PART 9

3.1K 95 0
                                    

12. MAKABARTARMU.~~Khadija aminu~~~
kabir ne ya shiga ?akin yana musu tafi yana cewa Hafsat bazaki ta?a bari na ba, ko kina so ko ba kyaso sai kin zauna dani. Tunda har kuna shirin guduwa dake da 'yarki. Ni kuma bari in shirya tattare ki ki koma gidan ku MAKABARTARKU. Kuma Mutuwa ne kawai zai rabaki da wajan ko kuma idan naga dari bisa dari kin yarda dani. Da na zata anan zamu rayu cikin mutane ashe zamu koma gurinmu na asaline. Ayya, Hafsat My wife, kina da taurin kai.
Ammi ce ta sake Batula sai ta durkusa a gabanta tace "Batula Dan Allah kar kice zaki bar gidan nan plz. Kinyi karama kina irin wannan Maganan, kinga abun da kika jawo mun kox. Ki tashi mu koma MAKABARTARMU. dan ni na kwammace in zauna a can akan in rabu dake."
tashi tayi, taku kadan zuwa wajen Kabiru. Sannan tace mu tafi MAKABARTARMU. mamaki ne ya debe shi sannan yace baxan daukeki ba Amma zan yi wani abu akan hakan. Juyawa yayi yaga Batula sannan yace zo ki tafi dakin ku.
Tafiya tayi cikin Hawaye. Amma taci Alwashin sai ta bar gidan. Zuwa tayi ta fara Alwala. Sai sallah takeyi tana neman Mafita.
Can cikin dare Batula ta idar da sallah har ta saka sleeping dress dinta riga da wando, ta daura dan kwali wanda Gashin ta sai da ya fito ta tsakiyan dan kwalin, gashi har gadon bayanta. Dama bata cika son kitso ba. Batula kenan, sarauniyar kyau. Ta fara addu'a sai taji an shigo dakin tana juyawa sai taga Amminta zuwa wajenta tayi tana cewa plz Ammi be Happy. Ina son kiyi mun smiling. Teachern mu yace somdtimes if u choose to be happy, u will. Ina son ki sosai. Ammi ma ta rungumeta ta bata wani Laalita tace ki ?aure a jikinki. Idan kina bukatar kudi ki dauka a ciki amma ki kula da kanki, addu'a ta bazata tashi a banxa ba.Duk inda zaki tsinci kanki ki cigaba da halinki na kirki.  Sai da safe.
Batula  kallon laalitar tayi da kyau sannan ta daura a cikin ta. Tayi addu'a. Zata koma bacci kenan sai ta kara jin budewar kofa. Tana zaton Amminta ne sai taga sa?anin hakan Abba ne. Janyo ta yayi yace zonan. Sai ya jata sukabar gidan. Har zatayi ihu sai ta tuna da cewa wannan opportunity ne. Kawai sai ta bishi. Sakata yayi a mita fiiiiiiiiiiii sai Hanyar Kafin Madaki. Gida Mai kaman MAKABARTA.**ummulkhairy***

13. MAKABARTARMU ~~ khadija Aminu
Batula Ta rasa abin yi taga tafiya yakeyi ba kakkautawa. wani dabara yafado Mata sai tayi wani irin kara tana cewa "wayyo,wayyo,wayyo ciki na zawo Abba zawo". Saita motan yayi dan baya ma so ta mishi kashi a mota. Sai ya ce Mata ki bari idan mun je ta dan gaba koda gidan mai ne. A lokacin ma karfe 2: na dare ne. Kuka takeyi mai ji da Rai kawai sai taji an tsaya. Sauri tayi ta bude motan, tana kokarin fita sai yace mata wajen a rufe yake  ko juyowa batayi ta ganshi ba kawai sai ta haura ta saman gate din gidan man ta shiga da gudu. Gudu takeyi cikin gidan man nan, tana neman inda zata boye dan kar ya ganta, sai ta hango wani mota irin na sojojin nan, gurin dama babu hasken lantarki sai hasken farin wata. Juyawa tayi ko zataga ko abbanta na ganin ta, sai ta lura baya kallonta kawai sai ta shige bayan motan. Dabarane ya fado mata sai tayi wani irin ihu.
