PART 2

6.4K 134 8
                                    

3~MAKABARTARMU~khadija Aminu
Yau kwana bakwai da rasuwar Inna hauwa amma hafsat kullum Batayi hakuri ba sai kuka. sai hajiya iya tanemi a kira mata ita bayan an kira ta sai ta fara mata nasiha kamar haka, kar kiga kin zama marainiya, baki da kowa sai Allah, ki zata cewa Allah baya sonki ne, A'a, ki gode wa Allah. ki yi tawakkali. kina nan kina ganin yanda ake ta yabon ta sannan ma ai Mutuwan shahada tayi. Ai murna zaki tayata dashi. kuma muma ki roki Allah yasa tamu in tazo mu cika da imani. Hafsatu ta daga kai kamar zatayi magana sai hajiya iya ta janyo ta jikin ta tace mata Kar ki damu ai da nakowa ne, nima zan rike ki har girmanki, Har auranki, insha Allah.
hafsat ce ta tsuguna a gaban hajiya iya zatayi godiya sai Hajiya iya ta dago ta tace A'a kar tayi. sai hafsat tace Amma ina son in san meye Mutuwar shahada dan naji kamar kina fada mun wai ai inna ta tayi mutuwar shahada. Gyaran murya Hajiya iya tayi sai tace ALAMOMIN WANDA YA YI MUTUWAR SHAHADA Manzon Allah (S.A.W) ya ce: "Akwai alamo goma sha Tara (19), wadanda ke nuna mutum YA yi mutuwar shahada". Su ne
1. Wanda maganarsa ta karshe kafin ya mutu ita
ce "La'ilaha Illallah".
2. Wanda ya mutu goshinsa na jibi.
3. Wanda ya mutu daren Jumu'a (Wato bayan
yammar Alhamis), ko kuma a cikin yinin Jumu'ar.
4. Wanda aka kashe a fagen yakin jihadi.
5. Wanda ya mutu a wajen aiki na daukaka addinin Musulunci.
6. Wanda ya mutu a cikin annoba (Kamar lokacin "Colera" ko amai da zawo da dai makamantansu).
7. Wanda ya mutu a sanadin ciwon ciki.
8. Wanda ruwa ya ci.
9. Wanda gini ya ruguzowa.
10. Matar da ta mutu wajen haihuwa.
11. Wanda ya mutu sanadin konewa a cikin gobara.
12. Wanda ciwon bulala ya zama sanadin
mutuwarsa.
13. Wanda ciwon tarin huka (T.B) ya zama sanadin mutuwarsa.
14. Wanda ya mutu wajen kariyar dukiyarsa (Kamar wanda ya yi fada da 'yan fashi sai su ka kashe shi).
15. Wanda ya mutu wajen kare martabar addinin Musulunci.
16. Wanda ya mutu wajen kariyar ransa ko na iyalinsa.
17. Wanda ya mutu wajen gadin jama'ar Musulmi (Kamar 'yan Banga da ire-irensu).
18. Wanda ya mutu yayin da ya ke yin aikin alkhairi (Kamar Azumi ko sadaka da sauransu).
19. Wanda azzalumin Shugaba ya kashe don ya
fadi gaskiya.
********************
Manzon Allah (S.A.W) ya ce: "Wanda ya mutu a daya daga cikin wadannan halulluka 19, to, ya na da busharar cewa shi dan Aljanna ne".** Allah ka datar da mu. Amin.
Bayan ta gama sai Hafsat tace Amin.
Hafsat tana birge mutane dayawa musamman saboda Ilimin ta da saurin daukan abu gashi tana da faran faran da mutane sai dai idan mutum bai zauna da ita ba. Idan hajiya iya ta kalle ta sai tace oh! Rayuwan nan yanxu dubi 'yar nan kamar ita ta zana kanta a halitta, ba bu abinda bata mallaka ba na 'ya mace, ita ba fara bace kamar baturiya amma idan ka ganta cikin farare tana dibi dasu haka idan ta zauna cikin bakake tana dibi dasu nan ma, zan iya kiran ta da wankan tarwada. tana da dimple daya a kumatunta na dama. kunsan dai yanda fulanin jeji suke basai an fada ba gashinsu kawi kulane baya gani amma Allah ya bata. hajiya iya tana kula da lamarin yarinyar nan sosai. Dayake babban gida ne, har ta saba da mutane ba kadan ba. kawayen ta sune su Jamila, Nana Maimuna, Da Fatima, da larai, da salaha, har ma da Rakiya. Suna shiri sosai, tare suke zuwa makarantar boko harda na islamiyya.

