Part 17

2.2K 70 4
                                    

29. MAKABARTARMU~~ KHADIJA AMINU
Hasbunallahu wa ni'imal wakim Kawai General yakeyi, Dan irin ihun da Batula tayi ta razana kowa da kowa.
Hankalinshi yayi Matukar tashi Dan tunda Innan shi ta haife shi bai taba jin irin ihun nan ba. Daga ta yayi ya kaita asibiti wanda hakan ne yasa Taron da akayi na Yi mata Sallah da kai ta Makabartamu ya watse. Yau sati biyu kenan Batula bata Farfado ba Kuma bata Numfashi, sai dai an saka Mata oxygen Wanda zai taimaketa wajen Numfashin. Likitoci sunyi iya binciken su basu Gano ciwon dake damunta ba, da Yake FEREPROD aka kai ta sai doctors da nurses suka gane ta, suka ce Ai tayi loosing Memory dinta lokacin da suka zo Na Farkon. Yanxu Kuma Basu San Abun da ke damunta Ba.
**** Sati uku kenan yanxu Dayin Aiki a zuciyar Sergernt Ahmad, Alhamdulillah an ci Nasara da Ikon Allah. Sai dai Fatan Allah ya Kara MASA koshin Lafiya. Yau dai da aka cire masa oxygen din Kuma zai iya Magana ya Damu a Kira MASA General Dan shi kadai Yake son ji. Salim!! Salim!! Sai kiran sunan shi sergent keyi Amma ya Fada Wani tunani, har imagination yakeyi cewa Zahran shi ta Mutu tana kwance a Kan Gado yanda ya barta, a cikin sati ukun Nan yayi Matukar wujijjiga akan tunanin Zahra. Har tunani yakeyi anya zai iya Rayuwa ba Zahran shi? Allah dai ya raya ta. Ba irn Abun da Baya cewa. Salim!!! Ya kara ji sergernt ya kira shi kawai sai ya dawo daga duniyar tunani yana cewa Na'am. Sergernt ne yace wai meke damunkane salim Nafi awa daya ina kiranka Bakaji na. Da sauri ya Fara cewa Dan Allah uncle...... Zai yi Magana sai Kuma yace Ba komai kawai dai. Amma Uncle Yaya jikin Naka? Da sauki inji Sergent sai yace Alhmdlh, dama Ina so ka kira mun General ne inyi waya dashi. Toh yace kawai sai ya dauko wayan sa ya kirasa. Gaisuwa sukayi a Mutunce sai General yayi mishi Albishir da cewa anga batula dan ya kwantar da Hankalinsa.
Da daddare da suka sake waya sai Sergernt ya kasa Hakuri yace yana son waya da Batula Amma sai akace Masa Ai bata kusa, da yaga Ana Mai juye juyen Hankali sai ya ce ayi mASA transfer din treatment zuwa Nigeria Abuja dan bazai iya jira har lokacin da suka kaidan ce Mai ba. Hakan kuwa akayi ba tare da an sanar dasu General da Popsy ba, dama can Salim ya da komawa Nigeria. Duk abun da ya gani a India baya burgeshi. Ranar da ya dawo daga sallah sai yaga sari na Mata sai da ya siya wa Zahran shi, haka Ranar na ya saya Mata clip din parking Gashi Dan Batula Nada Gashi, harda sarkan sawa a Gashin kai sai da ya saya, ya sayi tsarava da yawa da Yake tsammanin zai yi wa Zahran sa kyau. Haka suka baro India Yana Mai Farin ciki da Fargaban ko Zahra ta Mutu ko tana da rai?? Sergent Kuma sai addu'anfa Matafiya yakeyi yana Allah ya Fitar masa da Hafsat dinshi. Ya sa Lafiya Batula take. A haka suma ISO Nigeria kowa da tunanin da yakeyi.
****General ne da yaje Sallah Masallaci ya roki a saka shi a addu'a yarinyarsa Ba Lafiya. Sai limamin Masallacin da yaji irin Rashin Lafiyarta sai ya ce ya kamata a var Maganar na asibiti a koma addu'a, da Magungunan Musulunci, dan basu san irin cutar dake damun ta ba. Kila A sani idan anyi na Addinin. (Kira gareku 'yan uwa, ku taimaka wa kanku ba ko wani ciwo ake zuwa Ma asibiti ba, a yawaita Hada na asibiti da na addini, ku yawaita, shan su Habbatusauda da Man zaitun da dai sauran Magungunan Musulunci).Wani Mutumine Bawan Allah a cikin Masallacin ne ya ce ma General zai bishi Dan yana Ganin irin wadannan cututtukan daban daban. Hakan kuwa akayi General ya roki asibiti dasu bari a dawo da ita gida dan basu ga canji ba. Da Kyar suka yarda, da ba Dan Soja Bane Ma Ina fa da sunyi mishi rainin Hankalin yan Nigeria.
Bayan an tafi da ita, Malamin yace a kaita wani daki wanda babu kowa kuma Ba kaya. Bayan anyi komai ya shi ga dakin da jakan shi, yayi sauri ya tashi yaje Gurin Batula, yana Addu'a a zuciyarshi. Yaje Kanta Ya Roki a miko masa ruwa, da aka miko yayi sauri ya tofa addu'a a cikin ruwan ya dai-dai ci idonta ya Watsa Mata ruwan, Wani Kara ta Kara sakawa Wanda duk saida gidan ya dauka da Kara.
Malamin ne ya ummurci da a Bashi Kaskon turaren wuta, sai akace Masa Babu Amma akwai burner,  Haka aka kawo mASA ya jona a jikin wuta ya saka Wani turare Mai shegen wari sannan ya Shafa Mata Jan niski a Fuskanta da Man juda Sannan ya kunna kira'a a radion sa da Yake yawo da ita yaji yanda jikin ta Yake yi a lokacin kamar maciciya sai kadan Masifa Mai rikitar da Dan Adam din da yaji.
"Aslm Alaikum" abun da Sergernt Ahmad ya furta kenan daga shigan shi gidan General Dan ana n ya dauka Amma ihun da yaji yayi Matukar Razana shi.....
***ummulkhair***

HAUSA NOVEL (MAKABARTARMU)Donde viven las historias. Descúbrelo ahora