Kabir kam yaji shiru yayi shiru bata dawo ba kuma yaga tym na tafiya dan yanxu 2:30 na dare ne. Fitowa yayi daga motan yana leke leke sai yaji muryan batula tana  ihu. Abba!!! Abba! Abba! Wayyo! Ka taimakeni, zan fada rijiya. Wayyo!. Hankalinshine ya tashi sai ya shiga gidan man yana bin inda yake jin ihu amma babu direction. Kawai sai yaji shiru babu magana kuma. Kawai sai yayi shawaran neman inda rijiya yake a cikin gidan man, ya nema bai gani ba. Hankalinshi bai kwanta ba yana ta nemanta sai ya fara kiran sunanta still shiru. Batula!!! Yaji shiru, Batula!!! Bata amsa ba, yana cikin ihun ne sojoji biyu suka fito daga cikin motansu suna mika. Ganin wani mutumi yana ihu yasa su fashi da sauri suka dauki bindigan su suka zo wajenshi. Daya daga cikin su ya ce "zo nan". Kabiru yaje wajrn yana dan Allah ku taimakeni. 'yata nake nema. Ta shigo nan wai tana jin kashi shine na barta ta shigi ina jiranta a bakin mota. Sai naji ihunta tana kiran sunana. Na ma ji tana kiran zata fada rijiya. Sojojin ne zuka kalli juna suna cewa mu ma munji amma na zata mafarki ne. Zagaya wa sukayi suna neman ta amma shiru har suke cewa babu toilet ma fa anan gidan man. Kuma babu rijiya. Sai dai wani abune ya dauketa.
Har karfe hudu na dare nema suke mata basu ganta ba. Hankalin kabiru ya tashi, ya rasa abun da zai ce ma Amminta idan ya koma gida, dama da shawaransa idan ya kaita gidan kafin madakin nan zai barta har sai ta gane kurenta. Kuma idan ya dawo gida sai yace ma amminta kila guguwa tayi. Amma yanxu kam yasan Amminta kam ta tashi a barci. Zata gane cewa bai kwana a gida ba.
Shawara sukayi da sojojin nan yace musu dama Matarshi ce zata haihu shiyasa suka fito da daddaren nan daga Gombe zasuje kano. Sai ya basu number sa yace Udan suka ganta su kirashi. Ya mika musu du?u bibbiyu ya kama gabansa.
Batula ka tana jinsu harya tafi. Tana jinsu su na cewa "Baaaaba kaji mun samu kudi fa cikin daren nan. Allah yasa ba Mafarki muke ba. Na dade ban rike dubu biyu ba. Allah ya kyauta wannan gwamnatin." dayan kuma yace" ammafa nayi mamaki, ko hawaye babu a idonsa, kamar ba diyarsa ba, kuma ai batan 'ya ai ba abun wasa bane, ni kam ba 'yarsa da zan duba masa. Kila ma sato ta yayi ta gudu shine yake nemanta." daya kuma yace "Allah ya kyauta mu koma cikin mota mu kwanta kasan gobe da safe zamu tafi Abuja Dan oga yace mu sameshi a can".
Shiga Motan sukayi suka yi baccin su. Tun batula tanajin surutunsu tana jin dadi. Da ta daina ji kuma tsoro ya fara kamata Amma da ta tuna da addu'an Amminta sai ta kwanta tayi bacci.
*****Haske ta gani a idonta, kawai sai ta tashi, tunani tayi ko zata fita daga bayan Motan sai ta tuna da fa taji sunce zasuje abuja. Sai tayi shawaran gwara taje can. Makalewa ta kumayi a bayan motan. Wani leda ta gani a gefen ta sai ta lullube kanta. Ji tayi sojojin nan sun tashi. Sunyi Sallah. Tana jinsu har daya daga cikin su ya bude bayan Motan bai gane cewa akwai mutum ba har zai juya sai ya shiga ciki ya saka kayan sojojin shi ya fito. Dayan m hakan yayi, duk tana jinsu amma addu'a take tayi Allah yasa kar sujita.