Kwanci Tashi
*****Yau an wayi gari shekaran hafsat goma sha takwas a duniya samari sunyi mata caaa, saboda tsananin kyanta, baba lami ta aiketa galdimari karbo dinki anan ta hadu da wanda har yau baza ta taba manta Alkhairin bawan Allahn nan ba. Ta karyo kwana zata shiga gidan kenan sai taji an ban gajeta an wuce sai ta fusata ta juyi da zatayi masifa kawai sai ta tsinci kanta da cewa Nagode, sai ta juya abun sai ya daure masa kai, bata ma bari ya bata hakuri ba gashi har ta gode masa sai ya tsaya a bakin kofar gidan kawai yana jiran yaji dalilin godiyan nan da tayi masa. Ya zauna yafi minti ashirin dan yana jiran fitowan ta sai yaji shiru, sai ya shiga gidan dan ya duba ta sai akace masa ai tade da fita. shi bai masan cewa da ta fito daga gidan bayansa tabi ta wuce. yaji haushi sosai abinda tayi. sai kawai ya fita daga gidan yana huci. Bayan ya je gida kwana biyu yayi yana tunanin yarinyar nan, kawai sai ya yanke shawaran ya je gidan da yaga ta shiga hakan kuwa akayi, yaje gidan yayi musu kwatancen yarinyan sai aka hada shi da wani yaro ya raka shi gidansu hafsat. Ya mika wa yarn Naira dari biyar ya shiga gidan da sallama, da ya ke babban gida ne anan akayi mishi iso har babban falon gidan yayi bayanin abin da ya kawo shi gidan. sai da aka kira hafsat ko ta san mutumin ai kuwa ta amsa da eh tasan shi. dama itama tunda take bata taba jin namiji ya tsaya mata a rai kamar yanda wannan yayi ba. kawai sai ta shirya taje gurin shi, bayan tayi sallama ya amsa mata, sai ya rasa abin da zai ce mata amma sai ya ce dan Allah Nana Hafsah idan na bata miki rai kiyi hakuri, Ba da sanai na na bugeki ba. Nima naje neman kanina ne a gidan da kikaje, da ban gan shi ba kuma sai rai na ya baci na fito da sauri har na buge ki. sai hafsah tace bakomai Ai nasan bazaka bugeni haka kawai ba sai tace Nagode ta tashi tsaye zata tafi sai yace mata ban gama ba Nana Hafsah, duk sanda ya kira sunan ta sai taji kamar ba wanda ya iya kiran sunan ta kamar shi. kawai sai ta zauna, ya gyara murya yace mata dama ina so ki tausaya wa maraici na Dan Allah ki soni. Bani da kowa a duniyar nan da suka rage mun sai dai kanina. Ban cika zama a garin nan ba. Don kr2 nake yi a BUK kuma ina 400 ne level yanxu. abin da yake kawo ni ma sbd kanina ne wanda shi kadai Allah ya barmin a rayuwa duk da shi baya jin Magana sosai. kiyi Hakuri Na cika ki da surutu ban ma fada miki sunana ba, dan Allah kiyi hakuri. Sunana Ahmad Bello. Last year iyayenmu suka Rasu sakamakon Accident, nayi kukan rashinsu sosai, ki taimaka ki amshi soyayya ta dan ke kadai kika kwanta mun a raina. Yana gama fadan haka sai ya sunkuya dan yaga fuskan ta ko ta amince sai kawai yaga hawaye yana fita daga idanuwanta, sai kawai ta razanar dashi, sai yace na dame ki ko? bakyasona ko? kawai sai ta girgiza kai tace ba haka bane kawai dai naji zafin mutuwan su dan nima nasan zafin rashin iyaye, Nima iyayena duk sun rasu, bani da kowa sai Allah sai kuma Gata na Hajiya iya. sai kai wanda kaima kasan zafin mutuwan iyaye. A take kawai ya kara jin ta zauna a ransa kawai sai ya gode ma Allah tunda ta amince dashi. Kafin ya tafi sau da ya mata Alkawarin Aure. Amma sai tace A'a wai ita bazata yi aure yanzu ba sai tayi karatu dan yanxu tana jss3 ne sai yace mata idan dan wannan ne yayi mata Alqawarin Barin ta tayi kr2 a haka suka rabu. ranar zuciyan hafsa cike da farin ciki.
