. Dama Salim Baya son Bacin ran Popsynshi, duk da yanayin da ya shiga Hakan bai hana shi Tashi ya dauka kayan shi ba sai ya Bar hoton a wajen Ba tare da ya kalla ba. Fita kawai yayi yaje gidan General ko zai samu Popsynshi, Gashi kanshi duk a rude Yake kawai innalillahi wainna ilaihirrajiun Yake Furtawa. ***ummulkhair***

HAUSA NOVEL (MAKABARTARMU)Where stories live. Discover now