Sun kama Hanyan tafiya. Yunwa takeji sosai sai ta bude kanta daga cikin ledan sai ta fara duba cikin kayansu ko zata ga abinci, ai kuwa sai taga ruwan gora, ta dauka zata sha sai ta hango dabino, kawai ta Fara ci. Ta ci ta kishi sai ta kora da ruwa. Ta mike tana ta bacci, dama akwai iska sosai. Tunani kawai takeyi.
**** can gida kuma Abba ya koma ne karfe 5:00. Daukan carbi yayi a cikin mota da kurani da sallaya ya shigo gida. Yana shiga gidan sai ya shiga dakinsa, wa zai gani, sai yaga Ammi tana kuka a dakinsa. Ya rasa yanda zai yi kawai sai yayi sallama, bata amsa ba. Sai ta juya tana kallonsa tana cewa ina ka kaimun 'yata? Tambayan ya masa tsauri dayawa sai yace mata ni ban dau yarinyanki ba Sallah naje, kin ganni ma daga Masallaci nake. Juyawa tayi tana Harararsa tana cewa toh Allah ya kama ka. Lokacin sallah baiyi ?a ko assalatu ba'a kira ba. Kuma tun cikin dare naje daki tashin Batula Sallah ban ganta ba. Nazata ita tabar gidan nan da kanta sai na duba dakin ka dan in fada maka kuma baka nan. Dan Allah ka dawo da ita ni zan hana ta tafiya.
wani abune ya a makokoran sa ya tsaya. sai yaje bayanta yana Dan Allah kiyi hakuri zan dawo da ita plz m sry. Cewa tayi toh yanxu ina kabarta nasan dai bazaka kai har can ace ka dawo ba . Numfashi yaja yace. Dan Allah kiyi hakuri. Amma muna kan hanya ne na tafiya kawai sai tace mun tana jin zawo. Da muka sauka a gidan mai sai ta shiga ciki da gudu bata ma jira na yi parking na rakata ba ta fita. Da na ga bata dawo ba sai naji tana ihu................ Ya gama fada mata duk abunda ya faru. Ba abunda ammi takeyi sai kuka. Tana cewa "kabir ka cuceni, dama haka rayuwata take, yanxu ma zan cigaba da daukan kaddara Har in koma ga Allah."
Abba yaji tausayinta sosai. Ita kuma Da ta koma daki Farin ciki ta dinga ji tunda Allah ya subutar da 'yarta a hannunshi. Sai dai Fatan Allah ya hada su a nan gaba kuma ya kare mata diyarta. Da safiya yayi Har ta tashi tayi musu girki kamar yanda ta saba, ta gyara gidan tsa tsaf wanda hakan kabir baiyi tsammanin hakan ba. Kuma ta kai mishi abinci. Sai dai ta roke shi ya Mayarda yara makaranta. Da sauri ya yarda.. A ranar ya kai su skul Har ma da siya musu form din islamiyya. Abun har yaso ya bawa Ammi Mamaki sai dai tasan ita bazai barta ba.
*****A hanya ne ya kira sojojin da suka dauka sai yake tambayansu ko sunga 'yarsa sai suka ce Masa basu ganta ba, dama su ma kawai sun kwana a gidan man ne saboda sun taho daga Nijar kuma dare ya musu su na son su tafi abuja, sai suke ce Masa kuma yanxu ma su na kaduna sun kusa shiga abuja. Amma sunce masa ya je police office yayi report. Yayi musu sallama. A lokacin yayi Farin cikin rashin ganinta dan dama baya son ta. Yace Allah ma yasa wanine ya samu Nama. Yana nufin Allah ya sa masu yankan kai ne suka kamata.*** Ummulkhairy***

HAUSA NOVEL (MAKABARTARMU)Where stories live. Discover now