*****Maganar aure ta kan kama dan har ansa rana kuma an kawo kayan lefe. Hajiya iya, Baba binta mai jike jike ma sai da ta yi rawar gani, haka ma illahirin kawayen hafsa na gidan wanda suka yi dadin zama duk sunyi rawar gani a rayuwar hafsa, bata mantawa da Hajiya Gaga wanda take da kirki sosai a gidan sarkin Malamai Allah ya jikamsu ya gafarta musu.
yaune Rana babba wato ranar Auren Hafsat Muhammad Baba da Ahmad Bello. da safe Hafsat ta tashi tana abu kamar me farfadiya, ko Aljanu, bayan tun da take a rayuwarta bata taba tashin Aljanu ba, abun ya bawa mutune mamaki. Har safiya bata warke ba, sai akayi niyya kawai aka kaita gidan Malam Manga. Haka aka daga biki nan da sati biyu, kowa na ta jimamin ko Ahmad zai yarda a cigaba da neman aurenta bayan a gabansa yaji tana cewa bata sonshi. Yanxu dai bari mu huta anjima sai mu dubo ko meya sami hafsat haka har ta fara sunbatu, sai mu dubo yanda za'a kaya ko ahmad zai yarda ya aureta. ~~~ ummilkhairy~~
4⃣ MAKABARTAR MU~Khadija Aminu
"yaya Ahmad wai me yasa kullum kai idan ka sa a ranka zakayi abu ba'a isa a hanaka bane, ni ma fa dan uwan ka ne, jininka, ni kadai na rage maka, yarinyar tace bata sonka a ranar daurin aurenku ai sai ka kyaleta, ka nemi wata matar". tsawa ahmad ya daka wa kabir yana cewa " wai meyasa baza ka gane cewa son gaskiya nakeyi wa hafsat ba, bazan taba kin taba dan ta shiga irin wannan halin ba, daga gani ba ita bace tace bata sona ba, aljanu ne, kuma insha Allah sai na aureta kuma zata warke, kar in sakeji ka kara mun irin wannan maganar, idan kaje kasha kwaya ne kake fada mun wannan maganan...... get out of my sight kawai. sum sum kabir ya fita daga sight din yayan nashi yana mai jin haushin yanda yayi treating dinsa. kun san dalilin zuwan kabir wajen yayan nasa kuwa? a'a toh da sakel.
A gidan malam Manga kuma ana tayi wa Hafsat addu'oi ana shafa mata tana ta sumbatu. Malam manga hanshakin Malami ne wanda duk Northern Nigerian nan ba wanda bai san shi ba saboda ya iya maganin Aljanu. Ana zuwa wajen shi tun daga Maiduri, yola, gombe, kano, katsina, sokoto, zamfara, kebbi, damaturu har da Abuja ma dan maganin Mayu, Aljanu, sihiri da dai sauransu. Malam Manga ne ya fito yana neman wadanda suka kawo hafsat, sai Baffa Manga yace gashinan. Anan aka masa bayanin cewa turo mata Aljanu akayi dan su sata abin da takeyi. Amma su zaba abin da za'ayi, ko ayi kaikayi koma kan mashekiya, wato wanda ya turo mata sai a tura mai ko kuma a kona su kawai. saboda Allah baffa Manga yace ai kowa ma na laifi Allah yana yafe masa, ai mun yafe ma wanda ya turo mata, kuji masu tawakkali, Allah ya gafarta musu, amin.
Malam Manga ya dade bai ji mutane masu yafiya irin wannan ba sai yaji dadi ya koma ya kokkona Aljanun da suka shige ta har suna fadin cewa Ai turo su akayi dan su hana ta aure dan ta ce bata son wanda ya turo matan. Da ikon Allah, allah ya bawa Hafsat Lafiya. Alhamdulillah.
Bayan sati biyu kuwa Aka daura musu Aure da Ahmad bello wanda ya nuna son Gaskiya a Hafsat. Kabir Bello kuwa ya dau alwashin sai yaga bayan Auren nan Nasu. A bikin an shirya wata gagarumar Liyafa, amma sai akayi amfani da dama wajen kiran Babban Malami Mai suna Dr. Sagir Ahmad s.y, ficaccen Malamine sosai Allah ya kara masa girma, a inda yayi nasiha akan Ya fadakarda samari da 'yan mata akan soyayya kafin Aure kura ce da kan rago. Dama dai
so a cikin zuciya yake. Domin a gidan aure ne ake gane
soyayyar gaskiya da kuma soyayyar jabu. Allah
Ya kara daidaita hankulan ma'aurata. Wadanda
suke da niyya Allah Ya taimake su.
Soyayya kafin aure da muke yi, babu shakka a
cikin raina idan na ce, ba ta da wani alfanun da
ya kamata a ce ta samu gindin zama a cikin
zukatanmu. Domin duk abin da sharrinsa ya fi
yawa da kashi saba'in, ai barin sa ya fi zama
alkhairi, in dai gaskiya ake so.
Namiji ya nema wa kansa budurwar da zai aura,
ya rike ta a matsayin masoyiyarsa, wadda za su
rika soyayya har tsawon shekara daya ko biyu
kacal ma, ko da ya neme ta ne bisa gaskiya
kuma yana son ya aure ta, wannan al'amari babu
ko muhawara shirme ne ba soyayya ba,
musamman idan ta kai munzalin a daura mata
aure. Tsohuwar mota ce idan za ka saye ta, sai a bar
ta hannunka kana jinjina ta kwana biyu, har sai
ka tabbatar da lafiyarta lau sannan ka biya kudi.
Shi kansa wanda ya je sayen sabuwa, ai kudi
kawai zai biya domin ya karbi motar. Ke nan
wanda bai yarda da sahihancin wadda ya nema
aure ba, shi ne zai nemi dadewa ana soyayya har
sai ya ga ingancinta. Idan akwai nazari, ya
kamata a fara neman aure ne a lokacin da aka
tashi aure, idan kuma an nema sai a yi auren, ba
sai an tsaya ganin uwar-bari ba.
Tsohuwar hujjar da muke ta kafawa ita ce, wai
yin hakan shi zai ba masoyan damar su san halin
juna, mun gano karya ce! Sau nawa aka yi
soyayya ta tsawon shekara biyar, amma da aka
zo aka yi aure ba a shekara daya ba, kuma aka
rabu? Ashe shekara biyar din da aka yi ba su yi
wata rana ba! An bata gishiri wurin dahuwar kaho
kawai.
bata lokaci ne kawai, amma sha'awar duniya da
hudubar shaidan ta hana mu gane haka. Iyaye
sun makance, diya ma ta makance. Za ka samu
diyar mutum ta kai shekara goma sha biyar a
gida, sai ga wani ya fito yana son ta da aure,
maimakon a ce za a fara zancen aure, sai kawai
a bude mata sabon shafin zaman gida? A haka
zai ja ta har wasu shekara biyar akalla suna
soyayya. Yau ka ji ya zo hira, gobe ya zo da
Babur ko mota wai zai kai ta gidan su gwaggo ko
gidan kawu. Kuma ba ya daga wadanda Allah ya
kebance ba za su aikata sabo ba. Wa yake da
tabbacin abin da yake faruwa tsakaninsu idan sun
hadu da sunan Soyayya? Ka ga bata mutu ba ta
balgace.
karshe idan aka zo ba a yi auren ba, shi ke nan,
shi ya more da diyar mutane kuma matar wani,
ita ma ta more da dan mutane kuma mijin wata.
Ita ta yi ta kwalliya saboda shi a banza, shi kuma
ya yi ta biya mata kudin lalle da kitso a banza. In
ma an yi rashin sa a, to za ka samu sun ji dimin
juna babu adadi. Daga faruwar haka, sun jefa
gubar shakku a cikin zukatan junansu, domin
dukansu ba za su amince da abokan zamansu na
aure ba. Ita za ta rika kallon mijinta da cewa ya
yi ta holewa da wata budurwar kamar yadda ita
ma ta yi ta holewa da wancan saurayin. Shi ma
wancan kallon da zai rika yi wa matarsa ke nan.
Wurin gyaran gira an rasa Ido.
Ko ba ka yi min adalci ba, za ka yarda da cewa
duk wani da namiji da zai rika kebancewa da
budurwar da ba muharramarsa ba, to lallai ne da
shi har ita ba za su fi karfin shaidan ba. Ashe
akwai yiyuwar zargin da wadancan ke yi wa
abukkan zamansu, shi ma gaskiya ne, idan dai
har su kansu sun yi irin waccan soyayyar da
wasu! To ballai ma uwa-uba a ce wadanda suka
yi soyayyar ne suka auri Junansu! "Wai kar ta
san kar" Inji Bahaushe.
Idan wata rana bukatar zuwa gida ta kama ta, da
ta ce masa: "Maigida ina son zan je ganin gida."
Zai ce mata, "gaskiya ba inda za ki je," saboda
ya riga ya san ita ba mutuniyar kirki ba ce, don
me zai amince da ita? Ai ita ma ba ta amince da
shi ba. Ya take ji idan ya yi wanka zai fita
unguwa ko kasuwa? To ballantana ta ji labarin
zai karo mata kishiya! Ai karshen faduwar gaba
ke nan, don ita ma ta san sun zama su biyu ke
nan a wajensa, daya a gida, daya a waje. Eh
mana, to lokacin da suna soyayyarsu a waje me
suka fasa yi? To don me ba zai yi da wata ba?
Iyaye kada ku yaudari kanku, ku bude zuciyoyinku
da kyau kusa idon basira, idan ka san diyarka na
tare da wani suna soyayya, zuciyarka ta daina
lissafa wa kanka a cikin wadanda suka kare
mutuncin 'ya'yansu. Kai ma wanda ya rike diyar
mutane, ka sani ba son ta kake yi ba, zuciyarka
ce take yaudarar ka. Saboda haka, idan ka tashi
aure ka yi aure, idan kuma ba ka tashi ba, to don
Allah ka kyale diyar mutane ka je zuwa abin da
yake gabanka. Idan ka shirya, ka zo ka yi auren
yadda ya kamata a yi shi.
"Ita gaskiya fa akwai daci. Zafinta ba shi da
sassauci. Sai dai idan ga adalci. Ita ce Madubin
dubawa" Inji wani wai shi JIKAN BABI, a cikin
wakarsa mai taken Hasken Gaskiya.
Yabo da godiya sun tabbata ga Allah. wa Alaikumussalam. Anan Malam sagir ya kawo karshen wannan Wa'azin nashi. Hafsat ce aka kaita garin kano dan anan suka tare, sunyi kukan rabuwa ba kadan ba Da 'yan uwanta, masu ji da ita, hajiya iya tayi mata Nasihu ba kadan ba akan zamantakewa sannan tace mata tayi kokari ta rike Maraicinta. Duk kayan dakin da su hajiya iya suka mata Ahmad yace kar a taho da shi a barshi a gidan shi na misau. Gidan da suka zauna a Rijiyar zaki ne, gida mai kyau, duk Ahmad ya nuna mata yanda ake amfani da Abubuwan gidan. Ahmad ya nuna mata so sosai, ta Mallaka Mai kanta da rayuwar ta duka, sun rike juna da Amanada. Idan ya tafi lectures, itama sai ta girka mai Abinci, kafin ya dawo su sha soyayyansu.
Ana nan dai sai ranar ahmad ya dawo gida rai a bace, sai Hafsat da taga ya dawo ranshi a bace sai ta kwantar masa da hankali da dan Nasihohi akan rayuwar zaman duniya, a nan ne ya bata labarin abin da ya faru, wai kabir kanin shine ya dami jama'ar garin misau, kuma ya ma kade wani yaro, gashi Makarantar da yakeyi an koreshi dan yayi fada da Malami. Hafsat bata ji dadi ba Amma duk da Haka sai ta nuna damuwar ta sosai akan matsalan, Hafsat tayi koyi da Matan kwarai dan ana so idan Mijin ka yana cikin damuwa kanuna masa cewa kafi damuwa da damuwar sa. Bata bar wajen ba sai da ta tabbata cewa ta kwantar masa da hankali. Ta bashi Abinci yaci. A nan nema yayi mata Albishir da ya samo mata Admission a wani Makaranta Amma SS3 Za sata, dan idan ta zana WAEC DA JAMB sai ya sama mata degree. Anan ta kara nuna mai Farin cikin ta a fili, sannan tayi mai kyakkyawan Addu'a. kamar Allah ya kara budi, kuma ya kareka daga shartin makiya, kuma ya shirya mana 'yan uwa. ya Amsa da Amin. shikam kullum jin ta yakeyi sabuwa a ranshi.
Da daddare bayan sunxo kwanciya sai ya nemi wata Alfarma idan zata bari, ita kam ma har ta yadda tun kafin a fada mata, kawai sai yace Mata yana son ya dawo da Kabir kusa dashi, zuciyan Hafsat sai da yayi daram dan kuwa tasan cewa Kabir dan uwan ahmad, ya sota lokacin tana budurwa, kuma saboda tace mishi Bata son shi sai da yayi Mata Alqawarin cewa ko bazatayi aure ba, amma sbd zuciyar imani, kawai sai ta amince da kudirin shi dan bata son ya gane damuwar ta.
Bayan sati biyu kuwa sai ga Kabir ya dawo gidan Yayan sa, sai ku biyo ni dan jin abin da ya faru bayan zuwan kabir bello gidan Ma'aurata. ~~ummilkhairy~~

HAUSA NOVEL (MAKABARTARMU)Donde viven las historias. Descúbrelo ahora